Jagoran jam'iyar APC Sanata Bola Ahmad Tinubu ya kaiwa Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ziyarar ban girma a gidansa dake Abuja.
Ziyarar tana ciki da sirrika da saƙonni ganin halin da ake ciki na fuskantar babban taron jam'iyya mai mulki waton APC.
Managarciya ta kalato wani sirri da ziyarar take ƙunshe da shi, kan tafiyar 2023 ne na tabbatar da ɗaurewar nasarar jam'iyarsu a babban zaɓe dake tafe.
Ziyarar ta Tinubu ba baƙuwa ba ce ko sabuwa a gidan Wamakko sai dai ta ɗauki hankali ne kan kunnowar siyasar 2023 da batun takarar shugaban ƙasa da ake zaton Tinubu zai yi da kuma tunkarar babban taron zaɓar shugabannin jam'iyya na ƙasa dake tafe.
Ba a bayyana abubuwan da jagororin suka tattauna ba a hukumance sai dai wani makusanci ga Sanata ya ce an tattauna abin da zai kawo cigaban Nijeriya ne da zai ƙara dunƙuleta a matsayin ƙasa ɗaya, kuma da hanyoyin da za a ƙara bi don samun romon dimukuraɗiyya ga mutanen ƙasa musamman marasa ƙarfi.