ANA BARIN HALAL..: Fita Ta 33
ANA BARIN HALAL..: Fita Ta 33
*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE* l
*®️GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
_(Gaskiya Dokin Ƙarfe.Burin Mu Faɗakar Da Al’umma Domin Ribatar Duniya Da Lahira.)_
*BISMILLAHI RAHMANIR- RAHIM*
Idan kana/kina sha’awar:
_**Updates akan tallafin gwamnati (Grant & Loan)._
_**Hanyoyin samun kuɗi ta kasuwanci na online._
_**Sana’ar hannu da za ki iya yi daga gida._
_**Dabarun amfani da waya wajen samun kuɗi._
_To wannan group ɗin na Business/Grant/Loan naku ne! Zaku samu labarai kai tsaye + shawarwari masu amfani in sha Allah._
*Join yanzu don kada ku rasa sabbin damarmaki*
https://chat.whatsapp.com/C64wC3IDhW6FtwjSpWWDiL?mode=ac_t
*Page 33*
*INA UWARGIDAYEN SUKE? NACE INA UWARGIDAYE MASU CAPACITY SUKE, IDAN BAKI YI MATSA GA MASU* *AUTHOURITY, NACE TSAYA IDAN BAKIYI GA AMARE MASU AUTHOURITY,* *IDAN KIN SHIRYAH GWANGWAJE SHINFIƊAR MAIGIDA,* *TOU KI ƘYALE ƳAN LOCALLITY KI MATSO KI SAYI NAKI,* *BEDSHEETS ƳAN GASKE, KU MATSO KU YAƘI PORVERTY DAGA TASKAR HALIMA YISUF GWARZO, INA MAI TABBATAR MIKI IDAN KIN SHIMFIƊA ZAKI ZAMA MAI CAPACITY MAI AUTHOURITY,* *DOMIN KI WANKE ZUCIYAR MAIGIDA YA HASKAKA,*
*MUNA AIKAWA DA SHI KO'INA A FAƊIN ƘASAR NAN.*
*DOMIN SAYEN ƊAYA KO SARI, KU TUNTUƁE NI TA WANNAN LAMBAR*
08064586559
**********
Bayan motan muka shiga mu uku, hadiza, zainab da kuma ni, tunda muka shiga na kama bakina nayi shiru, daga hadiza sai M.G suke hira a tsakanin su, daga ni har A.G babu wanda aka ji bakin shi har muka isa gidan amaryah, sun daɗe a waje kafin suka tafi, da niyyan after magrib zasu zo su ɗauke mu.
Buɗan kan yayi kyau sosai, amaryah tafito cikin Alƙyabbah fara mai rastin golden, tayi kyau sosai da ita, ango sai wani washe baki yake cike da farin ciki, ana idar da sallan ishaa su Yayah M.G suka zo, wayana naga call ya shigo da baƙon number, har sai da naga zai tsinke tukun na ɗauka, ko a bacci aka tashe ni bazan kasa gane muryam shi ba, "idan kun shiryah muna waje", iya abun da ya faɗa kenan ya katse wayan, murguɗa baki nayi na share shi, don lokacin angwaye sun shigo kenan, haka ƙawaye da angwaye sukai ta hira da tsokanan juna, ni da zainab dai bakin mu shiru, amma hajjah khadijah kam sai zuba ake tayi da sauran friends ɗin amaryah, mudai bamu fito ba sai wurin 8:30, kuma M.G basu sake ƙirana ba kuma basu tafi ba, angwaye ne suka fara ɗaukan ƙawaye, sai lokacin naji wani irin tausayi da kaɗaici ya zo mun, Allah sarki maryam yanzu munyi nesa da junan mu, duk sai naji babu daɗi, muna haɗa ido da ita naga idonta ya cika da wahaye, da dabara nace zanje kitchen na ɗauko ruwa, sai da na fita na ƙira su hadiza a waya, suma cikin dabara suka fito, ummitah da hafsy ma fitowa sukayi, kaman sun san mun ƙaro ko kuma da ma suna da shirin hakan sai naga kowan su a motan shi yazo, babu yadda na iya dole na shige gaban motan A.G, domin muna fitowa naga ya ƙira ummitah da hafsy ya buɗe musu bayan motan shi, sannan ya bar gaban a buɗe ya wani ƙura mun ido, M.G dai yana ta wani sake murmushi a fuskan shi ya buɗewa hadiza gaba, ya buɗewa zainab baya, suna shiga naga ya rufe, dole na wuce gaban motan A.G ɗin na zauna, ko kallon inda nake baiyi ba ya tayar da motan shi, ina jin su hafsy suka gaishe shi amma ni nakasa buɗe baki na gaishe shi, sai ma juya kaina danayi ina kallon waje ta glass ɗin motan, chan na tsinko muryan shi yana tambayan su hafsy, "hafsat me kuke son ci"? Da yake ba mutunci bane ya ishe ta sosai kawai sai naji tace, "tou nidai nida aminaiyata muna ƙauna da kaza, kazar bauchi club, ita kuma Adda suna mutunci da tsiren wurin, don tana son harkan tsire," tana faɗa ummitah na taya ta da, "ae har soya milk Adda tana korawa time to time", ka marasa mutuncin ko dariya basuyi ba sai wani ɗagawa juna kai suke irin alaman kowa ta faɗi dai-dai, murmushi mai ɗan sauti naji A.G yayi, wanda har sai dana juya na kalle shi, "ku kuma kuna ƙauna da wani abun shan"? Ɗan dariya hafsy tayi tace, "ae muna madaran son coca-cola, wataran har pepsi mukan kora, idan ka ganmu da yogouth tou mutanen mu suna na, dole suke haɗamu da shi, har mun saba sha yanzu".
Ni wallahi hafsy da ummitah tsoro suke bani, yarah gaba ɗaya babu kunya a idon su, don wani dariya suka kwashe da shi suna wani godiyan iskan ci lokacin da yace, "yanzu dai a haɗa muku coke,pepsi,yogouth"? Dariya suka kwashe da shi suna godiya muke Babban yayah, kace har gobe zamuyita sha, don idan Allah ya kaimu sai munyi order hajiya shawarmah, sai mu haɗa da yogouth ɗin, yanzu mu karya ƙashin kaza da coke da pepsi na ummitah", murmushi yayi ya miƙa hanyan bauchi club, nidai kaman na fashe da kuka saboda haushin su hafsy, sai wani leƙo kai gaban motan suke kaman wasu sukaye suna ƙara godiya, har muka shiga bauchi club fuskan shi da murmushi, wanda hakan yake ta bani mamaki, amma nasan tsantsan shaƙiyan cin su hafsy ne yake bashi dariya, muna parking naga motan M.G ma yayi parking a gefen mu.
Tare suka buɗe motan suka fito, suna fita na juya ina hararan su, da sauri hafsy tace, "wallahi Adda kika ce wani abu recording ɗinki zanyi, yana shigowa na kunna mishi", ta faɗa tana ɗaga wayanta sama tana nuna mun, ita kuma ummitah cike da shaƙiyanci tace, "ae best friend nikan ma har na ɗana, tana kwabsa mana zamu antaya mishi", juyar da kaina kawai nayi na rabu dasu, sai wani dariyan rashin mutunci suke tayi, zuwa chan kaina yana ƙasa naji muryan hafsy tace, "wooww gaskiya gayen nan ƙarshe ne, friend kiga wani taku da yakeyi kaman wani Basaraken zaki, gaskiya matar shi ta more da haɗaɗɗen miji ɗan wanka da aji," ummitah ta amsa mata, "da kuma dace da miji ɗan ƙamshi, saboda Allah hafsisin london bakiji ƙamshin motan shi kaman daɗin zai saka kiyi bacci ba? Nifa na tsorita da gayen nan, don har na fara manta sunan saurayina, meye ma sunan shi friend"? Hafsy na dariya tace, "shege ƙamshi, ƙamshi ya gagara ae, sunan samrayinki, isiyaku zakaran bauchi club", dariya suka ƙyalƙyale da shi wanda har saida suka saka na ɗan dara, don tsiyar su tana da yawa, kuma saida suka saka na ɗan ɗaga kaina ma dubi A.G da yake shirin ƙarasuwa, ashe ya chanja shigan shi ba irin ta ɗazu bane, yanzu wata faran yadi ya saka mai ɗan shara -shara, sai wani lumshe ido yakeyi shi kaɗai yana tahuwa, da sauri na sauƙe kaina ƙasa zuciyata na bugawa da sauri -sauri,gefen shi kuma M.G nashi ne.
Buɗe motan yayi ya shigo, juyawa yayi kaɗan baya yana duban su hafsy da suka wani nutsu kaman gaske, murmushi yayi yace musu, "yanzu insha Allahu zasu kawo, sai kuma shawarman account ɗin waye za'a tura so dat goben sai kuyi ordern,", da sauri ummitah tace "zubasu kawai a acct ɗin Adda, don duk ƙawancen mun nan da kake gani akan almanu sai mu munafurci junan mu, bawa Adda kawai don ita mai amana ce, zata mana order gobe, inda chanji ma bazata ha'ince mu ba zata raba mana", tana faɗa hafsy na gyaɗa mishi kai, "eh yayah A.G hankaɗa su wurin Adda, don mu akwai ɗan sauran nutsuwa a tare da mu, ƙarshe idan ma ɗayar mu kasa sai ta ha'inci ƴar'uwarta duk ta saka rechage card ko data, don ba kan gado bane wataran damu".
Abun mamaki wallahi dariya A.G ya ƙyalƙyale da shi, sakarun suma suka shiga taya shi, nidai kaman na buɗe window na falfala da mugun gudu don kunya, tsabar wayo ne fah yasaka suka gaya mishi haka, wato *AUNTY NICE* na daɗe banga tsageru irin suba, kuma hattah yayah ishaq da yayah umar basu barsu ba, yanzu zasu haɗe su zaga su, halin sune yazo ɗaya shiyasa suke abota, kuma ko ƙaryah ɗaya tayi bazaki taɓa jin ɗayan ta ƙaryata ɗayar ba, sai dai itama ta tayata, gasu da shegen wayon tsiya, don ɗaya tana faɗan abu ɗaya take gane ina aka dosa, shidai A.G gaba ɗaya nishaɗi yake da shi a lokacin, muna haka har ma'aikatan suka kawo saƙon, bayan motan duk aka zuba musu, sannan A.G ya tayar da motan yana cewa, "wannan leda ɗaya kajin kune sai aka san muku tsiren kaɗan, don kada kuyiwa su Adda wayo ku cinye nasu, ɗayan ledan kuma na ummin mune, nasu Adda kuma yana hannun jama'an ta, tare dana hajiya ummah, kuɗin ku kuma zan zuba a acct ɗin Addan mu, haka yayi"? Ƙyalƙyala dariya sukayi lokaci ɗaya, hafsy na wani gyaran muryah tace, " yayan mu insha Allahu na maka alƙawari yau zan raba dare na tayaka da addu'an Allah ya baka mata ta gari wanda bazata hana mu zuwa gidan kaba, wacce zata barka kana mana abun duniya, kaga yayah muhammad da yayah Ahmad ae tsantsar addu'an da nake musu ne idan sun haɗani da abun duniya Allah ya amsa, kaga ae matan su nagari ne? Tou amma duk basu kai wannan aminiyata ɗin ba, don yayah umar yana kyautata mun, shiyasa nafi dagewa da roƙa mishi ta gari, kuma cikin ikon Allah sai ya samu Ummitah, ae ummitah mutum ce har da ƙari, matsalarta sai an dage ta bar yayah umar ya tara na kanshi, saboda bakinta baya hutawa da ciye-ciye, tou kaima ka shiga sahun addu'a na," dariya ummita ta sake ƙyalƙyalewa da shi tana duban hafsy tace, "Allahummah Ameen ƙawata, ae duk zamu saka shi cikin addu'a, amma nikan sai daga gobe idan Allah ya kaimu, don gaskiya yau kam naci naman nan bacci zanyi don na gajji, amma gobe kam idan Allah ya kaimu, zan maka addu'a Allah ya baka nutsattsiyar mace irim Addan mu, don yanayin ku ɗaya wallahi, akwai nutsuwa akwai alheri ". Ta faɗa tan turo kanta gaban motan, ni dai narasa dalilim da ya saka na haɗa hanya da su, don ni har wani jiri -jiri nakeji tsabar haushin su, a haka muka ƙarasu cikin gidan mu, inda A.G yake ce musu, "nagode da niyyan ku, ae ko bakuyi ba nagode, kuma Allah ya amsa bakin ku ya bani Addan na ku", ya faɗa yana ɗan maida idon shi kaɗan gefe na, shashun kuma haɗa baki sukayi suna wani ihun murna, ummitah nacewa, "wallahu kun dace, nifa ɗazu har mafarkin ido biyu nafara dana ganku, nace lallai za'a haifo yara ƴan gaske anan, wayaga kyau na dukan kyau, nutsuwa Na dukan nutsuwa, Allah dai ya tabbatar da alkairi, Allah yasa ka dace da samun zuciyata", murmushi yayi yana wani mun kallo da ya saka duk jikina fara rawa, ƴan tsiyar kuma sai wani smilling suke suna ƙara turo kawunan su gaban motan, ni da ma M.G ne ya kwashe su da nafi samun sauƙi, yana tsayar da motan na kai hannu zan buɗe sai naji ta lock, juyowa nayi na kalle shi, "yayah xaki fita bayan baki amsa musu addu'an su ba?" "wallahi kam yayah, kuma ma banga ta baka acct ɗin nata ba hehehehh", hafsƴ ta faɗa tana wani dariyan iskanci, kallo na yayi yace bani acct ɗin kafin ki fita," sannan ya buɗewa su hafsy ƙofan yana ƙara musu godiya, sai wanidariyan daɗi suke yi suna mishi godiya, sannan ummitah ta ɗan leƙo ta glass tace mun, "Adda nikan zan ƙira mama nagaya mata anan zan kwana, kuma a side ɗin ummie zamu kwana don kada mu takurako hajiya ummah ta takura mu, don tana ganin mu da ledan nan zata ɓoye nata ta saka ido a namu, gara muje wurin ummie, ita sai ma taci ta rage mana mu ƙara da safe, zamu ƙiraki zuwa anjima muji yayah labarin alert mai kukan tarararat", tana gama faɗin haka sukayi ciki da sauri suna dariya.
Tsaki nayi ban shiryah ba, hakan ya saka naji A.G ya wani ɗan tuntsire da dariya, a hankali yace, "kai yaran nan sun sakani nishaɗi, ballantana ma da suka haska mun ashe Adda tana son tsire mai ɗan ƙarago, ashe bazan sha wahalan wani sayan kaza ba" ya faɗa yana duban fuskana, turo baki nayi gaba, wanda sai lokacin bakina ya buɗe nace, "kai fa baka san kalan ƙaryan su ba fah? Maƙaryata ne na gasken-gaske, kuma wallahi wayo suka maka don ka saya musu nama da shawarma, haka sukeyi wa su yayah Ahmad, nidai babu ruwana", na faɗa ina maida fuskana kanshi da naji dai yau sai dariya yakeyi, "wayace miki ban fahimci wayon su ba, ae abun da yaringa sakani nishaɗi kenan har kika ga ina dariya, bakiji wayon da suka mun ba na maganan shawarman su na gobe"? Ya faɗa yana ƙara sautin dariyan shin, nima ɗan murmushi najyi kaɗan nace, "sun ɗauka ba'a gane sune ae, ni tsoro suke bani ma wallahi, harta masu son su basu ƙyale su ba", dariya ya ɗan sakeyi kaɗan yace, "nidai sun sakani nishaɗi, kin san mai wayo wani lokacin ɓuya yake a bayan wayon shi, bakiji sunce a tura miki kuɗin acct ɗinki ba, kinsan meye dalilin su"?
Dariyan naji ya ɗan zo mun, son nasan shima ya fahimce su.
Nima dariyan naji ya zo mun, sai na ɗan dakata da sauraren Ayshaa na ɗan dara, itama dakatawa tayi tana darawa, domin tuna lokacin da abun ya faru, gashi yanzu duk anzama iyaye,
*AUNTY NICE*
managarciya