DUHU DA HASKE: Fita Ta Shida

  DUHU DA HASKE: Fita Ta Shida


  DUHU DA HASKE: 


     Na
*Jiddah S mapi*


*Chapter 6*


                 ~Manal meyasa zaki tafi da wuri baki bari na tashi a bacci ba?"
murmushi tayi tace "sorry Ammi akwai abinda zanyi ne yau a company an sani zane kuma yau akeso ya zama dole na zana kalan kayan a gaban maids ɗina domin su fahimci yadda ake fitar da sabon designing na kaya"
driving take hankali kwance tana waya, tayi kyau sosai cikin riga da wando baƙi na suit ba karamin kyau yayi mata ba, kasancewar yau tanada yin zane shiyasa tasa wannan dressing ɗin, tayi rolling kanta da baƙin jessy veil karami, ta fito sak balarabiya goran ruwa ta buɗe tana sha, ammi tace "har yanzu na kasa tashi manal a cikin kwanakinnan ina jin nauyin jiki gaba ɗaya jikina babu daɗi ga shegen cin abinci dana koya kamar hauka, ko banson cin abinci sai naci kuma dama na ɓoye miki ne sabida kada hankalinki ya tashi amma da naci abinci nake amarwa"
da sauri tace "haba ammi shine zaki ɓoyemin rashin lafiyanki bari ina zuwa"
katse wayan tayi ta kira Dr Aisha tace "kije gida yanzu ammi babu lafiya ki dubata"
katse wayan tayi tace "na kira dr A'isha zata zo yanzu ta dubaki"
a hankali tace "to manal saikin dawo bye"
tace "love you ammi"
ammi tace "love you too"
koda ta isa company bata tsaya ɓata lokaci ba cikin action nata tace "kowa ya shirya zamu fara program yanzu"
duk suka nutsu tsit suna kallonta, babban black boat da tarin fentin zane aka kawo mata, stool ta janyo ta zauna, takalmin kafarta me tsini ne sosai, tasa aka kashe wuta wani abu kamar tv ta kunna a jikin bango kato sosai, ta kawo fentin ta fara zane duk abinda ta zana suna gani a jikin tv ɗin, rigan amarya ta zana me kyaun gaske tayi fentin kalan yayi kyau domin kuwa matured color ta zaɓo wato dark purple da adon black a jiki, color ɗaya ne ya rage ta kara ajiki ta juya fuskanta kamar kullum tace "a cikinku waye zai cika mana sauran kala ɗaya daya rage?"
duk sukayi shiru suna tsoron amsawa dan zata iya koran mutum idan ya faɗi abinda be mata ba, cikin ɓacin rai tace "waye zai cika mana ɗayan color daya rage?"
tsit ko tari bakaji, ranta yayi mummunan ɓaci cikin daka tsawan da yasa duk jikinsu ya fara rawa tace "kuna nufin a haka zakuyi aiki dani baku san komai ba akan zane? idan bana nan aka kawo aiki waye zaiyi a cikinku? ta ya zan zauna babu wanda ya kware a zane kamar yadda na kware?"
cikin ɓacin rai ta kashe tv sannan ta ture black boat ɗin tana huci tace "banga amfanin yi a gabanku ba jahilan banza marasa tunani"
fita tayi a fusace take tafiya kamar zata tashi sama, tana fita suka saki numfashi me kyau domin duk jinin jikinsu ya tsaya da aiki, manal nada kwarjinin da ko wani namijin baida shi, musamman idan ranta a ɓace ko fuskanta ka gani ba zaka iya mata magana ba, gaba ɗayanta fusatacciya ce, zata wuce waje taga me mopping tana cigaba da aiki bata tsaya ba, wani irin mugun kallo ta aika mata da sauri ta durkusa kasa tace "sorry madam"
cikin fusatan da take ciki taje inda take tsaye da sandan mopping da roban ruwan ta kalleta sama da kasa, kanta kasa jikinta yana rawa tace "sorry madam"
itafa babu abinda yake kona mata rai kamar taji ance mata sorry, ta tsani a bata hakuri, roban ruwan ta ɗauka tana cigaba da kallon fuskan yarinyar, ɗaga roban tayi sama daidai kan yarinyar ta fara tsiyaya mata ruwan, kankame jiki tayi tana jin masifan sanyin ruwan kamar daga frij aka ciro, rufe ido tayi tana hawaye, saida ta juye ruwan duka a jikinta sannan ta kifa mata roban akanta ya rufe fuskanta ta juya ta bar wajen, tana fita wayarta ya fara ringing dubawa tayi taga ammi, ɗauka tayi cikin kakkausan muryanta da babu tsoro ko wani shakka tace "ammi na"
cikin murna ammi tace "ki dawo gida yanzu akwai good news"
zatayi magana ammi tace "please manal this is the first time da zan rokeki kibar aikinki ki dawo gida"
a hankali tace "okay ina zuwa"
kallon agogo tayi taga lokaci bai tafi sosai ba, daga inda take ta buɗe motarta da remote, tana zuwa ta shiga ciki ta zauna, ɗaga glass tayi gateman da gudu ya buɗe gate ta fita, gida ta nufa tayi parking a compound ta fito tana tafiya cike da yanga da kasaita, da hanu ta kira wata me share cikin gidan, a tsorace tazo ta durkusa kasa babbar mata ce ta manyanta sosai, tace "gani hajiya"
cike da rashin walwala tace "dr A'isha tazo?"
da sauri tace "eh tazo hajiya"
bata ƙara magana ba ta tafi zuwa ciki, tun a kofan main parlour taga ammi tazo da gudu ta rungumeta, tsananin murna ne akan fuskanta da alama akwai abin farin cikin daya sameta wanda bata taɓa jin irinshi ba, cikin jin daɗi ta ɗaga manal tana juyi da ita, manal murmushi take tana kallonta, saida ta sauketa tace "ammi meya faru kike wannan farin cikin?"
hanunta ta rike ta zaunar da ita akan sofa, itama zama tayi bata saki hanunta ba tace "manal wannan shine karon farko a duniya da uwa zata fara faɗawa ƴarta wannan labarin"
cikin rashin fahimta tace "ammi menene?"
cikin jin daɗi tace "manal I'm pregnant"
kirjin manal ya bada sautin dum dum dum 
idanunta suka kara girma tana kallon ammi kamar gunki, jinta da ganinta suka ɗauke a lokaci guda, ammi tayi shiru tana kallon yanayinta, jikinta yayi sanyi tace "manal?"
ganin jikin ammin yayi sanyi tace "wow am shocked, ammi kenan za samu kani ko kanwa?"
ammi tace "yes manal zaki samu ƙani ko kanwa by god grace"
a ranta tace "kenan zamu zama mu biyu da wata ko wani akan ammi da dady?"
a fili kuma tace "wow congratulations bari na kira dady na faɗa mishi duk da yayi tafiya"
rike wayan tayi tana girgiza kai tace "ba yau ba, gobe zai dawo daga tafiya da yamma kamar karfe huɗu ni da kaina zan sanar mishi kuma zanso kiyi min decoration na gidannan yayi kyau sosai domin nafi son nayi celebration wajen faɗa mishi kuma kema ki tayamu"
murmushi tayi tace "to ammi zan tayaki gobe da kaina zan shirya gidannan domin nasan dady zai fiki farin ciki"
rungumeta ammi tayi tace "manal farin cikin da nake ciki bazan iya misaltawa ba"
hawaye ne ya zubo mata, da sauri ta share mata hawayen tace "please don't cry"
murmushi tayi tace "ina cikin farin ciki"
tace "ammi banda kuka please"
a ranta sam bataji daɗi ba, babu abinda ta tsana kamar haɗa abinta da wani, idan tanada abu tafi son ta zauna da abin ita kaɗai babu wanda zai taɓa, yanzu gani take cikin ammi zai iya shiga tsakaninta da ammi da dady, kawar da tunanin tayi, bata koma wajen aiki ba kuma tayi niyan gobe ma ba zata je ba.

washe gari tana tsaye akan kujera hanunta ɗauke da igiya me yalƙi tana ɗaurawa akan labulen ɗakin, dogon riga ne a jikinta roba roba mara hanu, tayi kyau sosai da hulan net ta cusa gashinta a ciki, cikin ɗakin yayi kyau sai yalƙi ke tashi ta ko ina, ƙamshi ne yake tashi tako ina, ammi ta fito daga ɗaki rike da waya tace "manal gashi dadynki"
tana daga tsaye ta karɓa ta kara a kunne tace "dadyyyy"
yace "yes ya kuke? yau zan dawo"
murmushi tayi tace "to dady saika dawo"
hira sukayi kaɗan kafin ta baiwa ammi tana kallonta tana murmushi tana yin wayan, da sauri ta ɗauke kai taci gaba da aikinta, ammi bayan ta kashe wayan ta kalli ɗakin tace "wow manal kin iya shirya ɗaki You are the best decorator in the world"
murmushi tayi tace "thank you"
leshi ne me tsada a jikin ammi peach color, sai glowing take kana ganinta kage me ciki domin tayi kiɓa sosai basu ankara bane domin har cikinta ya ɗan fito kaɗan, ta zauna akan sofa tace "manal sauko ki huta"
saukowa tayi tana rike bayanta alaman ta gaji, kallon dining tayi yadda ammi ta shirya warmer's ɗin data yiwa dady zazzafan girki ga juice kala kala data haɗa mishi, kallon ammi tayi taga sai kallon hoton dady take yi, tace "ammi bari naje na karɓo cake ɗin dan tamin saƙo ta gama baking"
buɗe wayanta tayi ta nunawa ammi hoton tace "kin gani"
murmushi ne fal a fuskanta ganin an rubuta "happy anniversary to you umar maidawa"
Ammi ce tasa aka rubuta hakan domin kuwa yau anniversary ɗinsu ne suna shekara 28 da aure, tace "yayi kyau sosai nasan idan dadynki ya gani zaiji daɗi sannan na dafa mishi favorite food nashi kiyi sauri kije ki ɗauko kafin ma yaje airport ya zama komai ya kammala"
da sauri ta shiga ɗakinta ta ɗauko wani guntun hijabi tasa, fitowa tayi tana danna remote na motarta tace "bye ammi"
ammi dake fesa turare tace "saikin dawo"
fita tayi da sauri take driving domin taji tana son cin cake, sunada nisa tsakaninsu da me baking ɗin tayi tafiya sosai kafin ta isa gidan, a kofa ta tsaya tana hon bata fito ba kuma bata daina hon ba, ranta ya ɓaci ganin matar bata kawo mata ba a fusace ta juya zata tafi taga matar ta fito da sauri, sauke glass tayi tana kallonta harta karaso wajenta, tace "kiyi hakuri na tsaya neman....."
karɓa tayi kawai taja motar bata tsaya jin me zatace ba, matar da kallo ta bita har ta fita a layin, driving take tana kallon cake ɗin a sama an rubuta sunan dady, ɗago kai tayi tana maida hankali kan hanya, da sauri ta koma baya ganin kamar motar budurwa dady ne a fake gefen hanya, nesa dasu tayi sannan tayi parking tana kallonsu ta cikin tinted glass, gani tayi dady ya sauke glass yana wurgar da ɓawon ayaba, runtse ido tayi ganin yarinyar ta shafa jikinshi tana kissing nashi tako ina tun kafin ya ɗaga glass ɗin har ya ɗaga, buɗe ido tayi a hankali, waya ta ɗaga tayi kira, ana ɗauka tace "nice nazo hotel naku rannan na baka miliyan ɗaya sabida kamin bincike na musamman"
shiru tayi sai kuma tace "ina jinka"
cikin kasa da murya yace "ko jiya suna tare domin anan ya kwana"
murmushin gefen baki tayi lokacin da taga ta fito daga motar tana gyara skirt ɗin dake jikinta sannan daga can gefe me gyaran takalmi ne da alama wanke mata takalmi yake, a hankali tace "thank you"
kashe wayan tayi ta kalli cake ɗin dake hanunta, daidai inda aka rubuta sunanshi tasa hannu ta dama ta watsar a waje, saida taga idon mutane babu dayawa sannan babu motoci a gefen titin ita kuma wacce akace mata sunanta zee tana can hankalinta akan me gyaran takalmi ta kunna motarta da mugun speed ta nufi motar da yake ciki gadan gadan, ganin bishiyan dake gaba dashi kaɗan ta kara gudun, bige motan tayi da karfi ta tura saida taga ya fara gangara kafin ta juya da gudu tayi nesa dasu ta yadda babu wanda zai ganta, ido ta zuba mishi tana ganin alaman hanunshi yana bubbuga jikin glass, hankalin zee ya dawo kanshi ihu tayi ganin motar zata bugu da bishiyan, rufe ido tayi lokacin da motan ya bugu da jikin bishiya atake ya tarwatse ya kama da wuta, ihu zee take yi tana neman taimakon jama'a, mutane suka taru makil a wajen suna kallon yadda motan yake ci da wuta, kowa yana kokarin kashewa amma abin yayi nisa domin har bishiyan saida ya fara ci da wuta, tana zaune daga cikin motan tana murza yatsun hanunta idanunta akan motar har ya zama toka, rufe ido tayi ganin ƴan sanda sunzo wajen zee ta gani ta silale ta gudu sabida tasan dole saita amsa tambayoyin ƴan sanda, murmushin gefen baki manal tayi ganin ta shiga mashin tada motan tayi ta fara binta har zuwa hotel ɗin, facemask manal tasa lokacin da zata shiga ciki, tana ganin zee ta shiga ɗakin hotel zata rufe kofa tasa hanu ta damƙe kofan, a tsorace ta kalleta, murmushi tayi ta cikin facemask taki yadda ta cire sabida tasan ba'a rasa cctv camera, duk yadda taso ta rufe kofan ta gagara, shigowa manal tayi ta rufe kofan gam, jikin zee ya fara rawa domin ta gane itace rannan ta rike mata hanu, a bakin gado ta zauna ta ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya tace "zee zee zee ya naga duk a tsorace kike kamar kin aikata wani laifi?"
shiru tayi tana neman hanyan gudu amma kofa yaki buɗuwa, tace "laa ko dai kinyi kisa ne kin ture mutumin dake cikin mota ya gangara ya bugu da jikin bishiya motar ta kone?"
zaro ido tayi cike da tsoro tace "wacece ke?"
dariya tayi sosai tace "sunana MANAL UMAR MAIDAWA"
idanunta a waje tace "kenan ke ƴar Alhaji ce?"
gyaɗa kai tayi tace "yes ni ƴarshi ce ke kuma fa?"
shiru tayi, tace "kema ƴarshi ce? ko matarshi?"
jin tayi shiru tace "ko dai karuwarshi?"
cikin tsoro tace "dan girman Allah kiyi hakuri ki fita a ɗakinnan bansan komai akan mutuwanshi ba"
dariya tayi sosai tace "to ai nazo ne na kuɓutar dake daga ƴan sanda, kinga wannan video?"
nuna mata video time ɗin da suke cikin mota da kuma time ɗin data fita tayi, sai tace "kinga kin kasheshi sabida ki kwashe komai nashi ciki harda wannan atm ɗin dake hanunki"
sai yanzu ta kula akwai atm a hanunta tace "wallahi talla...."
cikin tsawa tace "shiru"
tsit tayi, tazo gabanta ta tsaya, kwance mayafinta tayi tace "karɓi wannan mayafin naki"
karɓa tayi tace "so nake ki rataye kanki idan kuma ba haka ba sajna kira ƴan sanda na nuna musu wannan video sannan na bada manyan kuɗaɗe a lalatamin rayuwarki"
durkusawa kasa tayi tace "amma kinsan kuskure kike aikatawa na kisan kai? ke ki kashe mahaifinki da hanunki?"
cikin zafin rai tace "zaki aikata abinda nace ko saina kira ƴan sanda kinyi rayuwan crack?"
ganin ta ɗau waya ta karɓi mayafin ta kalli fanka dake ɗakin, ɗaurawa tayi ta runtse ido ta ɗau stool, tana kuka tana rokonta manal ta ɗaura kafa ɗaya akan ɗaya tana kallonta har saida ta rataye kanta taga bata numfashi kafin tasa hanunta a handglove ta ɗau wayarta ta turawa police text cewar "nice zee nice na kashe Alhaji umar maidawa domin na kwashe kuɗinshi amma dana dawo sai naji labarin kuna nemana shiyasa na kashe kaina"
tana gama turawa ta wurga wayan akan gado ta cire handglove ɗin, ba tareda ta taɓa ta ba tasa mata a hanunta sannan ta fice daga ɗakin, motarta ta shiga ta wuce gida, a bakin kofa ta tsaya tayi shiru, a hankali ta tura kofan ta shiga jikinta a mace, gani tayi ammi ta taso a haukace idanunta sun kumbura sunyi jajur ga hawaye dake wanke fuskanta, ta riketa da karfi tace "manal ina waya da dadynki naji yayi wani kara daga nan naji mutane suna ihu wai wuta, ina jinshi yana nishin azaba da ihu har nazo naji yayi shiru, manal ya dadynki ya mutu ne? manal dan Allah ki tasheni daga baccin da nake, shi kaɗai nake dashi shi kaɗai ya ragemin a duniya, manal Allah yasa mafarki nake"
shiru tayi tana kallonta a lokaci ɗaya ta zama karamar mahaukaciya, tana cikin kuka da ihu taji kiran waya, da sauri ta ɗauka cikin ruɗewa tace "hello my love kaine ko ka kirani da wani number domin ka tabbatarmin bada gaske abinda nake tunani ba ko?"
ji tayi ɗan sanda yace "hajiya muna me baki hakuri mijinki ya mutu sannan mun samu gawan wacce ta kasheshi a hotel zamu tura miki abinda ta rubuta ki karanta da kanki"
kashe wayan yayi ammi ta bushe ko motsi batayi, wayanta yayi kara alaman sako ya shigo, tana duba taga abinda aka rubuta, kasa take shirin faɗuwa manal ta riketa, gani tayi ta suma a jikinta idonta rufe, da karfi tace "ammi ki tashi, ammi ki tashi mana"
ji tayi an fara hayaniya a kofar gidansu, kwantar da ammi tayi a gefe ta fita domin ganin meke faruwa, gani tayi mutane sunata faɗan maganganu marasa daɗi "dama ɗan iska ne karuwa ce ta kasheshi"
komawa ciki tayi ta watsawa ammi ruwa a jiki, numfashi me tsayi taja sannan ta buɗe ido a wahale, tace "bacci nake ko manal? mafarki nake ko?"
girgiza kai tayi idonta fam da hawaye tace "da gaske ne ammi dady ya tafi ya barmu"
jin abinda mutanen suke faɗa ammi tayi, a hankali ta tashi jikinta kamar an zare laka, lekawa tayi kofa domin gani da idonta, ji tayi suna faɗan magananganu marasa daɗi, komawa ciki tayi tana shiga falon ta zube kasa a sume, manal ce ta ɗagata ta kwantar da ita akan sofa ta kira dr A'isha, tana zuwa ta fara dubata alluarai tayi mata sannan ta ɗaura mata drip ta tafi, saida ta jima tana bacci a hankali ta fara buɗe idanunta da sukayi nauyi ganin drip a hanunta ta fizge zata tashi tace "ina umar yake? ina yake manal?"
cikin tsawan da yasa jikin ammi rawa manal tace "will you please shout up your mouth"
tsit ko numfashin kirki bata kara yi ba, sai kallon manal ɗin da take a mugun tsorace, idanunta sunyi jajur cikin huci tace "kina ji akace miki a macen da suke zama a hotel tare ta kasheshi, hakan ya nuna bama tafiya yayi ba yana can tare da mace yana cutar dake, kina neman haukata kanki sabida maci amana"
a hankali tace "manal ba...."
a tsawace tace "shiru!!!!!!"
jikin ammi ya fara rawa dan bata taɓa ganinta cikin ɓacin rai haka ba, rungumeta manal tayi ganin jikinta yana rawa, shafa bayanta tayi a hankali alaman lallashi tace "ki koyi rayuwa babu shi, kada naji koda wasa kin kira sunanshi, sannan duk wani abinda kikasan ya shafeshi ki tabbatar kin kona ko kuma kinyi kyauta dasu"
shiru tayi tana jinta, tashi tayi ta shiga ciki, daga kan hotonsu ta fara harma da zanenshi da takeyi, zuwa kayanshi ta fito dasu, ammi tana ganinta tace "manal me zakiyi?"
a tsakiyan falon ta aje taje kitchen ta ɗauko fetur da ashana tazo a gaban ammi tasa wuta, waro ido ammi tayi tasa hanu a baki tana kallonta, zagaye kayan take ta goya hanu a baya tana kallon yadda yake ci da wuta, ammi ganin hoton da suka ɗauka ranan aurensu yana konewa da wuta taje da gudu zatasa hanu ta cire manal ta fizgota, a haukace tace "manal hotona da umar nefa ki barni naje na cire"
kankameta tayi duk dukan da ammi take mata bata ko girgiza ba har saida komai ya kone kurmus kafin ta saketa, faɗuwa kasa ammi tayi akan gwiwanta har yanzu hanunta a baki tana kallon tokan hawaye yana bin kuncinta yana zuba zuwa hanunta, cikin zafin rai tace "to idan kin kona komai cikinshi dake jikina kuma fa manal?"
fuskanta a ɗaure ta kalli ammi sai kuma ta shiga ciki batayi magana ba, akan gado ta faɗa tayi shiru ta rufe ido.

har dare ya ratsa ammi tana wajen bata motsa ba, saida bacci ɓarawo ya saceta manal tazo ta ɗagata ta kaita kan gadonta, zama tayi kusa da ita ta ɗan kishingiɗa akan gadon tana kallon kyakkyawan fuskan amminta, hawaye yana bin fuskanta da haka har bacci ya ɗauketa itama, washe gari ammi ce ta fara buɗe idonta da sukayi mata nauyi, ganin manal kwance a jikinta taji wani irin tausayin kansu ya kamata, manal batada kowa sai ita, itama batada kowa sai manal da kuma umar gashi ya mutu ya barta, share hawaye tayi a hankali ta fara zame jikinta domin zuwa yin alwala, buɗe ido manal tayi a hankali tana kallonta cikin sanyin murya tace "ammi na kin tashi?"
share hawaye tayi tace "na tashi manal"
riketa tayi ta kaita toilet, saida tayi wanka sannan tayi alwala koda ta fito manal ta cire mata kayan da zata sa marar nauyi da mayafi, sawa tayi bata damu data shafa mai ba ta shinfiɗa sallaya ta tada salla, addu'a take tayi tana kuka da haka har tayi sallama ta zauna shiru da carbi a hanunta, manal tazo ta kwantar da kanta a cinyarta tayi shiru.
da haka tayi kwana uku bata cin komai sai ruwan zafi take sha shima sai manal ta tsawata mata kafin take sha, haka suke zaune a gidan shiru babu hira babu komai, dama manal bata hira sai kuma abinda ya faru ya kara sa ta zama miskila domin idan ta zauna bata magana da kowa saide ta haɗa rai kamar yadda ta saba, gara da idan taga dama tana murmushi amma yanzu zata iya wuni ta kwana ta tashi batayi murmushi ba, komai ta maidashi serious, bata wasa bata kallo bata yin wani abu da zaisa taji daɗi a rayuwarta wannan ɗabi'an kuma tun tana yarinya haka take, yau tayi niyan zuwa aiki tun safe ta gama shiryawa ammi komai na buƙata domin bataso idan ta tashi daga bacci ta wahala, bayan ta shirya cikin hijab baki da siririn mayafi tafi gane sa takalmin me tsini, ta fito daga ɗakinta ta shiga ɗakin ammi dake bacci, murmushi tayi ta shafa gefen face nata tace "bye"
juyawa tayi zata tafi sai kuma ta juyo tana kallon ammin, kallon cikinta tayi sai taji gabanta ya faɗi, a ranta tace "wannan cikin be kamata ya zauna ba ya zama dole na zubar dashi"
murmushin gefen baki tayi sannan ta fita, tana fita ammi ta buɗe ido, a hankali tace "alhmdllh tunda ta fita yau zan iya kallon hoton umar ko zanji daɗi a raina"
hotonshi ta ciro daga ƙarƙashin gadon data ɓoye ta fara kallo tana murmushi tana hawaye, tana shafa cikinta tace "baka nan amma ina jinka a jikina, wannan cikin kaɗai nake gani ina jin daɗi kuma ina ganin baka barni ba, koba komai zan haifi ɗan da kaine ka samar dashi, zan haifu mana Umar abinda mukayi Shekara da shekaru muna nema, duk da abinda kayi na yafe maka duniya da lahira domin baka taɓa cutar dani ba a zamanmu da kai, koda sau ɗaya baka taɓa cutar dani ba, nasan kowane mutum da irin ƙaddaranshi kaima Allah ya kaddara maka hakan ne amma nasan ba halinka bane, koda kayi hakan to nasan sabida ni kayi, kanason mace amma kana jin kunyan karamin kishiya sabida na rabu da iyayena domin kai, kuma na tabbata wannan itace kaɗai macen da kake bi, nasan halinka umar nasan abinda zaka iya da wanda ba zaka iya ba, Allah ya yafe maka nasan sabida ni ka shiga wannan halin amma kai ba mazinaci bane nice shaida, kuma nayi alkawarin kula da duk abinda na haifa zan bashi tarbiyya irin yadda kake cewa zaka bawa ƴaƴanka idan muka haifa.
manal koda taje office ta wuni tana plan ɗin yadda zata zubar da cikin, bayan ta tashi daga aiki da yamma taje chemist tana shiga bata kula da mazan dake cikin chemistry ɗin ba ta ciro kuɗi masu yawa ta aje tace "abani maganin abortion"
duk suka kalleta bata kulasu ba tace "akwai ko babu?"
meshi ya kalli kuɗin data aje mishi yace "akwai"
bata yayi ya nuna mata yadda zatayi, ɗauka tayi ta fita daga wajen bata yiwa kowa kallo sau biyu ba, ɓoyewa tayi a jakanta lokacin data shiga gida ta samu ammi tayi musu girki, daɗi taji a ranta ganin ammin tana zaune akan sofa tana kallo, murmushi tayi mata tace "sannu ammi"
cikin murmushin tace "yawwa kin dawo?"
gyaɗa kai tayi ta wuce saida ta canja kaya zuwa na shan iska kafin ta fito ta kwanta kusa da ita ta ɗaura kanta a cinyarta itama tana kallo, a hankali ammi take shafa kanta, ji tayi cikinta yayi motsi tace "manal?"
cikin sanyin murya tace "umm"
tace "naji cikina yana motsi tun ɗazu inata addu'a Allah yasa namiji zan haifa"
bataso ta gano komai tace "Ameen"
murmushi ammi tayi tace "idan na haifi namji zansa mishi suna faruk"
tace "okay Allah ya kawoshi"
tace "ameen manal"


*Jiddah Ce....*
08144818849