Atiku ya caccaki ‘yan majalisar wakilai kan kin amincewa da wa’adin shugaban kasa na shekaru shida

Atiku ya caccaki ‘yan majalisar wakilai kan kin amincewa da wa’adin shugaban kasa na shekaru shida

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, a ranar Alhamis, ya caccaki majalisar wakilai kan kin amincewa da kudirin dokar wa’adin mulki na shekara shida ga shugaban kasa da gwamnoni.

Kudurin wanda dan majalisa mai wakiltar Ideato North/Ideato South Federal Constituency, jihar Imo, Ikenga Ugochinyere da wasu mutane 33 suka dauki nauyinsa, an yi watsi da shi ne a ranar Alhamis a wata kuri’ar da ‘yan majalisar suka kada a zauren majalisar.

A watan Oktoban shekarar da ta gabata ne Atiku ya aike da wasika ga Majalisar Dokoki ta kasa, inda ya bukaci a yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima domin kafa wa’adin mulki na shekara shida ga Shugaban kasa da gwamnonin jihohi.

A cikin takardar da ya mika wa kwamitin majalisar dattawa kan duba kundin tsarin mulki, Atiku ya kuma ba da shawarar a rika karba-karba a shugabancin kasa tsakanin Kudu da Arewa.

Daga Abbakar Aleeyu Anache