Tasirin Finafinnan Goloɓo Bayan Shakara 7 Da Barinsa Duniya

A makaranta kowane yaro yana da wasar da yake yi,tun ina dan aji daya bani da wasar da nake son yi bayan ta kwaikwayo,sai makarantarmu ta kirkiro dirama wadda aka samu cikinta,tun a wancan lokaci na fara suna don duk abin da aka sani in fadakar da jama’a kuma a ga sha’awa zan samu nasara.; a cewar margayin.   Golobo wanda ya kwashe fiye da shekara talatin yana wasan kwaikwayo na barkawanci ya yi fina-finai da ko shi bai san iyakarsu ba kamar yadda ya taba fada, amma dai yana wasani da yafi so  irin wasan da ya yi shekara tara yana yi wasar kwashi kwaram da sauna jak da Golobo wanda wannan sunan wasar ya bi shi har yau, a gidan talabijin na tarayya(NTA) aka yi nuna  wasanni bayan sati daya sai a nuna daya,har ya koma yana yin fim dinsa ba da gwamnati ba yana sayarwa jama’a don su samu nishadi da ilmi da gargadi.

Tasirin Finafinnan Goloɓo Bayan Shakara 7 Da Barinsa Duniya
GOLOBO YA KWANTA DAMA
Sanan ne dan wasan barkwanci Shehu Jibril Talata Mafara (Golobo),ya kwanta dama an haife shi ne a garin Talatar mafara ya yi firamare anan da  sikandare a garin Gusau  daga nan ya fara aiki da ma’aikatar yada labarai ta jihar Sakkwato,sai suka tura shi Center for Nigerian culture study dake Zariya,in muka dawo baya tun aji dayan firamare yake wasan kwaikwayo har zuwa wannan satin da ya rasu, hasalima a wurin daukar fim ne ciyon ajali ya kama shi a kano bayan nan aka mai doshi gida a Mafara daga nan aka kawo shi Sakkwato in da mutuwarsa ta riske shi.
Golobo a wata tattaunawa da aka yi das hi lokacin rayuwarsa ya fadi abin da ya ja shi ga shiga wasan kwaikwayo ‘A makaranta kowane yaro yana da wasar da yake yi,tun ina dan aji daya bani da wasar da nake son yi bayan ta kwaikwayo,sai makarantarmu ta kirkiro dirama wadda aka samu cikinta,tun a wancan lokaci na fara suna don duk abin da aka sani in fadakar da jama’a kuma a ga sha’awa zan samu nasara.; a cewar margayin.
 
Golobo wanda ya kwashe fiye da shekara talatin yana wasan kwaikwayo na barkawanci ya yi fina-finai da ko shi bai san iyakarsu ba kamar yadda ya taba fada, amma dai yana wasani da yafi so  irin wasan da ya yi shekara tara yana yi wasar kwashi kwaram da sauna jak da Golobo wanda wannan sunan wasar ya bi shi har yau, a gidan talabijin na tarayya(NTA) aka yi nuna  wasanni bayan sati daya sai a nuna daya,har ya koma yana yin fim dinsa ba da gwamnati ba yana sayarwa jama’a don su samu nishadi da ilmi da gargadi.
Malam Kabiru Ibrahim Visibble daya daga cikin mutanen da suka shaku da margayi Golobo suna tare da shi tsawon lokaci mai tsawo kafin rasuwarsa  kuma shi ya dauki margayi a matsayin mahaifinsa wanda ya haifesa sukan yi shawara ga juna a a kodayaushe.
Malam Kabiru ya shedawa Aminiya mutuwar Golobo ta girgiza shi don ya dan yi jinya kafin rasuwarsa ta sati daya. ‘Ni ban san yawan fim dinsa a duniya ba don tun kafin a haifeni yake wasa yanzu haka yana da wasanni kasa wadan da ba a saki kasuwa ba, kamar fim dina nida ke Magana mai suna Zugum, da wani  wanda yake nasa ne da Hanyar Kano wanda ana yinsa ne rashin lafiyar ajali ta kama shi, da sauransu.
Golobo rayuwarsa tana da kyau abar koyi baya son rigima yana da tsari sosai,ina kira ga sauran ‘yan fim da su yi hakuri da rashinsa kuma su yi koyi da shi, In ji Kabiru.
Tasirin finafinnansa sun sanya haryanzu mutane na kallonsu domin samun nishaɗi.
Goloɓo ya shiga cikin 'yan wasa da ba a mancewa da su a fagen barkwanci domin duk mai shawar kallon wasan barkwanci ya kalli wasan Goloɓo zai gamsu kuma ya samu abin da yake bukata na barkwanci.