ƊANYAR GUBA
Page page 19 & 20
Zaune yake kan kujerar ofishinsa ya hakimce ga tarin takardu a gabansa, idanunsa na kan biron da ke kan table ɗin sai cije leɓensa na ƙasa yake. Har ya ɗauki biron ya fara cike takardar da biron ke kai kuma sai ya saki abin rubutun ya faɗi. Ya sake taune leɓe yana kallon agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunsa yana yamutsa fuska. Kallo ɗaya za ka yi masa kasan ba nutsuwa a tattare da shi. Akwatin tarhon da ke gefen shi sai jeranta ƙara take yi alamar kira na shigowa. Yana sane da sakatariyarsa ce ke ta kira ko bai ɗaga ba yasan kwanan zancen. Sai dai kuma a yanayin da yake ba ya son ganin kowa sai mutum ɗaya da ba ya tsammanin ganin shi a irin wannan lokacin, duk da kuma zaman dakon shi yake.
Aikin da yake yi ma ba daɗin shi yake ji ba kwata-kwata shi ya sa ma ya kasa ci gaba da gudanar da aikin gudun tafka kuskure ko yin aikin gayya. Wani kiran ne ya sake shigowa a karo na barkatai, don haka rai a matuƙar ɓace ya ɗaga kiran tare da fara magana cikin murya mai kaushi.
"Sau nawa zance miki idan kin kira ban ɗaga ba ba na son takura ne?"
Cikin ladabi ta fara maido masa amsa "Sorry sir, wanda ya zo ya ce kana buƙatar shi ne...."
"Dakata! Ba dogon turanci na nemi ki yi mini ba ko waye kawai ya tafi yau ba zan ga kowa ba, and kar ki sake kira na hope kin gane?"
Bai jira jin me za ta sake cewa ba ya ɗauke tarhon daga kunnensa sannan ya ajiye shi daga gefe a buɗe ba a jikin akwatinsa ba, ta yadda koda za a kwana ana sake gwada kiran ba zai shigo ba.
Sai dai duk da hakan da ya yi bai tsira ba don ko zaman shi kedawuya wayar tafi da gidankan da ke gefen shi na dama kan teburin ta hau ɓurari. Ya ja wani siririn tsaki tare da warto ta da nufin hucewa a kan koma waye ya kira.
Amma idanunsa na sauka kan sunan mai kiran annuri ya bayyana a fuskarsa. Ya ɗaga kiran cikin zumuɗi, bai ma jira an fara magana a can ɓangaren ba ya ce,
"Yanzun nan nake ta zancenka a zuciyata kamar zan kirawo ka kuma dai na kasa. Abubuwan nan sun samu kuwa?"
"I Alhaji, ina ma tafe da su to an tsayar da ni a ƙofa wai ka bada izini na koma ba za ka ga kowa ba in ji sakatariya."
Alhajin ya ɗan sosa ƙeyarsa tare da faɗar "Am! Ka yi haƙuri Bilya, tabbas umurnina ne amma ban san kai ne ka zo ba, don zaman ka kaɗai nake a office ɗin nan yau. Ba sakatariya wayar."
Bilya bai sake cewa komai ba ya cire wayar a kunne ya miƙa mata. Bayan ta karɓa ya fara magana cikin dakakkiyar murya. "Mutumina ne bar shi ya shigo." Iya abin da ya ce da ita kenan ya katse kiran.
Bilya ya karɓe wayarsa ba tare da ya tsaya jin me za ta ce ba, ya bi ƙofar da za ta sada shi da ofishin Alhaji Muktar Dala. Ita ma ba ta yi gigin dakatar da shi ba don kuwa sarai ta san waye ogan nata ba ya son a kawo masa wasa a lamuransa.
Yana taɓa handle ɗin ƙofar ya ji ta a buɗe don haka ba jira ya afka ciki da sallama a bakinsa. "Wa'alaikumus Salam, sannu da ƙarasowa Bilya, ina saƙon?"
"Me kake ci na baka na zuba Alhaji? Dalilin zuwana nan kenan kasan kuma ba zan koma da shi ba." Ya faɗa yana 'yar dariya tare da ƙoƙarin sauko da jakar da ke rataye a kafaɗarsa ya ci gaba da cewa,
"Yau an yi katari da zafafan hotuna waɗanda nake kyautata zaton ba za ka rasa daidai da ra'ayinka ba a ciki. Amma dai Hausawa na cewa gani ya kori ji." Ya sauke furucin daidai lokacin da yake yunƙurin zuge jakar, ya zaro wani farin envilope ya miƙa wa Alhaji Muktar.
Alhajin kuwa har hannunsa na rawa garin karɓar gidan hotunan, a lokacin da yake amsawa Bilya zancensa da faɗar "Ɗanɗane kuma ya zarce ganin idon ba."
Sarai Bilya ya fahimci inda zantukan shi suka dosa duba da yanayin fara'ar da ke fuskarsa yayin da yake furta kalaman, sai dai bai ce masa kanzil ba yana kallon shi ya ciro hotunan da za su kai guda goma manyan katuna (jumbo) daga gidan hoton ya fara kallon su ɗaya bayan ɗaya yana lashe leɓe kamar tsohon maye.
Idan ya zo kan wani hoton sai ya kai minti ɗaya zuwa biyu yana ƙarewa halittar da ke jikin hoton kallo yana haɗe yawu. Can ya je kan hoto na bakwai wanda daga kansa ne ya dakatar da kallon hotunan matan da yake yi. Ya ware shi dabam sannan ya sake zaro wani hoton a cikin waɗanda ya riga ya kalla ya kife a kan table daga nan ya haɗa sauran da waɗanda ya gama kalla ya mayar a envilope ya miƙa wa Bilya yana faɗar.
"Za ka iya mayar da waɗannan na gama." Murmushi kawai Bilya ya feso masa ba tare da ya yi magana ba ya fara kiciniyar mayar da su inda suka fito. Alhajin ya miƙa masa hoton da ke hannunsa yana faɗar "Yawwa mutumina, ka ga wannan to ita za ka nemo mini...."
Kafin ya gama rufe bakinsa Bilya ya yi saurin tarar numfashinsa da faɗar "Alhaji ita wannan za ta yi wuyar samu kamar da baiko a kanta, koda yake ban san da wace siga kake neman ta ba." Ya ƙarasa zancen yana sosa ƙeya haɗe da dariyar shaƙiyanci.
Alhaji Muktar ya kewaya teburin ya zauna yana ƙara cin serious. "Ka ga Bilya ban damu da ko nawa za a kashe ba ni dai kawai wannan ɗin nake so, ita kaɗai ce a nan ta dace da zubin halittar irin macen da nake ra'ayi, ban dai sani ba ko a gaba na ga wacce ta fita. Ka yi duk mai yiwuwa ka samo mini ita."
Wani shu'umin murmushi ya yi kafin ya ce "Ni ma wani yarona ne da yake taya ni aikinka ya kawo mini hoton amma ban san ta ba. Sai dai yadda yake ta mun ƙi-mun-ƙin bada hoton ya nuna mini ko da baiko a kanta ko kuma suna da wata alaƙa ta kusa. Amma dai ba damuwa sai dai shi ɗin ne...."
Sai kuma ya yi shiru yana faman sosa ƙeya da sunkuyar da kai.
"Shi ɗin ne yana da jarabar son kuɗi, ko ba haka za ka ce ba Bilya?" Alhaji Muktar ya faɗa yana dariyar yaƙe kana ya ce
"Kada ka damu, da kai da shi duk ba ku da matsala. Ni dai kawai damuwa ta na mallake ta nan da wata ɗaya jal."
Bilya ya ɗago a tsorace ya kalle shi sannan ya sake soke kai ƙasa, don a gaskiya ba haka aka so ba ƙanin miji ya fi miji kyau. So yake ya tatsi alhaji da kyau kafin deal ɗin nan ya faɗa don haka ya ɗan ɗago yana faɗar "Alhaji da wuri haka? Ai dai..."
Alhaji ya yi 'yar dariya "Kash! Shi dai biri ko ya karye sai ya hau rumbu! Kamar ban faɗa maka Alhajina ya kunno mini wuta ba..." Sai kuma ya yi saurin sakawa bakinsa linzami yana girgiza kai da alama dai ya dakatar da kansa daga yin shaɓaɓa ne. Ganin Bilya ya kafe shi da ido sai ya canza tashar maganar da faɗar
"Da alama ba ka san gagarumar matsalar da take tunkaro ni ba muddin ban yi auren nan a cikin gajartaccen lokaci ba."
Ya sake sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi. "Any way! Ka tabbatar ka nemo mini ita." Daga haka bai sake cewa komai ba ya hau juya kujerar da yake a zaune yana karkaɗa kai, da alama yana tuna wani tarnaƙin rayuwarsa ne.
"Ka fi ni gaskiya Alhaji, zan yi magana da shi yaron nawa idan mun haɗu. Yanzu dai shi wannan hoton da ka ware fa?" Ya faɗa yana ɗaukar hoton kan teburin yana dubawa.
Alhaji Muktar ya yi shu'umin murmushi yana faɗar "Ita kuma wannan ɗin ina so ka haɗa mana ganawa a wani keɓantaccen wuri. Amma fa ba yanzu ba don ka san yanzu pressure da idanun jama'a sun yi yawa a kaina, sai ina taka-tsan-tsan."
Lokar da ke gaban teburinsa ya janyo ya fito da bandir ɗin dubu ɗaya guda biyu ya wullo su zuwa gaban faffaɗan teburin yana faɗar
"Ga wannan, ka ɗauki ɗaya ka ba wa shi mai wancan hoton ɗaya. Sauran aiki kuma ya rage naka."
Hannu na ɓari Bilya ya tattare kuɗin ya zuba a jakarsa ya juya cikin zumuɗi ya bar ofishin. Tun bai ƙarasa barin masana'antar ba ya dallawa wanda yake kira da yaron nasa kira.
Bilya na ficewa shi ma ya kwashi keys ɗinsa da wayoyinsa ya zuba a aljihun babbar rigarsa tare da kulle ofishin ya nufi parking space bayan ya yi wa sakatariya umurnin tashi idan lokacin aikinta ya ƙare.
Bai san dalilin fitowar shi daga office ba, bai san kuma ina ya nufa ba shi dai ya ji zuciyarsa na azalzala masa ya fito.
Kuma dai ba gida ya nufa ba, duk da shekarunsa za su kai hamsin amma har a lokacin shi ɗin tuzurun ne ballantana ya ce shauƙin iyalinsa ne ke ɗibar shi zai koma gida.
Cikin rashin madafa ya cilla motarsa a kan babban titi ya durfafi hanyar cikin gari. Ya yi tafiyar mintuna 30 danger ta tare shi a wani babban titin cikin gari.
Cikin wani irin yanayin da ya kasa tantancewa ya ci burki yana sauke huci kaɗan-kaɗan alamar wani abu mai ciwo yana masa zillo a rai. Kamar an ce ɗago kanka ka kalli gefe ya yi tozali da wata tsaleliyar halitta da ta dame wacce ya gama ƙulafuci a kanta ta shanye a fagen kyau da tsaruwar halittar jiki.
Nan da nan ya saki baki ya shagala da kallon jan ƙunshin da ke zane a farar fatar ƙafarta. Da yake rabin ƙwabrinta duk a fili suke hakan ya taimaka sosai wurin ba shi damar ƙarewa ƙafar tata kallo tun daga duga-duganta har zuwa inda ya bayyana na ƙafar tata. Ƙunshin ya bala'in tafiya da imaninsa, kusan shi ne abin da ya ja ra'ayinsa ya ɗaga duban shi ya sauke a kan hannayenta da ta ɗaga tana gyaran kallabinta wanda a nan ne ma ya samu damar ganin kyakkyawar fuskarta a lokacin da take magana da wanda ya goyo ta a mashin kyawawan haƙoranta farare tas suka bayyana. Tsam ya ji tsikar jikinsa tana tashi a lokacin da idanunsa suka sauka a kan ƙirjinta da kusan rabinsa yake a fili.
Ana cikin haka bai ankara ba sai ganin gilmawar su ta gaban shi ya yi, ashe har danja ta bada hannun bai lura ba. Da hanzari ya taka burki ya dinga bin bayan su da kare-kare har ya ga ƙofar gidan da mutumin ya yi parking.
A kan idanunsa abar harin tasa ta sauko ta yi wa gidan key tare da shigewa. Ga mamakinsa a maimakon mamallakin mashin ɗin ya juya ya tafi bayan ya sauke ta. Sai kawai ya ga shi ma ya ɗaga mashin ɗinsa ya ɗora a kan ƙofar gidan yana yin dabarar shigewa da shi ciki. Bayan ya yi nasarar shigewa kuma ya kullo ƙofar.
Abin ya ɗaurewa Alhaji Muktar kai sosai, ya dinga jin fargaba a kan hasashen shi da ya ba shi cewar mata da miji ne.
Can kuma ya girgiza kai yana ƙoƙarin ƙaryata hasashen nasa da faɗar "Ina! Ai ba zai yiwu ba abotar kura da akuya. Matar aure da wannan shigar kuma mijinta ya yi yawo da ita a gari haka? Sai dai ko yayanta, ko wani makusanci."
Take a wurin shaiɗaniyar zuciyarsa ta raya masa cewa koda a ce matar aure ce ma ba zai haƙura ba in dai kuɗi yana da rana don wannan ba matar ƙananun mutane ba ce irin tasu ce.
Nan da nan ya gusar da tunanin tare da fara yin sabo na yadda za a yi ya samu ganawa da ita. Shiru ya yi ya ci gaba da zama a wurin har na tsawon mintuna biyar bai ga wulgawar wani yaro da zai iya aika ba kasancewar har a lokacin yara ba su taso school ba. Yana nan yana ƙulawa da kwancewa ya ga fitowar matashin daga gidan ya nufo inda motarsa ke tsaye da alama zai wuce ne.
Ba ɓata lokaci ya buɗe murfin motar ya fito ya sha gaban shi yana ba shi hannu da faɗar "Amincin Allah ya tabbata a gare ka."
Shi ma matashin cike da fara'a ya amsa bayan sun yi musabaha alhajin ya ce "Don Allah idan ba damuwa ina son ganawa da 'yar'uwarka." Da mamaki ya ce wacce kenan?"
"Wannan da kuka shiga ciki tare ba jimawa." Ya amsa masa.
Salis ya kalle shi a ɗage a ransa ya ce 'Oh! Haka ya fahimta cewa sisterna ce? To mu je a haka.' A zahiri kuwa cewa ya yi "Allah sarki bawan Allah ina ce ko lafiya?"
Da sakakkiyar fuska alhajin ya ce "Lafiya lau wallahi, kawai dai na gan ta ne kuma ta yi mini shi ne na biyo ku a baya."
Kamar ya dalla masa mari haka ya ji a lokacin da mutumin ya yi zancen ta masa. Shi kan shi bai san ya aka fara ba ya ji wani ƙololon kishi ya masa ƙabe-ƙabe a maƙoshi. Amma sai ya haɗiye shi da ƙarfin ruwan zallar kwaɗayin abin duniya. Ya ƙara kallon motar kalar sararin samaniya da mutumin ya jingina da ita.
Ya gane motar sarai Audi S5 ce koda shi ba ya sahun masu yatsu da yawa amma ya san kalar motocin da suke hawa, gidaje dama suturunsu. Ya hardace sunayen kowacce mota da kuɗinta. Don haka cikin dabara ya ƙara satar kallon gaban motar da tayoyinta ba shakka ɗaya daga cikin motocin da ake yayi a ƙasar a wannan zamanin ce kuma kuɗinta ya kusan kai Naira miliyan biyar duk da bai kiyaye ba. A zuciyarsa ya ce 'Mai yiwuwa ma ita ce ƙarama a cikin motocinsa.'
"Malam ba ka ce komai ba." Alhajin ya datse masa igiyar tunani.
Da kamar zai ce matarsa ce a lokacin da kishin ya tsikaro shi sai kuma ya hango mamora a jikin bawan Allahn don haka ya ce "Ka yi haƙuri gaskiya ba za ka samu ganin ta a nan ba. Zan ma roƙe ka wata alfarma don Allah kada ka ƙara zuwa neman ta a nan?"
Da sauri alhajin ya ce "Ban gane ba meye dalili? Tana da baiko ne?"
Kamar zai ce eh kuma dai ya tsinci bakinsa da faɗar "A'a kawai dai ka ba ni contact ɗinka ni zan shirya muku haɗuwa daga baya."
Alhaji Muktar ya yi mamaki ƙwarai kuma ya shiga ruɗani to amma ba ya son ya ɓarar da damarsa don haka ya yi wa Salis godiya yana faɗar "Ya ma sunan naka ɗan'uwa?" "Salim." Salis ya sake tsintar kansa da yin ƙarya a karo na biyu.
Alhajin ya buɗe mota ya miƙo masa compliment card ɗinsa da bandir na 'yan dubu-dubu guda biyu yana faɗar "Ga Katina don Allah ka kira ni. Idan kuma na ji shiru zuwa gobe zan dawo don dai na ga ruwan da ke yi mini wanka." Daga haka ya ja lafiyayyar motarsa ya tafi da mamakin wane irin mai kwaɗayin abin duniya ya haɗu da shi? Daga tayi ya karɓe kuɗaɗen ba wani alamar yabawa kuma.
A nan dai ya bar Salis yana hango kansa a cikin wacce ta fita a lokacin da burinsa da yake ta ginawa ya cika. Ya jima yana jujjuya kuɗin a hannunsa kafin ya waw-waiga ya ga ba kowa ya yi musu kyakkyawan ɓoyo a aljihunsa ya wuce zuwa sabgar da ta fito da shi daga gidan yana ta ƙissima abubuwa a ransa. A lokacin ne ya ji wani sabon tunani ya tsirga a zuciyarsa. 'Babu shakka nan kawai ya dace na tunkara a yanzu.'
********
Bayan kamar awa biyu da yin wannan Ajasu ya nufi unguwar Rukuba a kan mashin ɗinsa cike da annashuwa. Tun farkon shigar shi unguwar yake gaisawa da wasu daga cikin mazauna unguwar da suka kasance kiristoci.
Duk da kowa yana sane da cewa abin mamaki ne a birnin Jos a ga musulmi a arear kiristoci saboda irin zaman doya da manjan da mabiya addinan suke a tsakanin su. Amma shi Ajasu ko kaɗan ba ya fargaba ko shakkar ratsa unguwar har ya zauna a ciki na tsawon lokacin da yake so ba tare da fargabar komai ba, duk da akwai da yawan mutane masu hantarar shi akwai kuma wanda yake shakka.
Yanzun ma abin da ya faru kenan suna haɗa ido da wani matashi da ke zaune a kusa da gidan da ya zo, matashin ya zabga masa harara yana bin shi da kallon za ka sani. Ya jima da sanin cewa a kaf unguwar nan ba wanda ya tsane shi sama da Peter, don kuwa da za a ba shi makami a ce ya ciro kansa ba abin da zai faru da shi da da gudu zai aikata hakan cikin shauƙi.
Tuna hakan da ya yi ne ya saka ya mayarwa Peter da martanin murmushi a lokacin da yake kashe mashin ɗinsa a ƙofar gidansu Rose.
Ba komai ya saka shi yi wa Peter murmushi ba sai don imanin da ya yi cewa yi wa maƙiyi murmushi kan jefa shi a fargaba, kuma hakan ya kan rage masa ƙarfin damar yaƙarka saboda rashin sanin lagonka.
A daidai lokacin ne wani ƙaramin yaron da ba zai haura shekara biyar ba ya fito daga cikin gidan ya rungume Ajasu ta baya. Dalilin da ya tilasta masa ɗauke idanunsa a kan Peter kenan ya mayar kan ƙaramin yaron da ke rungume da shi bayan ya janyo shi ya dawo gaban shi suna fuskantar juna. "Welcome Daddy." Cewar yaron.
Daidai lokacin Rose ta fito sanye da wani gajeren buje iya gwuiwa baƙi da ɗamammiyar farar rigar da ta bayyana rabin halittar ƙirjinta, kanta ba kallabi, gashin nan ya sha kitson attach ja. Da alama ta biyo sawun John ne.
Tana zuwa wurin ba ta ko kalli Ajasu ba ta ja hannun yaron suka koma cikin gida tana mitar daga dawowar shi makaranta ya fito waje da uniform. Murmushi ne ya ƙwace masa da ya ga yanayin fusatar da ta yi kawai shi ma sai ya bi ta zuwa cikin gidan.
Irin manyan gidajen nan ne da a mafi akasarin jihohi ake bayar da su haya, a irin su ne za ka ga ɗakuna goma a jere daga wata kusurwar, a kusurwa mai fuskantar ɗayar ma za a iya samun ɗaki goma ko ƙasa da hakan.
Ƙofar iyayen Rose ce a farkon shiga gidan a ɓangaren hagu, yayin da ƙofar Rose take a ƙarshen layi a ɓangaren dama. Saboda haka duk lokacin da ya zo wucewa yana da wahala bai yi kicibis da ɗaya daga cikin iyayenta ba. Yanzun ma hakan ce ta faru, sako kan shi gidan kedawuya suka yi arangama da baban Rose wanda ake kira Mr Bitrus.
Suna haɗa ido baba Bitrus ya aiko masa da saƙon harara mai cike da ishara iri-iri. A cikin zuciyar Bitrus yana jin da zai samu dama shi ne mutum na farko da zai fara ɗauke kan Ajasu saboda yadda wutar ƙiyayyar musulunci ke zaɓalɓala a zuciyarsa da kuma laifin da Ajasun ya musu. Sai dai kash! Duk da kasancewar shi shugaba a wannan unguwa ya kasa aiwatar da hakan. Uwa uba ma a cikin rigar alfarmarsa Ajasun yake iya ratso unguwar ba tare da an ko mintsine shi ba har ya shigo masa gida. Kuma shi ne yake ba shi kariya da ƙarfin ikon da yake da shi a unguwar.
Shi ma martanin murmushi Ajasun ya mayar masa sannan ya nufi ɗakin Rose kai tsaye. A buɗe ya tarar da ƙofar kuma yana da tabbacin saboda shi ta bar ta a buɗen don haka ya faɗa ɗakin a lokacin da take kiciniyar canzawa yaron kaya daga uniform zuwa na gida.
Tana jin motsin shigowarsa ta ƙara haɗe girar sama da ta ƙasa. Murmushi ya kubce masa ya nemi wuri kan kujerar da ke fuskantar ta ya zauna. Da ya ga ta yi kamar ba ta san da wata halitta a ɗakin ba sai ya kalli yaron yana faɗar "Son ya makaranta?" Ya tambaye shi da irin gurɓataccen turanci da suke rayuwa da shi.
Yaron ma ya mayar masa amsa da irin shi cikin sake fuska "Lafiya, Daddy me ya sa ba ka zo ba two days? Ina ta nemanka, abokanaina sun ce na zo da kai."
"Kai! mai shegen surutu shige ka je ɗakin Mommy." Rose ta dakatar da shi a fusace tare da janye hannunta daga kan ƙafarshi da ta durƙusa tana saka masa takalmi.
Jikin yaron ya hau ɓari ba shiri ya bar ɗakin da gudu yana ƙoƙarin yin kuka.
Idanun Ajasu ƙyam a kan ƙirjinta tun lokacin da ya shigo ɗakin ya kasa ɗauke idanunsa a wurin.
Tun yana yaro aka jarabce shi da son mata masu cikar halitta kuma guntaye, amma kuma ya rasa dalilin da ya sa ƙaddara ta ba shi mata akasin wacce zuciyarsa ta tsara masa mallaka.
Lura da irin kallon ƙurillar da yake yi mata ya saka ta yi saurin miƙewa ta juya masa baya. Sai dai ba ta sani ba ta yi rufin kan Uwardaɗi ne, don kuwa juyawar da ta yi ma wani abin kallon ta juya masa, abin da ya fi tafiya da imaninsa fiye da komai. Lumshe ido ya yi ya sake buɗewa a ransa yana ƙara yi wa Allah godiya da a cikin ƙaddarar ya ba shi mata da ta mallaki kwatankwacin abin da yake so, duk da ko alama ba ta kamo ƙafar Rose ba a komai kuma ita ɗin doguwa ce akasin guntuwar halittar da ya ƙwallafawa rai tun daga ƙuruciya duk da an samu akasi ta fito daga addinin da ya saɓa da nasa.
Ganin tana yunƙurin tafiya ya sanya shi ya yi saurin miƙewa ya riƙo hannunta yana faɗar "Sorry my dear."
Ƙwace hannun nata ta yi daga riƙon da ya yi mata ta juyo a kufule tana faɗar
"Me ka zo yi a nan? Kwananka nawa rabon da ka zo? To tun wuri ka juya ka tafi bana buƙatar ka a nan. Ka koma gida tun da sun fi ni muhimmanci."
Sake matsawa ya yi kusa da ita yana ƙoƙarin sake riƙo hannunta ta goce, cikin kwantar da murya yake faɗar "Na sani kina sane da cewa ina sonki, a kan ke da John ba abin da ba zan iya yi ba. Kin san cewa wannan arear tana daga cikin areas masu hatsarin kusanta ga masu riƙo da irin addinina. Ni ma ba don wanzuwar ki a nan ba ba abin da zai saka na ci gaba da saka rayuwata a hatsari saboda kare ki da yaronki. Ki fahimce ni mana Rose."
Jin waɗannan lafuzan da suka fito daga bakinsa ya saka ta saki fuskarta tana faɗar
"Na sani ka saka rayuwarka a hatsari da yawa saboda ka ceci rayuwata, ina alfahari da hakan kuma ina godiya. Sai dai duk da haka bana son kana yin nisa da ni, saboda hakan kan iya jefa mu a matsala." Tana zuwa nan ta ɗan ɗigawa zancen nata aya, sannan ta ja dogon numfashi ta sauke ta ce "Well, me ka zo mana da shi? Na san kamar eagle kake ba ka saukowar banza."
Ya yi ɗan murmushin jin daɗi ganin ta ware har hakan ya saka ya kamo hannunta ya sumbata kafin ya ce
"Wasu kuɗi na samu masu ɗan dama, kuma kin san duk duniya ba ni da wanda na yarda da shi a kan kuɗi sama da ke...."
Ya saka hannunsa a aljihu yana ƙoƙarin fito da kuɗin da ke ciki, yayin da ita kuma take ƙara washe baki kamar gonar auduga.
Daidai lokacin suka ji an banko ƙofar dakin da ƙarfi ana faɗar.....
Share please
ƊANYAR GUBA BOOK 1