Abin Da Babba Ya Hango, Fita Ta Biyu

Bacci yake ji amman baya jin zai iya baccin kirki matuƙar ZULFA'U bata saurare sa ba, sai dai ta yaya?.

Abin Da Babba Ya Hango, Fita Ta Biyu

Fitowa ta biyu


RUBUTAWA; DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.

بسم الله الرحمن الرحيم 


A parking space ta yi parking kana ta fito daga cikin motar tana taku a hankali kamar wacce bata son taka ƙasa.

Jin shigowar mota cikin gidan ya sanya sa saurin yaye labulen taga yana me ƙare mata kallo daga sama har ƙasa, fara ce sol kyakkyawar gaske sai 'yar zagayayyar  fuskarta mai ɗauke da dara daran idanuwana sai hancinta mai tsayin gaske yayin da bakinta yake zagaye ɗauke da manya manyan pink lips doguwa ce ba sosai ba, bata da wani jikin azo a gani daga ganin ta kaga kalar Buzaye.

Sauke idanuwansa ya yi a kanta a cikin ransa yana faɗan "ga kyau har kyau amman ba a gurin da ya dace ba."

Shigowarta ɗakin tana taku a hankali yayin da bakinta ke fitar da sautin ƙarar cingam ya sanya shi mayar da hankalinsa kanta.

Ko kallon gurinda yake ba tayi ba ta yi shigewarta ɗakinta tana faman juya mazaunai.

Tashi ya yi daga kan kujerar da yake yabi bayan ta, yana shiga ɗakin aka fara  kiran sallah.
Da hanzarinsa ya fice daga ɗakin ya nufi harabar gidan suka gabatar da alwala kana suka nufi masallaci shi da Ayuba.

Sai da suka gabatar da isha'i sannan suka dawo gidan.

Sallama ya yi wa Ayuba sannan ya shige , bakinsa ɗauke da addu'oin samun nasarar shawo kanta.

Sai dai me?.

A ƙargame ya tarar da ɗakin nata , jikinsa a sanyaye ya nufi nasa ɗakin.

Zubewa ya yi a saman gado yana me tunanin wai inane zai je ya samowa ZULFA'U kuɗin nan ko hankalinsa ya kwanta.

Wayarsa ya janyo yana duba kwanan wata. jikinsa ne ya yi sanyi ganin 9feb, "ko yanzu da sauran lokaci kamin a fara albashi", ya faɗa yana mai ƙara duba wayar domin ya tabbatar da gaske ne ko kuwa idanuwansa ne ke yi masa gizau.

"Lallai haka ne kam" ya faɗa yana me wurgar da wayar gefen gadon.

Bacci yake ji amman baya jin zai iya baccin kirki matuƙar ZULFA'U bata saurare sa ba, sai dai ta yaya?.

"Ai ke dai bari Hajiya Turai gobe zan je wajen nakan tudu don naga kwanannan  kansa ya fara hayaƙi, duba ki ga yau kwana biyu kenan fa da yi masa maganar ina buƙatar dubu ɗari kacal amman ya tsaya yimin kwana kwana, yana son ya ce min bashi da dubu ɗari ne , zan shigo ki raka ni."

Banji me wancen ɓangaren aka ceba, sai kawai naji ga ta kwashe da dariya kana ta ce "barshi saina nuna masa dani yake zance, Allah zan bashi mamaki."

Ko wannan karon banji me waccen ta faɗa ba , na daiji ta ce "okey saina shigo, ki shirya da wuri wuri tun 8am zan shigo."
Kana ta yanke wayar, tana me ƙara gyara kwanciyarta a saman makeken gadon ta.


Ya jima yana juyi kamin ya samu ɓarawo ya sace sa wato bacci.

★★★★★★

Kiran sallar farko a saman kunnensa a kayi sa, miƙewa zaune ya yi yana me karanto addu'ar tashi daga bacci, kana ya sauko daga kan gadon ya nufi banɗakin dake cikin ɗakin.

Ruwa ya watsa kana ya zura jallabiya fara ya fito, ɗakinta ya ƙwankwasa duk da yasan ba tashin zata yi ba, amman ai gwanda ya fitar mata da haƙƙinta.

Lokacin da taji bugun ƙofar tsaki kawai taja ta ƙara jan rufa tana me ƙara lafewa a saman gadon.

Jin shuru ko motsinta beji ba ya sanya shi , yi gaba don gudun kada jam'i ya wuce sa.

Sai 7am ya shigo gidan hannunsa riƙe da carbi , a saman benci ya zauna suna gaisawa da Ayuba me gadi.

7:10 ya miƙe ya nufi ɗakinsa domin shirin zuwa wajen aiki.

Sai 7:30 ta miƙe daga kan shimfiɗar ta nufi ban ɗaki, brush kawai tayi ta fito ta janyo jikkar da take ajiye kayan maƙulashe a ciki , fitowa ta yi da manya manyan biscuit ta hau ci, sai da ta ji cikinta ya ɗauka sannan ta kwashe ragowar ta mayar a cikin jikkar sannan ta miƙe ta janyo mai ta hau shafawa.

Shiri ta yi sosai kamar wacce zata je gasar kyawawan mata , ba tare da tayi sallah ba balle shi wanka ta rataya 'yar jikkarta a kafaɗa kana ta janyo ɗakinta ta rufe.

Ba kowa a Parlour hakan ne yasanya ta ficewa daga cikin sa ba tare da wani jinkiri ba.

Jin ƙarar mota ne ya sanya shi saurin fitowa daga cikin ɗakin hannunsa riƙe da key ɗin motarsa.

Tun kan yakai da ficewa daga cikin parlourn yaji ya daina jin kukan motar.

Komawa ya yi cikin parlourn ya zube a saman kujera yana faɗan "Ya Allahu."

Ya jima gurin zaune ganin ba sarki sai Allah ya fice daga cikin gidan gaba ɗaya ya nufi ma aikatar su.

Tafe take a cikin motar kiɗa kawai ke tashi a ciki, ita kuwa sai faman girgiza kai take yi alamun waƙar na shigarta.

A dai dai wani ɗan madaidaicin gida ta yi parking tana me fitowa daga cikin motar, kana ta nufi cikin gidan.

Gida ne ɗan madaidaici, mai ɗauke da ɗakuna biyu , daga shigarka gidan zaka fara cin karo da ledodin kayan ciye ciye bar katai ba tsari.

Tsalla ke ledodin ta fara yi kamin ta sadu da ainihin gidan.

Cikin ɗaki ta yi kai tsaye.

Kwance take saman katifa daga ita sai ɗan guntun wando sai breziya da take sanye da'ita.

Ta yi ɗay ɗay ɗay a saman katifar ya yinda gashin kanta yake babbaje da shi , sai sharar bacci take yi.

Duka ta yi mata a saman cinya wanda ya sanyata saurin miƙewa.

Harara itama ta sakar mata sannan tace "to meye naki a ciki?."

"Oya ni dai ba faɗa nazo yi ba, miƙe ki je ki shirya muje, kinsan ko yanzu mun makara sai mun isko layi sosai".

"Karki ga laifina kiga laifin Ruka don ita ce ba ta tadani ba, kuma sai da na gaya mata wurin da za mu je amman tana gama shirinta ta fice ta barni a kwance."

"Ruka anan gidan ta kwana ne?".
"Eh mana, mutuwa ake fashi ko hisabi¿."

"Ba'a fashin komai amman ya kamata ku zo ku daina wannan ɗabi'ar gaskiya ba mai kyau bace ba."

"Ke yanzu gurin da zaki je guri ne mai kyau?" Hajiya Turai ta faɗa.

"Ko ba mai kyau ba ne ba, Allah yafi wannan lalacin da kuke yi, ni kin ganni nan komai iskanci na wallahi bazan iya neman 'yar uwata mace ba, kyamar abin nake yi gaba ɗaya, plx kuma kuzo ku daina dan Allah."

Wucewa ta yi ta nufi hanyar waje ba tare data ce da'ita komai ba.

Taɓe baki ta yi tana faɗan "ai dukan ku bakwason gaskiya."


Zaune yake a saman kujera , gaba ɗaya ya zurfafa duniyar tunani.

Harya shigo office ɗin besan ya shigo ba, sai da ya sakar masa dun du a baya sannan ya yi firgigit yana rarraba idanuwa.

Jan kujerar dake fuskantar tashi ya yi ya zauna sannan ya kallesa ya ce "wai anya abokina lafiya kake kuwa kwana biyu?."

Sauke nauyayyiyar ajiyar zuciya ya yi sannan ya ce "ba lafiya ba kam, wallahi Bash ina cikin tashin hankali kwana biyunnan, gaba ɗaya al'amuran ZULFA'U suna neman su kwance min kai, mace gaba ɗaya bata da lokacin komai da kowa saina yawo da neman kuɗi?, gaba ɗaya 2days ta fitineni saina bata dubu ɗari bansan me zata yi dasu ba."

"Ni kuwa kaga yanzu ba kuɗi a hannuna shekaran jiya na harhaɗa kuɗina gaba ɗaya na bayar a shigomin da waɗansu Atamfa sabon design a ƙasar Jamus, kuma gashi ta fitine ni gashi yau 10  balle nasamu a abani albashina a wancen gurin da nake ."........️

Za mu ci gaba a gobe......