ƘADDARA TA: Fita Ta 13

 ƘADDARA TA: Fita Ta 13


 ƘADDARA TA: 


        Na
*Jiddah S Mapi*


*Chapter 13*


                  ~Saida yayi bacci me isanshi kusan dare kafin ya tashi yana turo karamin bakinshi, kallon Alameen da yake sa jallabiya yayi, alameen yace "ka tashi? lokacin salla yayi saika tashi mu idar"
tashi yayi ya yaye bargon, bathroom ya shiga yayi alwala yazo sukayi salla, abinci aka kawo musu zama yayi sabida yayi missing abincin maman alameen ci ya fara alameen yace "gaskiya ka daina kuka kamar mace idan abu ya sameka"
shareshi yayi kamar baisan yana magana ba, alameen ya saba haka halin hameed akwai shariya idan ma baiga dama ba kana mishi magana zaiyi kamar baya wajen, alameen yace "wannan girman kan naka shine matsalanka ai, koda shike ya karɓeka tunda kai ɗan sarki ne, sai shegen soyayya kamar tattabara amma abu kaɗan yana samunka zaka fara raira kuka kamar mace"
tsaki yaja yaci gaba da cin abincin, Alameen cikin tsokana yace "to ya akayi ka rage ciwon cikinka na jaraban ne da kayi aure?"
pillow ya janyo ya maka mishi tarewa yayi yace "wayyo"
maka mishi pillow ya fara, gudu alameen ya tashi zaiyi ya rikoshi, turo kofan mama tayi rike da glass jug cike da zobo, tace "to to to baku girma ba kenan kun tuna da baya zaku fara haukan kuma ko?"
sakinshi hameed yayi, ta mika mishi tace "gashi na san kanaso shiyasa na haɗa maka"
wallahi duk bakin cikin da yake ciki idan yazo gidansu alameen ji yake bakin cikin ya ragu, ya fara sha da bakin jug ɗin bai wani sa a cup ba, fita tayi alameen ya ɗauko cup yace "samin dayawa"
hararanshi yayi alaman ba zansa ba ka kwata, yace "wallahi zan kwata kasan ba fin karfina kayi ba ko?"
juyawa yayi ya zauna a bakin gadon yana sha, kiran wayan ya kaseem ne ya shigowa alameen, amsawa yayi, yace "hello ya kaseem"
yace "hameed yana gidanku?"
yace "eh gashi nan yana nan"
yace "to kada ka barshi ya dawo yau ku kwana acan sabida yana cikin damuwa"
yace "to yaya"
aje wayan yayi yana kallon hameed da yayi shiru jin ya kaseem ne ya shigo, durkusawa yayi a gabanshi yace "yarima hameed ya kamata ka fara fuskantar matsalanka da kanka sannan kasan yadda zakayi solving komai da kanka, yanzu fa kai ba yaro bane sabida ya kaseem ya shagwaɓaka hakan baya nuna kai yaro ne karami, nasan kana cikin damuwa tun auren zeenat bakada kwanciyan hankali amma hakan bashi zaisa ka zama rago ba, na sanka da jarumta hameed kaifa yarima ne idan baka saba da gwagwarmaya ba haka zakayi idan ka zama sarki? kana gani fa ya kaseem har yau baiyi aure ba sabida bayaso ya raba lokacin da yake baka da wata, ya kamata kasan yanzu mun girma mu ba yara bane"
sunkuyar da kai yayi yana jin alameen har ya gama, ɗago ido yayi ya lumshe sannan ya gyaɗa kai alaman to, rungumeshi yayi yace "yawwa my bro"
a ɗakin suka zauna saide a kawo musu abinci a gidan ya kwana da dare alameen yana bashi labarin school sai dariya yake suna cikin farin ciki, yana matukar son alameen kamar jininshi yake jinshi hakan yasa ma suka bashi kanwarsu meenat tun tana karama kuma har yau suna kan bakansu shi zata aura.

Wasa wasa yau hamma najeeb yayi sati bai dawo gidan ba, duk inda tashin hankali yake tofa Asmeeta tana ciki, gaba ɗaya ta zauce, lungu da saƙo nemanshi take, meenat wacce itama ta damu da rashinshi harma tafi Asmeen damuwa har ta rame, komai ya tsaya musu abinci ma ba samu suke ba, zaune take a cikin gida tana kuka kamar kullum, har muryanta ya dishe dan kuka, tace "Ameena ina zanga hamma na? ina zan ganshi wallahi shi kaɗai nake dashi a wannan duniyan ameena ya zanyi?"
rungumeta meenat tayi tace "kiyi hakuri ki daina kuka asmee hamma najeeb zai dawo yamin alkwari zai dawo kuma nasan ba zai karya alkawari ba.
tace "to meyasa bai dawo ba? ko dai mutuwa yayi?"
tace "ki daina kuka dan Allah kukan ya isa haka Asmee"
shiru tayi tana ajiyan zuciya, mimi wacce take rashin lafiya sosai ta fito daga ɗakin tazo ta faɗa jikin asmee tace "adda jikina ciwo"
rungumeta tayi tace "zaki samu sauki mimi zaki samu lafiya bari na baki maganinki"
tashi tayi ta ɗauko mata magani a kwarya ta kawo mata, sha tayi saida tayi rabi kafin ta cire tace "zo na goyaki"
goyata tayi meenat duk lokacin data tunashi sai tayi hawaye ɗauke kai take sabida bataso su asmee suyi kukan sabida kukan yayi yawa, suna zaune a gidan cikin maraici da kewanshi, abinci ma gagaransu yake basa samu, saide Asmee taje ta tatsi nono kafin taje ta siyar ta dawo musu da kuɗin suci abinci, wata rana suna bacci aka shiga aka kwashe shanayensu gaba ɗaya, ko guda ɗaya basu bar musu ba, washe gari asmee taje dubawa taga babu shanu, suma tayi meenat ce ta tayi gudu taje ta ɗibo ruwa tazo tana watsa mata, a hankali ta buɗe ido tana kallonta tace "sun sace shanayen?"
zaman kauyen ya musu wuya babu me shigo musu kuma babu me taimaka musu haka suke zaune duk sun lalace, koda yaushe suna gida harda mimi itama tana tare dasu batada lafiya kuma maganin bai karɓeta ba, goye take a bayan Asmeeta tana jijjigata tace "yi shiru mimi na zaki samu sauki kinji?"
tana kuka tace "jikina yana ciwo Adda"
tace "kiyi hakuri zai daina"
itama meenat ba lafiya ne da ita ba, cikinsu asmee ce kaɗai me lafiya, itace take kula dasu.
tun suna damuwa har suka daina damuwa da rashinshi, sun fara koyan rayuwa babu shi, yau ya kai wata uku babu shi kuma babu alamanshi, mimi wacce ta rame sabida zazzaɓin daya sata a gaba Asmee tace "ya kamata mu san abinyi akan mimi sabida jikinta cigaba yake"
meenat wacce tayi tagumi babu abinda yake mata daɗi a wannan duniyan, taja numfashi tace "kuɗin nan da kika karɓo a wajen me nama kinga sunada yawa ya kamata mu kaita asibiti ko anan birni ne idan akwai kusa damu"
tace "Ameena kin san wani sharaɗi yamin akan kuɗin?"
ta girgiza kai, tace "wai fa saide naje na sameshi a gidanshi yau matarshi zata fita unguwa ni kuma nace mishi to"
waro ido tayi tace "kin tabbata babu abinda yai miki?"
tace "haba Ameenah sai kace baki san halina ba? ya za ai na kula wannan ƙazamin?"
tace "na san halinki Asmee tawa kawai de kin san ke amana ce a wajena dole na kula da amana"
murmushi tayi tace "to na gode kema amana ce a wajena sabida hamma najeeb yana sanki sosai, yanzu ya zamuyi?"
tace "ya zama dole mu gudu mu bar kauyennan kafin me nama yazo mu kai mimi asibiti ta samu lafiya"
tace "to bara na shiga na ɗauko kayanmu"
shiga tayi ta ɗibo kayan sannan ta fito tace "mu tafi"
meenat tace "amma inaso ki bani wani amsa dan Allah"
tace "na me?"
tace "mimi ƴarki ce?"
murmushi tayi sai kuma tace "mimi ba ƴata bace tsintarta mukayi a bakin hanyan shigowa wannan kauyen an wurgar da ita cikin tsumma hakan yasa muka riketa nida hamma"
cikin tausayi tace "naga bakwa kama ko kaɗan amma naga kina sonta"
murmushi tayi tace "mu tafi"
meenat ce ta goya yarinyar a baya ita kuma asmee ta rike kayansu suka fita, sauri suke su samu su bar kauyen kafin dare yayi, tun meenat tana daurewa har ta fara gajiya, Asmeeta ce ta karɓi mimi ta goya suka kara fara sabon tafiya bayan sun huta, tafiya me nisa sukayi kafin sukayi rabi, ganin dare yayi suka kwanta a cikin jeji bacci sukayi da yunwa a jikinsu, saida gari yayi haske kafin suka tashi suka kara fara sabon tafiya, Asmee tace "sannu mimi ta"
tace "to"
hawaye tayi sabida tausayin yarinyar, mashin me kafa biyu suka gani suka tsaya Asmee ta rokeshi yace su hau ta rage musu hanya, hawa sukayi a matse suka tafi, meenat tana tsoron mashin me kafa biyu har suka fara hango garin dake gabansu, hamdala sukayi ya ajesu a bakin titi yace "to nayi iya wanda zan iya sabida yarinya karama da batada lafiya yanzu zaku iya samun taxi da zai kaiku asibiti Allah ya bata lafiya"
godiya suka mishi sun jima a wajen kafin suka samu taxi shiga sukayi bayan sunce mishi asibiti zai kaisu, sai yanzu meenat ta fara murmushi sabida taga gari, har ya kaisu asibiti suka fito da kayansu, kati suka yanka na ganin likita meenat ce ta shiga da ita likita ya ganta ya gwada yaga maleria ne yace a basu gado ya rubuta musu magunguna da drip Allah yasa kuɗin hanunsu da ɗan yawa suka biya, gado aka basu Asmee tace meenat ta zauna zataje ta siyo musu abinci da sauran kayan bukatu, ta fita da jimawa har meenat ta fara damuwa da tunanin ko dai ta ɓata ne?
turo kofan tayi da ledoji manya a hanunta ajewa tayi tace "gaskiya birni babu daɗi ko kaɗan kana tafiya mutane na kallonka kamar aljani?"
dariyan farin ciki tayi tace "kyawunki suke kallo"
taɓe baki tayi tace "idan sunga hamma najeeb kenan cinyeshi zasuyi"
shiru meenat tayi tana jin wani iri a ranta, ganin haka asmee tace "kiyi hakuri sunan hamma najeeb ba zai taɓa fita daga baki na"
share hawaye tayi tace "nima ba zan iya mantawa dashi ba asmee ko ina yake ina mishi fatan alkhairi"
jikin mimi ya tashi da dare sosai ya dameta asmee sai kuka take, da asuba tace "ga garinku"
sunyi kuka sosai har suka gode Allah.
suna asibitin da tunanin ina zasuje?
Asmee tace "karmu damu ba zamu rasa wajen zuwa ba Allah dai yaji kan mimi yasa mutuwa hutu ce a wajenta watakila idan ta rayu zatasha wahala Allah yasan me yake yi yasa ya ɗauke ta"
mesnat tace "ameen ya Allah"

sun fito da kayansu jikinsu duk a mace, basu san inda zasuje ba, a gefen titi suka zauna asmee tace "bari na siyo mana wancan abin da naga mutane suna siya"
zuwa tayi ta tsaya itama tana ganin yadda ake siya, sai kallon ta suke bata damu ba tace a bata itama guda biyu, ice cream ne aka bata akan tsinke gani tayi abin kaɗan kuma kuɗi dayawa ta bayar ta zaci za'a cika mata leda, nan fa tace bata yadda ba sai an kara ko a bata kuɗinta, rigima suka fara da meshi meenat ganin haka taje da sauri tana janta tace "dan Allah asmee kiyi hakuri watakila da tsada ne abin"
tace "kalli fa kalli wannan abin kaɗan ɗin sai wannan shegen tsinken me uban tsayi shine zaice kuɗina ya kare?"
janta asmee take yi me ice cream yana zagi tana ramawa, wani mota ne baki jeep ya tsaya a wajen yana kallon yadda suke rigima da kyar meenat ta samu ta jata zasu tafi sauke glass na motan yayi yana cire bakin glasses na idonshi domin tabbatar da wacce idonshi suke mishi karyan ya ganta, idanu ya zaro yace "meenat?"
kallonshi tayi ta taɓe baki taja Asmee suna tafiya, fitowa yayi daga motan yace "meenat baki ganeni bane? nine fa sarkin gadi na gidanku"
tsaki taja tace "Asmee kinga irin waɗannan ƴan iska ne so yake ya nuna ya sanni daga baya ya cuceni"
Asmee tace "amma kamar yadda yake maganan fa kamar ya sanki"
tace "mu tafi dalla"
tafiya sukayi shi kuma ya shiga mota yana binsu, asmee tace "yana binmu fa Ameena ko dai da gaske ya sanki?"
tace "bai sanni ba ɗan iska ne"
tafiya sukeyi waya ya kira ya sanar musu yaga meenat, a rumfan me shayi suka zauna suna jiran ya dafa musu indomie sabida yunwa, gani sukayi dogalin gidan sarki sunzo cike fam da mota, Asmee tace "me suke nema?"
mutumin ne ya fito daga mota yace "kun ganta wallahi itace"
meenat ta rike hanun Asmee tace "tashi mu gudu"
tashi tayi zasu gudu suka taresu, ɗaukan meenat sukayi zasu tafi da ita tana ihu tana cewa su saketa bata sansu ba suka sata a mota, Asmeeta ganin haka ta fara cewa "saide ku tafi damu tare wallahi na zan bari kuje ku cutar da ita ba"
a motan suka sata itama suka ja motan suna tafiya, sai kwacewa take tace "satani zakuyi ku sakeni nikam"
kuka suke itada Asmee domin duk zatonsu satasu akayi, gidan sarki aka kaisu sai rarraba ido suke, ɗaukanta sukayi cak asmee tana cewa "ku sake ta"
da haka har suka shiga da ita ciki Asmee tana bayansu, Ammi da sauran ƴan gidan duk suna falo harda Abi wanda ya kasa zaune ya kasa tsaye sai safa da marwa yake, tana ganinta a tsakiyan falon tace "me na muku zakusa a kamani? me nayi?"
ya kaseem yace "meenat?"
tace "ni sunana ba meenat ba ban sanku ba"
matsowa Ammi take wajenta baya take tana cewa "ku barni na tafi ban sanku ba"
plate ɗin hanun Aneeta ne ya faɗi ya tarwatse ganin meenat a tsakiyan falon, jikinta ya fara rawa, ammi tace "meenat ki nutsu mune iyayenki nan gidanku ne"
bin gidan take da kallo tace "nan ba gidanmu bane gidanmu yana kauye"
kaseem yace "akwai matsala ta samu buguwa a kanta kuma saita kara buguwa zata dawo daidai"
Ammi cikin damuwa tace "wani irin buguwa kenan kaseem?"
yace "akwai abinda ya samu kanta dole sai irin abun ya kara samunta zata dawo daidai"
Asmeeta dake waje ta manta tsintan meenat sukayi harma ta manta zasu iya samun iyayenta a koda yaushe ita dai tasan koma menene bataso a rabata da Ameena.
hameed ne ya karaso wajen a hankali ya rike hanunta yana kallonta, fizge hanun tayi tana yin baya tace "idan wani laifi nayi muku to kuyi hakuri"
kaseem ne ya bar wajen babu jimawa ya dawo da wani katon sanda me nauyi a hanunshi, idanu ammi ta zaro ganin yana bi ta bayan meenat ɗin cikin sanɗa kada ta ganshi, da ihu tace "kaseem me zaka yi...?"
kafin ta karasa ya bugawa meenat a kanta, rike kan tayi tana kallonshi faɗuwa zatayi hameed zai riketa kaseem yace "karka taɓata barta ta faɗi"
da kallo suke binta a tsorace har ta faɗi ƙasa kanta ya kara buguwa da tiles ɗin, ihu tayi wanda ya ɗauki gidan, Asmeeta dake waje tana jijjiga kofan dole sai sun barta ta shiga tace "shikenan sun cutar da ita, dama masu kuɗi ba imani ne daku ba gashi kun cutar da matar hamma najeeb kuma wallahi ba zai barku ba idan ya dawo ba zai taɓa barinku ba tunda kuka taɓa matarshi"
meenat suma tayi ya kaseem yace "ɗauketa hameed da yaddan Allah idan ta tashi zata dawo hayyacinta"
ɗaukanta hameed yayi yana kallon fuskanta yadda ta koma baka ta lalace, akan sofan ya kwantar da ita duk da Ac dake aiki hakan bai hanata zufa ba, fifita yake mata yana kallonta cikin ranshi yana farin cikin ganinta, alameen ne ya shigo sabi yaji labari an samu meenat, bai kula da Abi da ammi da suke wajen ba kawai yaje ya zauna a kasa kusa da hameed ya rike hanunta daga karshe ya rungumeta yana farin ciki, ya kalli hameed yace "an samu meenat? Allah ya karɓi addu'a na"
hararanshi hameed yayi ganin baima san dasu ammi a wajen ba.
kaseem ne yazo da allura, hameed kallonshi yayi a ranshi yace "indai allura ne wannan shine a gaba"
yace "bari nayi mata alluran ciwon kai dan idan ta tashi kanta ciwo zaiyi"
Aneeta jikinta rawa yake ta kalli sultan sannan ta mishi alama ya biyota, jikinshi a mace ya bita, taja hanunshi cikin ɗakin ta rufe, yace "me kuma?"
cikin ɓacin rai yayi maganan domin ya tsaneta, tace "ka tabbatar kabi duk wani hanya da kasan zaka iya ka hana meenat ambaton sunana, ka hanata faɗan duk abinda ya faru idan ba haka ba"
ya kalleta kallon tsana yace "idan ba haka ba me? kasheni zakiyi? ko ita zaki kashe?"
murmushi tayi tace "kafi kowa sanin me zanyi sultan"
buɗe kofan tayi tace "ya kamata ka zauna kusa da ita domin kada ta farka baka kusa"
fita tayi daga ɗakin, cikin dagulewan lissafi ya fita shima.
meenat bata farfaɗo ba har yanzu, hameed ya kalli ya kaseem da alama meyasa bata tashi ba?
hanunta ya kaseem ya rike yana dubawa a hankali ta fara buɗe idonta da yayi bala'in nauyi, da sauri ta rufe idon ta kara buɗewa, tashi tayi a firgice tace "ammi tana kirana kuma banje ba na kwanta inata bacci"
murmushi kaseem yayi ya rufe ido yana godewa Allah, hameed ne ya riketa shima fuskanshi ɗauke da murmushi, babu wanda yayi mata magana ta sauka akan sofan taji kanta da nauyi tace "wayyo nayi bacci sosai har kaina yayi nauyi, ammi kiyi hakuri kinyi ta kirana bacci nake"
kallon kayan jikinta tayi tace "ammi waya samin wannan kayan me dattin? kece kika canjamin kaya?"
kallon Alameen tayi tace "ya alameen yaushe ka dawo?"
cikin farin ciki ya rungumeta, tureshi tayi kasa kasa tace "baka ganin su ammi ne?"
sakinta yayi yana kallonta with so much love, Aneeta ce take takowa karan takalminta sukeji kwas kwas, hanunta rike da cup cike da juice yellow, gabanta ta tsaya tace "ga juice meenat"
da kallo ta bita tana kallon juice ɗin tana kuma kallonta, so take ta tuna wani abu amma ta kasa tuna komai, cikin rainin hankali da lalaci tace "karɓa mana meenat"
a hankali ta karɓa tasha sosai sannan ta kalli ammi tace "amma ammi kamar...."
Asmee wacce sai yanzu ta samu daman bigesu ta shiga ɗakin a guje, duk suka juyo suna kallonta harda hameed, da gudu taje ta bige glass cup ɗin hanun meenat tace "kar kisha, kar kisha duk abinda suka baki zasu cutar dake ne ki tashi mu bar gidannan hamma najeeb zai dawo tunda yayi alƙawarin zai dawo"
rike hanunta tayi tana janta, da kallon mamaki meenat take binta, fizge hanunta tayi tace "wacece ke? waye hamma najeeb?"
a razane Asmee ta kalleta da mugun mamaki tace "har kin manta hamma najeeb naki? kin manta nice Asmeeta kawarki kuma ƴar uwarki ta kauye"
taja hanunta tace "na san abu suka baki na maye shiyasa kike faɗan haka muyi sauri mu bar gidannan"
kwace hanunta tayi tace "wai ina zaki kaini?"
tace "ammi wacece wannan?"
ya kaseem a ranshi ya tuna idan har aka bari yarinyar ta kara tuna mata abinda ya faru ƙwaƙwalwanta zai kara samun matsala domin zata fara tunani me zurfi, asmee zatayi magana yace "security"
shigowa security yayi cikin girmamawa yace "gani"
nuna Asmeeta yayi yace "fita da ita"
asmee tace "babu inda zanje wallahi babu inda zanje"
ɗagata yayi zai fita da ita tace "Ameenah kenan kin manta ni? kin manta mimi?"
Abi yace "security?"
tsayawa yayi 
yace "da alama batada kowa ka kaita wajen bayi daga yau ta zama baiwa"
yace "Allah ja da ran sarki an gama"
fita yayi da ita tana wurga kafa tana cewa ya sake ta, ɓangaren bayi ya kaita wurgi yayi da ita a wani ɗaki ya daka mata tsawa yace "nutsu ƴar talakawa nan gidan sarki ne, kuma wallahi zan faɗa miki gaskiya kuskure kaɗan kikayi zaki iya rasa rayuwarki domin kasheki za'ayi kuma babu abinda aka isa ayi musu, idan kika kuskura kikace zaki faɗi wani abinda zai shafi gidansu ko kuma wani abinda zai kawo musu matsala ƴan uwanki ba zasu kara ganinki ba zaki ɓata ɓat sabida haka kija bakinki kiyi shiru duk abinda kika gani kiyi shiru kuma duk abinda kika sani kiyi shiru matukar kinaso kiyi tsawon rai"
tsit tayi tana kallonshi har ya gama yace "nan shine ɗakinki ku biyar ne a wannan ɗakin za'a kawo miki uniform kisa daga yau kin zama baiwa"
juyawa yayi zai tafi sai kuma ya dawo yace "gargaɗi na karshe wanda idan kinji to kin taimaki kanki idan kuma baki ji ba to ke kika sani, duk ranan da kikayi kuskuren gudu a gidannan idan har aka gane sunanki gawa, bayi sunfi a irga wanda suke gudu amma ana kamasu babu wanda ya taɓa nasara zanso ki bini na nuna miki wani sirri wanda zai taimaki rayuwarki"
a hankali take binshi da ido, sai kuma ta tashi cikin tsoro tabi bayanshi, gani tayi ya kaita wani waje me nisa a cikin gidan, yaye mata bakin labulen yayi taga mata ɗaure cikin yunwa da uniform na bayi a jikinsu wasu ma tanada tabbacin sun mutu, a tsorace ta kalleshi yace "wannan duk gudu sukayi niya aka kamasu kinga yadda rayuwarsu ta zama"
yace "muje"
binshi take a baya yace "kin san meyasa na faɗa miki duk wannan?"
ta girgiza kai, yace "sabida bana taɓa mantawa akwai watarana da mamana batada lafiya kuma an kasa gane me yake damunta tayi jinya sosai kamar zata mutu har mun cire rai da ita, sai akace akwai wani wanda yake bada magani a wani kauye aka mana kwatance babu ɓata lokaci muka tafi kauyen kin san waye ya bamu magani har ta samu lafiya?"
girgiza kai tayi da idanunta wanda suka kara girma yace "yayanki amma a lokacin kina karama bazan taɓa mantawa da fuskan yayanki ba hakan yasa ina ganinki na ganeki, shiyasa na faɗa miki duk wannan sirrin wanda ba kowa ya sani ba, kuma zan haɗaki da kawa wacce komai zaku rinƙa yi tare na yadda da hankalinta, wannan gidan akwai sirruka dayawa wanda idan kikaji tsinkewan zuciya ba zai barki ki rayu cikin nutsuwa ba, amma zanso ki iya bakinki, tunda na ganku tare da meenat nasan ku kuka tsinceta sabida yayanki kullum yana wajen neman magani a daji, to abinda nakeso ki sani shine basaso meenat ma tasan kunyi rayuwa tare sunaso su ɓoye matukar kikace zaki faɗa mata wallahi ba zaki kara ko kwana uku a duniya ba"
jikinta yana rawa yace "kar kiji tsoro idan kin kiyaye babu abinda zasu miki koda kin san wani sirrinsu kada ki nuna kin sani kinji?"
tace "to na gode"
har ɗakin ya kara rakata, wata kyakkyawar budurwa yace "salma ga baƙuwa ki rinƙa kulawa da ita idan kinga zata ɓata ki sata a hanya, kizo ki karɓa mata uniform nata"
ta kalli Asmeeta tace "ya sunanki?"
zama tayi sabida jiri tace "sunana Asmeeta"
tace "sannunki"
fita tayi domin karɓo mata uniform, shiru tayi ta dafa kanta wannan wani irin masifa ne yake tunkarota ko kuma tace ya sameta?

_Jiddah Ce...
 08144818849