PDP ta bayyana takaici yadda Gwamnatin Sokoto ke wasa da lafiyar al’umma
Jam’iyar adawa a jihar Sokoto ta bayyana takaicinta yadda gwamnatin jihar ke wasa da lafiyar al’umma, hakan ya sa suka tura ma’aikatan da b su kware ba a fannin.
A wata takardar bayani da jam’iyar ta fitar ta hannun jam’in hulda da jama’a nata Hassan Sahabi Sanyinnawal ta aikawa Managarciya ta ce jami'an kiyon lafiya da aka tura a ma'aikatar lafiya ta jiha abin takaici ne a tura mutanen da ba su da kwarewa Kuma su ne za su kula da lafiyar al'umma a jiha.
Ya ce an sauya kwararrun ma'aikata da suke da gogewa da wasu da ba su da kwarewa domin kawai suna goyon baya jam'iya mai mulki hakan ya nuna an siyasantar da aikin gwamnati a jiha.
A cewar bayanin na PDP yakamata APC ta mayar da hankali ga bunkasa harkar kiyon lafiya a jiha amma ta kasa yin hakan wurin kawo ma'aikata da ba su da kwarewa don cimma manufa ta siyasa.
PDP ta yi mamaki yanda wasu daga cikin ma'aikatan suka mayar da ofisoshinsu wurin yekuwar zabe a lokacin da siyasa ta kare, yakamata mutane su sani ofis na gwamnati ba wuri ne na biyan bukatar kashin kai ba.
managarciya