SILAR MALAMINA: LABARIN TAUSAYI DAKE TABA ZUCIYA(2)

SILAR MALAMINA: LABARIN TAUSAYI DAKE TABA ZUCIYA(2)
*SILAR MALAMINA __________(2)*
```Gajeren Labari``
 
 
 
     *Na*                      
 
 
*Hauwa'u Salisu*                              
          (Haupha)
 
 
 
Hawaye suka zubo wa Mubarak, tabbas shi ne sanadin faɗawar mahaifiyarsa halin, shi kuma Malaminsa ne sila. Tun daga ranar kullum sai ya yi kuka, kodayaushe da tsanar kansa yake kwana yake tashi, amma ai mai uzuri saboda rabi da kwata sam ba laifinsa ba ne ba laifin Hukumar Makarantar ne da ta ba shi gurbin karatu a ɓangaren da ba shi ya je nema ba. Ayuba ya dafa mai kafaɗa ya ce, "Kar ka damu ban san kana yawan tunani komai na Allah ne kuma lokaci ne, don haka lokacinka ne ya zo kai ma da komai zai zama tarihi a rayuwarka."
 
Sai da su ka shafe wata guda cur a asibitin sannan Mama ta samu lafiya kamar ba ita ba, har wata ƙiba ta yi a lokacin ƙannensa kaf Ayuba ya maida su makarantar islamiyya da boko hatta gidan ya gyara masu shi kamar ba shi ba, sun murmure daga rayuwar talauci zuwa ta rufin asiri abinci bai fi ƙarfinsu ba, haka ma sutura rayuwa suke cikin jin daɗi ba laifi duk silar Ayuba wanda ya zama abokin Yaya Mubarak komai nasu tare suke yinsa.
 
Zuwa yanzu Mubarak da Ayuba sun shaƙu sosai har ta kai Mubarak na zuwa gidan Ayuba ya kwana shi ma Ayuba ya zo ya kwana a gidansu. Mubarak yasan Ayuba na sana'ar hatsi da ta kayan gini amma yana mamakin yadda yake samun kuɗi sosai fiye da tunanin mai tunani sannan sau tari sun sha  kwanciya tare amma ya farka cikin dare bai ganshi ba, washegari ya ganshi kwance da jakar kuɗi ya kuma kasa yi mai magana kan ina yake zuwa wani lokaci da dare kuma jakar kuɗin da yake gani ta ina yake samo ta tun da dai kuɗin kasuwanci yawanci a banki ake tara su kuma juya su ake ma ba wai ajewa ba.
 
Shi kam akwai tarin tambayoyin da yake so ya yi ma Ayuba amma ya rasa ta ina zai fara yi mai su, saboda yasan Ayuba shi ne gatansa shi ne komai na rayuwarsa bayan Ayuba da yanzu mahaifiyarsa ta rasu ko tana kwance cikin jinya, amma yanzu ga shi silarshi ya samu inda ya dogara da kansa ta hakan har ya aurar da ƙannensa mata uku yanzu haka. 
 
Ga shi ya fara samun nashi na kanshi shima tun da shi ne ke kula da shiga da fitar hatsin Ayuba, kuma ana samun alheri ba laifi a harkar sosai.
 
Yau tun da yamma Mubarak ya shirya ya nufi gun Ayuba akan sabon mashin ɗinsa da zummar zai kwana gunsa saboda gobe za a sauke masu hatsi, sai dai tun da ya je bai ga Ayuba ba har dare hakan yasa ya kasa samun natsuwa saboda duka layukan wayar Ayuba ya kira ba wanda ya same shi don haka ya haƙura kawai ya kwanta amma barci ya yi ƙaura daga idanunsa. Zuwa ƙarfe biyun dare ya ji an buɗe ƙofar ɗakin an shigo, hakan yasa yai ajiyar zuciya don yasan Ayuba ne ya dawo, sai dai tunaninsa ya tsaya cak lokacin da ya ji Ayuba ya faɗi yana wani irin nishi irin na azabar ciwo hakan yasa a tsorace ya tashi ya kunna hasken ɗakin ya kai idonsa inda Ayuba ya faɗi. Ja da baya ya dinga yi madadin ya matsa inda Ayuban yake kwance yana nishi ganin yadda jini ke bin ƙasan ɗakin wanda ba tantama daga jikin Ayuba yake fita.
 
"Ayuba lafiya!!!
 
Ita ce tambayar da ya jefa ma Ayuban ya isa inda yake kwance cikin jini ya taɓa shi jikinsa ko'ina rawa yake don firgita da lamarin da ya yi. Ayuba azabar da yake ciki tasa bai san ma da wani a kansa ba don hankalinsa ya isa gushewa daga jikinsa, ganin haka yasa Mubarak saurin dawowa nutsuwarsa ya ɗauki waya ya kira lambar Likitan da yasan shike kula da Ayuban ko da yaushe. Cikin sa'a kuwa ya amsa kiran Mubarak ya gaya mai Ayuba ba lafiya ya dawo cikin jini yanzu ya zo don Allah.
 
Ba a jima ba sai ga Likitan ya iso ya shiga duba Ayuba sai wajen sallar asuba sannan ya gama yi ma raunikan jikin Ayuba ɗinki idan ba idon Mubarak ƙarya yai mai ba yaga kamar har da harbi a jikin Ayuba don yaga Likitan ya fitar da bullet daga jikin Ayuban.
 
Magunguna Likitan ya ba Mubarak ya ce ƙarfe shida na safe yaba Ayuban ya yi mai bankwana ya fice yana fatan samun sauƙi ga Ayuban.
 
Tunani kala-kala ya cunkushe kan Mubarak kan Ayuba, waye ya ji mai wannan raunikan, ba dai hatsari ya yi ba, don da hatsari ya yi tabbas daga asibiti za a samu kiran halin da yake ciki ba za a barshi ya taho haka ba, to ko ƴan fashi ne suka tare shi kan hanya su kai mai fashi? Gaban Mubarak ya faɗi tabbas ba shakka ƴan fashi ne suka tare Ayuba Allah Ya taimaka basu kashe shi ba. Har zuwa ya yi sallar asuba ya gama Ayuba bai buɗe idonsa ba, sai da ƙarfe shidan da aka ce a ba shi magani ya motsa hakan yasa cikin sauri ya jiƙa magungunan a kofi ya kafa mai a baki, cikin ikon Allah ya shanye su tas ya rufe idonsa ya ci-gaba da barcin wahala.
 
Wasa-wasa sai da Ayuba ya kwana biyu kwance bai san inda kansa yake ba ko ya farka bai jimawa yake komawa barci amma ko da yaushe Likitansa yana zuwa yana duba shi yana sa ma shi ƙarin ruwa da na jini saboda ya zubar da jini sosai.
 
Ranar kwana na biyar ne Ayuba ya samu sauƙi sosai tun da har yana iya magana yana iya zama. Mubarak ya kawo kaf mutanen gidansu sun duba jikin Ayuba hatta ƙannensa dake gidan aure sun zo sun ga jikin Ayuba.
 
                   Bayan sati uku jikin Ayuba ya samu sauƙi hatta inda aka halbeshi ya maƙe sauran raunikan kuwa duk sun ɓanɓare wasu ma ba tabo gun, suna zaune shi da Mubarak suna shan kayan lambu Ayuba ya yi murmushi ya dubi Mubarak ya ce, "Na gode sosai Mubarak Allah Ya saka maka da mafi alheri a rayuwarka tabbas kai min abin da ba kowa ne zai iya min ba, ka kula da Ni a halin jinya na tsawon lokaci kuma baka damu da komai ba duk da nasan cewa kana da tarin abin da kake son ka tambayeni amma ka ja bakinka ka yi shiru saboda ban gaya maka ba.
 
 
Mubarak Hausawa sun ce "Ranar wanka ba a ɓoyon cibi." To a Yau a yanzu zan baka amsoshin da suka shige maka duhu a kaina, amma ina fatan kai ma kanka adalci Ni ma kai mun idan na gama baka labarin. Kamar yadda na gaya maka sunana Ayuba na tashi ba Uba sai uwa mun yi rayuwa mai cike da ɗacin gaske mai cike da baƙar wahala saboda talauci ya yi mana katutu sosai ba mai tausanmu ba mai shiga lamarinmu a haka mahaifiyata ta dage ta sakani makaranta da daɗi ba daɗi haka take kulawa da karatuna har na gama primary na je secondary school ita ma na gama ta, mahaifiyata da kuɗin wankau na kayan mutane da dakau take biyamin komai, lokacin da na gama secondary school sai da na shekara biyar  zaune ban ci-gaba da karatu ba duk da cewar takarduna sun yi kyau amma kyan banza ne tun da bamu da kuɗin da zan wuce makarantar gaba. A haka mahaifiyata ta shiga adashe (zubi) ta dage da yin aiki tuƙuru na duk wata wahala dan kawai ta haɗa kuɗin da zan wuce jami'a hakan yasa Ni ma na dage da yin dako da duk wani aiki da ka sani na wahala ina tara kuɗaɗen nima don mu samu mu samu wanda zan biya kuɗin makaranta da su. Haka kau akai da ƙyar da jiɓin goshi na wuce makarantar jami'a da kyakkyawar niyya da burin na gama na samu abin da zan tallafi rayuwar mahaifiyata da shi, kasancewar ban gane Turanci yasa na cike Hausa amma sai na iske ashe Turancin dole ne ko da ace ba shi ka ɗauka ba, Mubarak kowace semester ina wuce kowane darasi na gidan Hausa amma ban da na gidan Turanci saboda sam ban iya turanci ina iya karantawa na riƙe a kaina amma ban iya zuwa na rubuta shi a jikin takarda kamar yadda yake a cikin kaina. Wannan yasa na dinga samun carry over ko da yaushe a gidan Turanci har na kai ajin ƙarshe Turanci ne matsalata a karatuna, zuwa lokacin kuma hatta gidanmu mahaifiyata ta saida shi saboda biyan kuɗin makaranta ta bamu da komai bamu da kowa sai Allah. Fahimtata da Malaman sukai yasa suka dinga ban maki arba'in ina wucewa amma sai Malami guda ne kawai ya riƙe Ni ya kasa mun alfarmar na wuce kuma darasin tun na aji guda yake bina har zuwa ajina na ƙarshe , lokacin da za mu yi jarabar ƙarshe sai na tattara na koma cikin makaranta duk da ban da kuɗin da zan dinga ci da kaina amma haka na tare saboda wannan darasi guda ɗaya kacal da nake son naga na wuce shi saboda shi kaɗai ne damuwata ban da wata damuwa da sauran darasin da ake koya min da Hausa duk na iya shi wannan kalma duk wahalarta zan iya rubuta ta ban yi kuskure ba.
 
Daren da za mu yi jarabawar haka na kwana ina rubuta abin da na karanta saboda rubutu ne damuwata ni, so nake ya zauna min sosai akai yadda idan na je zan iya rubuta kalmomin daidai. 
 
Karfe goma na safe muka shiga ajin jarabawar baki ɗaya ƴan aji ɗaya ne saboda duk ajinmu Ni kaɗai ke dakon wannan darasi na kasa tsallake shi. 
 
Bayan mun zauna an raba mana tambayoyi mun fara amsawa kaina akan abin rubutuna saboda ban san in ɗaga kaina wata kalma guda ta fice min daga idanuna kawai na ji an anshe biron hannuna an ɗauke min takardar da nake rubutu a ciki. Na ɗago ina kallon Malamin dan nasan dai lokacin tashi bai yi ba sai kawai naga ya haɗa wata takarda mai rubutu da tawa yana dubawa, ban fahimce shi ba sai da ya ce min, "Me kake da wannan takardar ?" Na kalli takardar Ni ban san inda aka sameta ba ma dan haka nace ai ban san ko ta miye ba Malam. Nan take ya ce min ya kama Ni ina satar amsa tun da a kusa da Ni yaga takardar kuma abin da nake rubutawa akwai shi a cikinta. Ba yanda ban ba don Malamin nan ya gane ba Ni na aje ta ba amma idonsa ya rufe kai tsaye ya cike min Form na satar amsa ya kai ni ga hukumar makaranta aka kore Ni. Ita ce jarabawar ƙarshe a guna kuma ba satar amsa nake ba, karatu nayi bakin rai bakin fama amma ya ce bai yadda ba a kusa da Ni ya ganta da na kula zai ganni na yada ta.
 
Haka na koma gida cike da tashin hankali ina gayama mahaifiyata ta dafe gefen zuciyarta kafin a kaita asibiti ta rasu! Ya fashe da kuka ya ci-gaba da cewa, "A wannan ranar ji nayi da ina da dama wannan Malamin ba zai sake kwana duniya ba, da ina da iko ni ma sai na kashe mahaifiyar Malamin idan yana da ita. Mubarak ba zan iya bayyana maka halin da na shiga ciki ba a lokacin na rasa uwata na rasa karatuna wanda muka sha wahalar gaske Ni da mahaifiyata gun nemansa wanda muka rasa gidanmu da komai namu dominsa, kukana ya kasa tsayawa saboda tashin hankali na rasa me zan yi na ji daɗi baki ɗaya naji tsanar kowane Malamin jami'a a cikin zuciyata sam suka daina birgeni kallonsu nake tamkar abokan gabana. Bayan arba'in mahaifiyata maigidan da ya bamu haya ya ce min na bar mai gidansa zai zuba sabbin masu haya a ciki tun da ko ya barni ban da abin da zan biya shi haya.
Haka na koma kwana tasha saboda ba wanda ya shiga lamarina hatta dangin mahaifina da mahaifiyata saboda sun mutu ba su bar komai ba.
 
A cikin rayuwar da nake ta zaman tasha ba wahalar da ban gani ba na ci wahala na sha baƙar azabar rayuwa har Allah Ya kawo wasu samari biyu wata rana gurina suka ce na zo na shiga cikinsu na huta da baƙar rayuwar da nake ciki, ban ja na afka cikinsu na koma gidansu ashe sana'ar FASHI DA MAKAMI suke yi ban mafitar da ta wuce na amshe ta don haka na shige cikinsu muka ci-gaba da tare hanya muna shiga gidajen manyan masu kuɗi muna fashi. 
A haka ne wata rana a cikin daji muna tare hanya muka tare motar motar su Malamin nan nawa, ba ƙaramin daɗi na ji ba saboda ya zo a lokacin da nake da ƙarfin da bai da shi kasancewar nafi su ƙoƙari yasa suka ban shugabancinsu suke kira na da Oga ba kowane aiki ma nake fita ba sai babba. Ba ƙaramin razani ya shiga ba Malamin ganina shugaban ɓarayi ba, na sa a ka gurfanar min da shi gabana nace ka gane Ni? Jikinsa na rawa ya ce "Don Allah kai haƙuri kai min rai." Dariyar takaici nayi nace lokacin da nake baka haƙuri ka yi min ne kai?" Yana kuka yana komai ya dinga ban haƙuri sai naji kamar yana zuba min darma a cikin zuciyata na dube shi nace, na ji zan yafe maka amma da sharaɗi shin zaka iya maido min mahaifiyata daka sa ta haɗe zuciya ta mutu saboda baƙin cikin korar da kasa akai min a makaranta? Shin zaka iya maido min da jiya ta zuwa Yau komai ya dawo kamar ba ai ba? Shin zaka iya biyana baƙin cikin da nayi tun daga ranar zuwa Yau? 
 
Ya fashe da kuka ya ce, "Ba zan iya ba amma don Allah kai min haƙuri hakan ya zama izina a guna ba zan sake ba."
 
Cikin yarana wani ya kwashe shi da mari ya ce, "Rufe mana baki yana magana kana magana saboda halshenka na bakinka har yanzu ko? "
 
Ban ankara ba suka yi mai dukan tsiya suka kakkarya mai jiki za su kashe shi na hana su nace ku bar shi ya je ya yi dakon alhakina nasan duk abin da na aikata yana da kamasho a cikinsa saboda shi ne SILAR zama na a yanayin da nake ciki.
 
Na zuba mai kuɗi sosai a mota na ce yaransa da ke motar ya kai shi asibiti. Sai a ranar na ji wani ƙaton abu da ya tokare min a ƙahon zuciya ya fice.
 
Mubarak ina san ka sani wannan ita ce asalin sana'ata wadda SILAR MALAMINA na same ta da ace bai min sanadin barin karatuna ba da yanzu mahaifiyata na raye da yanzu na gama karatu na samu aikin yi ba mamaki nayi aure na samu yara ma. Ina san ka shigo cikinmu kai ma tun da mun riga mun zama ɗaya kamar yadda ƙaddarar rayuwarmu ta zama iri ɗaya Mubarak duk SILAR MALAMI muka faɗa halin da muke ciki. 
Wannan karon mun je wani gida ne aka samu rashin dace sojoji suka buɗe mana wuta har akai rashin sa'a suka harbeni"
 
Mubarak dake zaune yana kuka yana jin tsanar Malaman jami'a shima ya kalli Ayuba ya ce, "Tabbas kai min duk abin da ya kamata ace Uba ya yi wa ɗansa don haka ba zan ƙi amsa tayinka ba amma da sharaɗin bayan wani lokaci zan daina kai ma zaka daina za mu tuba mu yi aure muyi rayuwar farin ciki."
Ayuba ya yi murmushi ya ce, "Na yadda da wannan sharaɗin naka Mubarak."
 
Mu haɗu a kashi na uku kuma na ƙarshe in shaa Allah.
Taku: *Hauwa'u Salisu (Haupha)*