Ɗaya daga cikin tsoffin mata a Kannywood ta bayyana yanda ake biyanta a kowane fim

Ɗaya daga cikin tsoffin mata a Kannywood ta bayyana yanda ake biyanta a kowane fim
Shahararriyar 'yar wasan Hausa  wacce take fitowa a matsayin uwa ko kaka  a masana’antar Kanywood, Ladin Cima Haruna  ta koka game da yadda ake biyan ta kuɗin aikin da ta ke yi na fitowa a fina-finan Hausa.
Ladin Cima, wacce a baya a ke kiran ta da sunan Tambaya,  ta baiyana koken nata ne cikin wata hira da ta yi da Sashin Hausa na BBC a cikin Shirin su na “Daga Bakin Mai ita”,  anda a Cikin sa suke tattaunawa da Yan wasan Hausa.
Dattijuwar, wacce ta ce ta kwashe sama da shekaru 50 ta na harkar fim, ta ce ta taɓa shiga matsalar da ko yanzu ta tuna ta sai ta yi kuka,  wato matsalar rashin muhalli.
“Banda Allah ya tsare da yanzu ina bakin bata ina kwana sakamakon matsalar da na shi ga. Amma Allah ya rufa min asiri na fadawa mutane. Shi ne Allah Ya taimakeni na fita daga cikin Matsalar” inji Ladin Cima.
Bayan an tambaye ta ko ya aka yi ba ta tara abin da ta ke samu ba don mallakar muhallin, sai ta kada baki ta ce "ai ba wani abu mai yawa a ke bani in nayi fim din ba.
” Ban taba yin Fim an bani Naira dubu 50 ko 30 ko ma 20 ba, Naira dubu 5 ce ko 3, yau ma na je nayi Aiki Naira duba 2 aka bani, to me naci me na ajiye a dubu 2 ko 3?.”
Ta ce akwai ƴaƴa 7 da ita ta ke kula da su don haka tace bata da ikon adana Wani abun a an abun da ake bata.
Hakan ke nuna 'yan wasan Hausa matasa su ne ke da lagwada da babban kaso a harkar wasan kwaikwayo na Hausa.