Za mu tattauna yadda za’a shawo kan matsalar tsaro a Najeriya—Muryar Talaka
Daga Habu Rabeel Gombe.
A kokarin kungiyar muryar talaka na kasa wajen kare hakkin al’umma musamman talakawa tana kokarin gudanar da taron ta karo na goma sha daya Kano mai taken kawon karshen kalubalen tsaro a Najeriya.
Da yake zantawa da manema labarai a Gombe Sakataren kungiyar na kasa Kwamred Bishir Dauda, yace kungiyar a taron ta na goma sha daya da za ta gudanar a garin Kano a tsakanin ranakun 18 da 19 ga watan nan na Fabarairu za su tattauana matsalolin da suka ji banci tsaro ne inda masana da masu fashin bakin al’amuran yau da kullum za su gabatar da laccoci na al’amuran da suka shafi matsalar tsaro.
Kwamred Dauda, yace kasar nan na fama da matsalar tsaro da ta addabi kowa wanda ta kai a wasu jihohi mutane na kwana ido biyu a bude ba tare da suna iya runtsawa ba saboda halin da ake ciki.
Ya kara da cewa saboda yanayin tsaro har ta kai wasu yankunan kasar nan ba’a iya yin Noma da kiwo balle a samu yadda za’a gudanar da kasuwanci yadda ya kamata.
Sakataren yaci gaba da cewa matsalar ta tsaron ne yasa a wannan karon ne yasa taron zai fi mayar da hankali kan abubuwan da suka shafi tsaro saboda kar hankali ya koma ga hada-hadar siyasa kadai a dinga duba bangaren tsaro.
Sannan yace taron zai hada mutane ne masana daban daban a wannan bangare na tsaro da masu fashin bakin al’amura za su tattauna yadda za’a samu mafita.
Daga nan sai yace cikin manyan bakin da za su halarci taron su kuma gabatar da mukala sun hada da gwmnan jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar da mataimakin gwamnan Jihar Kano,Nasiru Yusuf Gawuna da mai taimakawa shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari kan kafofin sadarwa na zamani, Bashir Ahmad.
managarciya