ƊANYAR GUBA: Fita Ta 15 da 16

In ji hausawa suka ce wai haƙuri zuga ne, ta tabbata don kamar kada ta yi magana ya ƙara hayyaƙo mata. Ai kam ranar ta sha ruwan masifa ya zazzage mata buhu-bubun rashin albarka ko banza ga yunwar azumi ga zafin dukan da gardawa suka masa bai da halin ramawa. Ƙari da waɗannan abubuwan ne suka saka shi ya ci gaba da kumfar baki da faɗar "Ki ji ni da kyau ina son haihuwa, lokaci ya yi da za ki sarara da wannan iskancin. Kin dai gama karatu yanzu ba wani uzuri da zai hana ki son haihuwa. Idan kuma kika yi wa kanki illa ruwanki, ni namiji ne ina da wata mafitar."

ƊANYAR GUBA: Fita Ta 15 da 16
ƊANYAR GUBA: Fita Ta 15 da 16
 Page 15 & 16
 
 
 
 
 
 
A cikin ɗan lokaci rayuwa ta juya wa ma'auratan baya har abin da za su ci yana neman gagarar su, wannan kuma ya biyo bayan dokar ta ɓaci na hana fita (lockdown) da gwamnatin ƙasar ta saka a gabaɗayan jihohinta saboda zargin cutar mashaƙo na ci gaba da karaɗe jihohin ƙasar dalilin tafiye-tafiye da yawan gamayyar jama'a a wurare irin su kasuwa, gidan biki, da duk wani wurin taron jama'a da ake ganin shi ke ƙara yawaitar yaɗuwar cutar. Tuni aka rufe hanyoyin tashin jiragen sama da na ruwa da ma na motocin sufuri.
Lokaci ne da 'yan ƙasa suka shiga matsatsi da takura aka ajiye su a wuri ɗaya kamar kifin gwangwani. Tuni kasuwanci ya tsaya cak don kuwa kowacce kasuwa da shaguna a kulle suke sai lokaci bayan lokaci ake bada damar buɗe wa don al'umma su nemi abincin da za su ajiye a gida don su rayu. Ba zancen fita aikin gwamnati ko makarantu, iya 'yan jarida da ma'aikatan lafiya da sauran ma'aikatan da fitar su ke da matuƙar tasiri ne kaɗai aka ba wa damar fita su ma cikin takatsan-tsan da bin dokokin da hukumar lafiya ta duniya ta gindaya na bada tazara tsakanin mutum da mutum da yin amfani da facemask(amwali) bayan wanke hannu akai-akai don kare kai daga cutar.
Lokacin da matsi ya kai matsi rayuwar babu ta dirarwa cima-zaunen ahalin, Nu'aymah ta saka Salis ya nemo mai sayen mota ya zo har gida ya ga motarta tare da yi mata kuɗi. 
Ba ta yi wani tsada sosai ba saboda shan jikin da ta yi da kuma kasancewar ta da ma can ba sabuwa ta saye ta ba. Bayan kwana biyu ya cake musu kuɗinsu ya karɓi motar. A ranar wata Alhamis da aka buɗe kasuwa Nu'aymah da maigidan nata suka nufi can don haɗo abubuwan amfanin da suke buƙata don ci gaba da tattalin rayuwarsu.
Bayan wani lokaci suka koma gida suka jibge kayan, su suka ci gaba da ɗan tsakura tun da kwabon kowa ya daina shigo su ballantana su fantama hakan ya ja suka kasance kamar ɗan kasuwar da ibtila'in gobara ya lamushewa duka kadarorinsa.
Da ma sai ta fita ta yi mu'amala da mutanen ta da ta kira na arziƙi ko kuma shi ya fita ya yo buga-bugarsa ne suke samun kuɗi, to kuma a yanzu babu wannan damar mutane gudun junan su ma suke yi.
iPhone Xr ɗin da ke hannunta a wannan lokacin ce kawai ta tsira ita ma ta sha yunƙurin sayar da ita sai kuma ta tuna an ce bayan wuya sai daɗi. Idan lokacin wuyar ya ƙare kuma ya za ta kare ɗan guntun ajinta da mutanenta ke hangen ta da shi? Hakan ne dalilin da ya hana ta saidawa.
Suna cikin yanayin ne suka samu mummunar labari na rasuwar yayan mahaifiyarta a can garin Bauchi.
Ta shiga alhini sosai, abin takaici shi ma ana danganta mutuwarsa da cutar mashaƙo. Amma ita dai ba ta yarda da hakan ba musamman da ta tuna cewa a lokacin ba a mutuwar Allah, duk wanda ya mutu sai a yaɗa jita-jitar cutar ce ta kashe shi. Ta so ta je Bauchi sosai ko don jimawar da ta yi ba ta je ziyara ba, amma tuna yanayin da ake ciki ya saka ta dangana sai a waya ta kira umman tata da danginsu ta yi musu ta'aziyya. 
Wannan al'amarin bai jima da faruwa ba Salis ya bijiro da zancen zuwa Lagos tare da abokan harƙallarsa, ba yadda ba ta yi da shi ba a kan ya shawarci abokanan sabon kasuwancin nasa da su haƙura da wannan tafiyar har bayan wucewar wannan ibtila'in. 
Amma ya kafe kai da fata shi sai ya je tare da tunatar da ita shi fa da ma bai yi wani imani da wannan cutar ba. Haka ma abokanan tafiyar tasa, su suna ɗauka duk waɗannan tsauraran dokokin ana saka su ne don ƙuntatawa talakawa da takure rayuwar 'yancin da ake iƙirarin suna da ita. Sai da suka yi sa-toka-sa-katsi kafin bisa ga tilas ta haƙura ta ƙyale shi. Ranar wata Asabar shi da abokanan nasa suka bi wasu motocin da ke sufuri ta hanyar satar hanya suna ratsawa ta jejuka suka nufi Lagos.
A daren ranar da zai tafi ya shawarce ta da ta je gida ta samo ɗaya ko biyu a cikin ƙannenta su taya ta kwana, kasancewar ya san halinta da baƙin tsoro kamar farar kura. Ba ta musa masa ba washe gari ta buga waya gida ta sanar da maman Ashna buƙatarta. Sosai maman ta yi ta ƙorafi a kan Salis irin abin da ake kira faɗan gwaggwo a Ƙofa, kafin daga bisani ta ce "Shi kenan Ashna da Nusrat za su zo, da ma yanzu ba makaranta tunda duk an rufe."
Maman na katse wayar kuwa ta je ƙofar maman Nusrat ta sanar da ita. Ba ta wani samu matsala da ita ba kasancewar gabaɗayan matan da suke zaune a gidan gandun suna da haɗin kai sosai, kuma sashen su na girmama wani sashe, sai dai saɓanin halayya da take tsakanin su.
 
Can wuraren ƙarfe uku na rana Nu'aymah ta karɓi baƙuncin ƙannen nata, zuwan su gidan ya zo mata da abu biyu murna da akasin ta, ta wani ɓangaren ta yi murna saboda tana da 'yan hira da taya bacci ta ɗaya ɓangaren kuma tana ganin cewa zaman su a gidan zai takura rayuwar da take yi duk da lokacin ba ta da customers sai wasu daga cikin nataccin da suke manne da ita a waya ko a chat. 
 
 
 
A ɗan zaman da suka yi a gidan sai da ta kai Nu'aymah ko banɗaki za ta shiga sai ta je da wayarta. Bisa tilas ta ƙirƙiri salo irin na ƙwararrin 'yan wasa ta fara amfani da shi don kawar da hankalinsu a kanta. Sarai ta san halin Nusrat da bin diddigi, ga ma tun ranar da suka zo ta ga hoton Hafizu a wayarta har ta yi mata ƙarya da cewa ɗan'uwan Salis ne take takura mata da zancen shi har zuwa yanzun da aka shekara biyu ba ta manta ba.
 
 
 
 A wani daren ranar talata bacci ya kwashe Nu'aymah a kan doguwar kujera a lokacin da suke tsakiyar hira da kallo ita da Nusrat. Da ma tuni Ashna ta shige ɗakin Nu'aymar ta kwanta ta bar iya su biyu a falon.
 
Damar da Nusrat ta samu kenan ta yi saɗaf-saɗaf ta zagaye Nu'aymah ta ɗauko wayar da ke ajiye kusa da ita, sannan ta durƙusa a gaban ta a hankali ta kama yatsanta na dama manuni ta dangwala a jikin thumbprint na wayar. Ba ɓata lokaci wayar ta buɗe, cike da murna ta sake hannun Nu'aymar a hankali ta miƙe ta tura ƙofar kitchen cikin sanɗa ta shige ta mayar da ƙofa ta rufe. 
A sannan ne ta shiga ɗakin hotuna na wayar ta fara yin lalube wai ko ta samo wani hotonsa ko wata shaida da za ta iya gane sunan shi don ta nemo lambar shi ta kwafa.
Sai dai rashin sa'ar ta ɗakin hotunan a rufe yake da lambobin sirri (pin number) a nan ta shiga ƙoƙarin shigar da lambobi huɗun da suka rufe gallaryn amma ta kasa, duk wanda ta saka sai a rubuto mata ba daidai ba ne.
 Bayan ta yi gwaji sau biyar ne wayar ta ƙi karɓar ƙarin kowacce lamba sai bayan cikar daƙiƙu sittin a cikin waɗannan sakannin ne ta tsaya ta yi wani nazari.
Wayar da ke aljihunta ta zaro ta gwada shigar da ƙarshen number Nu'ayman nan ma duk sammaƙal, don haka ta lalubo lambar Salis da ke wayarta ta saka numbobin ƙarshe nan ma duk labarin ɗaya ne. Ba mamaki hakan na faruwa ne da yake Nu'aymar ta san abin da take shukawa shi ya sa ta yi da gaske wurin ɗinke duk wata ɓaraka da za ta fallasa sirrinta. 
 
 
 
Cike da jin haushi Nusrat ta dungure wayar a kan carbinet na kitchen ɗin sannan ta ɗauki kofi ta buɗe ƙaramin bokiti mai murfi da ke ajiye a ciki ta sha ruwa tare da sauke ajiyar numfashi tana mai ƙara zurfafa nazari a kan mabuɗin wayar.
 Can wani abu ya faɗo mata a rai, kamar a majigi hoton wataranar zagayowar ranar haihuwar Salis ya hasko a idanunta. Take ta tsinkayo ta kwance a kan katifa tana kallon status a wayarta kwatsam ta ci karo da status ɗin Nu'aymah da take cewa Happy birthday sweet bro 1985 shekarar da ta shiga jadawalin tarihi. A lokacin ta yi mata reply da cewa 'Birthdayn wane yayan ne a cikin yayunmu?' 
Nu'aymar ta dawo mata da emoji na murmushi sannan a gaban murmushin ta rubuto mata 'Ke Birthdayn Habibie ne fa, saboda 'yan gulma na dunƙule abin." Iya nan hoton ranar ya ɓace a idanunta.
 
 Nan da nan ta sake ɗauko wayar tana fatan kintacen ta ya yi daidai, jiki a sanyaye ta shigar da 1985 ɗin nan take kuwa ɗakin hotunan ya buɗe. 
Cike da zallar murna ta hau lalube ko za ta samo hotunansa da wani abu game da bayanan shi, hotuna ta ci karo da su birjik waɗanda suka birkita tunaninta. 'Wai ina yaya Nu'aymah take samo hotunan waɗannan zafafan gayu da alhazawan nan? Me take da hotunan gardawa a waya alhali tana matar aure...' kafin ta gama jan zaren tunaninta idanunta ya faɗa kan wani hoto da take kyautata zaton mace da namiji ne, macen ma kuma Nu'aymah namijin ne ba ta shaida ba take ƙoƙarin shaidawar. Kafin ta kai ga shiga ciki ta ji motsi alamar ana turo ƙofar, ba shiri ta dannawa wayar lock ta ɓoye ta a bayanta.
Makunnin gulof ɗin aka latsa nan take haske ya garwaye ɗakin girkin dake akwai wutar NEPA har lokacin.
"Me kike yi a nan?" Nu'aymah ta faɗa da muryar bacci mai haɗe da razana, "Me ya faru kika taso a ɗimauce haka?" Nusrat ta mayar mata da tambaya cikin dakiya.
 
"Ke wayata ce ban gani ba, na sha ɓarawon ne ya ɓuya nan na rutsa shi. Ba ki ji motsin shi ba? Mu je ki taya ni neman shi na shiga uku." Nu'aymar ta sake faɗa tana yunƙurin juyawa a firgice kamar za ta tsunduma ihu. Ganin yadda hankalinta ya tashi ya saka Nusrat ta fito da wayar daga in da ta ɓoye ta tana faɗar "Ayyah! Sorry sis ga ta fa a hannuna na ɗauko ne na haska na sha ruwa."
Da kallon tuhuma Nu'aymah ta bi ta kafin ta ce "Me ya sa ba ki kunna gulof ba duk da kin san da nepa sai kika ɗauki wayata?" Sosa dokin wuyanta ta yi tana maida mata martani da cewa "Yi haƙuri sis bana son na kunna gulof hasken ya dame ki ne."
Tun daga nan Nu'aymah ba ta sake cewa komai ba face kallon tsaf da ta yi mata wanda yake tabbatarwa Nusrat cewa ba fa ta yarda da ita ba sannan ta juya ta koma inda ta fito.
Nusrat ta sauke doguwar ajiyar zuciya ita ma ta biyo bayan yayar tata tana godewa Allah a ƙasan ranta. Nu'aymah ba ta yarda ta kwanta ba sai da ta shiga settings  ta sauya kalmomin sirri zuwa masu ƙarfi tukunna.
*******
Salis kuwa ba su suka juyo gida ba sai da suka shafe sati biyu cur a Lagos. Washe garin ranar da ya sauka yana zaune ya miƙe ƙafafuwansa a kan doguwar kujerar falon yana daddanna ƙaramar wayarsa yayin da yake jiran saukar abincin karyawar shi. Nu'aymah kuwa tana zaune a gefen shi tana ƙoƙarin kwance ɗaurin ledar viva da ya zo da ita wacce ta so kuncewa tun jiya amma da yake saukar dare ya yi sai ta haƙurƙurtar da zuciyarta ta bari har garin ya waye.
"Sai na ji kamar ana ƙwanƙwasa gyat ko?" Ta faɗa tana ci gaba da abin da take.
Ɗan saurarawa ya yi kaɗan kafin ya ce "Ni ma kamar haka na ji. Bari na ga ko waye da sassafen nan haka."
Ya miƙe zai fita dai-dai lokacin suka ƙara jin sautin ƙwanƙwasar.
"Kai kuwa ba za a kira yanzu da sassafe ba, don goma ta gota kai ne dai ba ka tashi ba sai yanzu." Ta faɗa a lokacin da ya buɗe ƙofar falon ya fita ba tare da ya tamka ta ba.
 Yana buɗe ƙofar ya fito kamar daga sama ya ga wasu jami'ai sanye cikin rigunan leda koraye sun rufe hancinsu da wani kororon mazuƙin oxygen za su kai su biyar ko fiye da haka sun yi wa ƙyauren gidan ƙawanya.
Cike da tantama ya kalli motar da take ajiye a gaban gidan nasa a zuciyarsa ya karanto abin da aka rubuta a jikin motar, a nan ya tabbatar da cewa jami'an kiwon lafiya ne masu kula da ɓangaren cutar C19. Tsaye kawai ya yi kamar an dasa shi a wurin yana son gano wa ya ba su masaniya a kan tafiyar da ya yi don ba ya raba ɗayan biyu dalilin zuwan su kenan.
Amma don ya wanke tantamar sa ya kalli ɗaya daga cikin su "Lafiya me ya faru?" Ya tambaye su a dabarbarce.
"Ma'aikatan lafiya ne ƙarƙashin hukumar lafiya ta duniya (WHO) mun zo ne don mu yi maka gwajin cutar Covid 19 idan ka tsallake shi kenan sai mu kama gabanmu."
 
Hangame baki ya yi yana ta kallon ikon Allah ya ma kasa motsawa daga gun. Mutum biyu daga cikin su suka kama shi suka zaunar da shi a cikin rumfar makwaftansu suka fara yi masa wasu 'yan gwaje-gwaje.
Mamaki da tsoron Allah ne ya kama shi har ya hana masa cewa uffan sai raka su yake da ido yana jinjina ƙarfin halinsu.
 Sun shafe fiye da daƙiƙa goma sha biyar suna abu ɗaya kafin daga bisani suka tattara shi suka watsa shi a bayan motarsu. Zuwa lokacin wasu tsirarun mutane daga gidajen da ke makwaftaka da nasa sun fara leƙowa ta jikin ƙyaurayen gidan su dalilin yawaitar motsin da suke jiyowa.
 Wasu kuwa da suka kasa jure tsegumi daga nesa sai suka fito suka tsaitsaya nesa-nesa da juna suna kallo.
Nu'aymah da tun lokacin da ta ji shirun ya yi yawa Salis bai dawo daga duba mai sallama ba sai ta ji hankalinta ya kasa kwanciya musamman da ta tuna da jami'ai masu farautarsa, don haka a hanzarce ta zura hijab ɗinta ta fito ƙofar gidan. Ganin abin da ke faruwa sai ta ƙame ƙiƙam a wurin tana kallon su. Ba ta yi magana ba sai a lokacin da ta ga an watsa shi a bayan mota sannan ta ja sanyayyin ƙafafunta ta matsa kusa da jami'an tana faɗar "Me kuma mijina ya yi muku? Ina za ku kai mun shi?"
"Za mu wuce da shi inda ya fi dacewa da zaman shi wato (isolation center)"
 "Me... me kenan kuke nufi, yana ɗauke da wannan cu...cutar?" Ta tambaya da katsattsen sauti idanunta suna tara ƙwalla.
Gyaɗa kai ɗaya daga cikin su ya yi yana faɗar "Haka muke nufi, ke ma don kina mace ne za mu bar ki. Kuma a rahoton da muka samu jiyan nan ya dawo daga tafiyar don haka zaman ku bai yi nisa ba, ba lallai kin kamu ba amma a shawarce ke ma ki killace kanki na tsawon kwana uku idan kin ji wata alama sai ki tuntuɓe mu." Suka wurgo mata wani ɗan kati mai ɗauke da sunan ƙungiyar da wasu lambobi sannan suka ja motar suka bar wurin.
A wurin ta durƙushe tana gursheƙen kuka na jin raɗaɗin tafiyar mata da miji da saya mata tikitin ƙyamatar mutane da suka yi.
Ba ta sake tabbatarwa lallai an saya mata tikitin ƙyamatar da ta raya a ranta ba sai da ta ɗaga kai ta kalli tarin jama'ar da ke warwatse a wurin suna kallon ta amma an rasa mai matsowa kusa da zimmar ya rarrashe ta. 
Ta sake ɗaga kanta ta sauke dubanta a ƙofar ƙyauren gidan makwaftansu ma fi kusa, ta ga Sadiya da ta kasance ƙawarta kuma matar wannan gidan tsaye a wurin tana bin ta da ido. Suna haɗa ido ma sai Sadiyar ta juya ta shige gidan nata a hanzarce tare da maida ƙofa ta rufe.
Su ma sauran 'yan kallon kamar ta ba su fatawa duk sai suka tarwatse suna ƙoƙarin komawa cikin gidajensu. 
Dalili kenan da ya sanya ta ƙara sautin kukanta, sai da ta yi mai isar ta ba mai lallashi sa'annan ta miƙe ta share hawayenta ta shige gidanta tare da mayar da ƙofar ta rufe ta saka sakata. 
A nan saman dandamalin barandarsu ta yasu tana mai ƙara kecewa da kuka musamman da ta kalli bangon gidan na gabas da yamma ta tuna cewa yau ita kaɗai za ta kwana ba mijinta, sai ta ga gidan ya yi mata girma sosai. 
Wannan ma kafin yamma ta yi kenan to ina ga duhun dare ya shigo tsoro ya fara riskar ta? Ta ya ya za ta kwana a cikin gidan ita kaɗai? Rashin samun amsar ya saka ta miƙe tare da goge hawayenta ta nufi cikin ɗakinsa inda ta baro wayarta ta ɗauka sannan ta zauna a gefen gadon cikin wani irin yanayi mai bayyanar da zahirin damuwa ta lalubo lambar mama ta danna mata kira.
Ringi ɗaya kafin ƙarewar na biyu ta ɗaga kiran da sallamar ta. "Wa'alaikumus saalam, mama barka da safiya." Ta faɗa cikin raunanniyar murya.
"Barka dai 'yar nan, lafiya dai kika kira ni da safiyar nan?" Ta amsa da yanayin mamaki a muryarta, saboda ta sani Nu'aymah ba ta kiran ta idan ba wani dalili, idan har ta ji kiran ta to wata matsala ce ko kuma neman alfarma. Ita tana da wannan ɗabi'ar ta ko oho, kawai idan kai ke buƙatarta sai dai ka neme ta.
"Am! mama da ma ina neman ƙarin wata alfarmar ne..." Tun ba ta ajiye zancenta ba maman ta tari numfashinta da faɗar "Koda na ji! Na san cewa ai ba kya kiran banza. Gaisuwa kuma ba za ta saka ki kira ni ba tun da ba ki riƙe ni mahaifiya ba, da dai yaya ce. Ba wannan ba dai yanzu me kike buƙata ai ni uwa ce ba zan gajiya da yi miki ba."
 
Sosa kai ta fara yi da inda-inda kamar tana gaban maman a ranta ta ce 'Mama ba dai mita ba.' A zahiri kuwa sai ta ce "Uhm! Da ma ina so ne idan ba damuwa don Allah su Ashna su dawo su sake taya ni kwana yau ma."
 
Tun da ta fara maganar maman ta sake baki, sai da ta kashe saƙar zancenta sannan ta ce da ita, "Ah! Ah! Ina ce jiyan nan da dare suka dawo daga gidan naki bayan dawowar Salisu, yanzu kuma me kike so ki ce? Salisun ya sake yin tafiya ne?" Tsuru-tsuru ta yi tana ƙoƙarin gano yadda ya kamata ta fara yi wa maman bayani kafin ta ce "Uhm! Am da ma..." Sai kuma muryarta ta fara rawa alamun kuka na neman ƙwace mata.
"Da ma me 'yar nan?" Kin sani a duhu fa.Cikin muryar kuka ta ce "Da ma Jami'an lafiya ne suka tafi da shi wai yana da cutar mashaƙo a faɗar su."
"La'ilaha illallahu Muhammadur Rasulullah! Yaushe hakan ta faru?" Maman ta faɗa tana dafe ƙirji. "Ɗazu ne ba jimawa sosai."
"To Allah ya kyauta." Maman ta maida mata sannan ta yi ɗif kamar ba za sake yin magana ba sai kuma ta ce 
"To 'yar nan sai dai ki yi haƙuri, kin san sha'anin cutar nan kowa tsorace yake da ita. Su kansu 'yan'uwan naki idan suka ji labarin me ya sami mijinki ba za su yarda su raɓe ki ba don ta yiwu ke ma kin kamu. Kawai ki yi haƙuri ki killace kan ki kamar yadda aka killace mijinki, za mu dinga kira muna jin lafiyarki." Tana gama faɗa ta katse kiran a ɗan tsorace.
Ganin hakan sai Nu'aymah ta sake kecewa da matsanancin kuka tana jin raɗaɗin yadda matar da ta riƙe a matsayin uwa ta biyu kuma uwar riƙonta ta nuna ƙyama a gare ta.
 
'Yanzu kenan idan a gaban su nake wannan ƙaddarar ta same ni sai ta guje ni?
 
Yanzu kenan 'yan'uwana da muka rayu da su tsahon shekaru sai su guje ni saboda tsoron cuta?'
 
Haka ta shafe lokaci mai tsaho tana kukan zuci da na sarari a ƙarshe haka ta haƙura ta lallashi kanta kuma ta kwana a daddafe. A wannan daren ko iska mai ƙarfi ta kaɗa sai ta ɗan firgita ballantana idan aka yi rashin sa'a wani abu ya faɗo ko ya yi ƙara. Da ƙyar ta ga wayewar gari don duk sai ta ji daren ya yi mata tsayi sosai.
Haka ta ci gaba da rayuwarta ita kaɗai ba mai shigowa gidanta kaf unguwar. Ko ɗan shigowar da Sadiya kan yi su yi 'yar hira duk ta daina. Yaran maƙota ma da take samu 'yan aike duk suka ɗauke ƙafafu a gidan. Bar ta su ma ko almajirai basa leƙowa gidan, a da kuwa ko ƙofar na rufe sukan tsaya daga waje su yi ta bara har aji. 'Yan'uwanta kuwa ko a waya ta kira su a yanzu basa ɗauka sai ka ce waɗan da aka faɗawa ana iya ɗaukar cutar a waya ma.
 
Tun daga lokacin da aka ɗauke Salis rayuwa ta yi wa Nu'aymah ƙunci, daidai da wayar samari ta daina amsawa koda an samu wani nataccen da ya kira ta kuwa. Ba wai ta haƙura da sana'ar tata ba ne, sai dai tana cikin ƙuncin da ba zai ɓoyu ba, dole ta koyawa kanta rayuwar kaɗaicin da ta aure ta. Da ma kuma kasuwar tasu a suƙe take a wannan taƙin tun da ba fita ko nan da can.
Sai bayan wasu 'yan satuka ta haƙura ta fara karɓa kiran mutanenta. Nan ma Alhaji Sani Jibiya ne kaɗai take kulawa sosai shi ma saboda ya yi mata alƙawarin canza mata waya ne. A farkon sati na uku da ɗauke Salis ne alhajin ya aiko mata da wayar har wurin aiki ta hanyar masu kawo saƙo, don zuwa lokacin ta gaji da killace kan nata kuma ba ta ga alamar sauyi ko wata cuta a tattare da ita ba sai ta cire fargabar ko mijin nata ya shafa mata cutar, don haka take amsa kira idan an buƙace ta a ofis don yin wani shiri na musamman. Sabuwar iphone 11 ce da ake ya yi a lokacin, ita dai Allah ya ɗora mata ƙaunar wayoyin yayi.
Ta yi farinciki sosai, ma fi girman abin da ya ƙara sama mata farin ciki shi ne tsohuwar wayarta tana hannunta bai karɓa ba. Ga shi kuwa abincinsu saura ƙiris ya ƙare tana ta zullumi da taraddadin yadda za ta rayu bayan ya ƙare sai ga mafita Allah ya kawo mata, don haka ta saida wayar ranar da aka buɗe kasuwa ta je ta yi cefanen kayan abinci ta zo ta ajiye.
Sai da Salis ya share sati uku cif a hannun hukumar lafiya kafin suka sallamo shi da shaidar cewa ya wartsake garas, haka ya nufo gida yana ta ja musu Allah ya isa da mita faɗar yake "Daga 'yar mura da zazzaɓi na laulayin mota shi kenan aka dabaibaye ni da sharri."
Lokacin da aka sallamo shi gaf da za a fara azumi ne don haka a gida ya azumci watan Ramadana tare da matarsa.
Ba laifi a watan sun rage wasa da ibada suna iya ƙoƙarin su na yin abin da ya sawwaƙa kamar yadda kowanne musulmi mumini ke ninnika adadin ibadarsa a watan, duk da Nu'aymah tana ta rakin yin azumi da ƙorafin yadda ya ƙara ramar da ita a kan ramar da ta yi ga kuma yanayin murɗar ciki da aman da suka dawo mata kamar lokacin baya. Bisa wannan dalilin Salis ya saka ta shirya tare da ɗaukar takardun jinyarta da rana fatse-fatse suka nufi asibiti.
Ba su suka samu ganin likita ba sai ƙarfe 3 da kusan arba'in na rana. A daddafe suka ga likitan na waccan ranar ya yi musu bayani kan cewa allurar hana ɗaukar cikin da ta sake yi ce ta janyo mata waɗannan matsaloli bayan bijirewa shawarwarinsa da suka yi a baya.
Ya yi musu iya taimakon da zai iya sannan ya sallame su bayan ya shaida musu barazanar hana ta ɗaukar ciki da allurar ka iya yi. Rai a dagule Salis ya goyo ta suka bar asibitin lokacin bai fi saura minti biyar huɗun ta yi ba, ga shi ƙarfe huɗu na bugawa dokar hana yawo a gari ke fara aiki, lokacin kuwa ba zai ishe su isa gida ba.
Ba su yi wani nisa ba suka tarar da jami'ai a bakin aiki nan suka tare shi suna tuhumar shi daga inda yake. Fuskarsa ya ƙara tamkewa yana ta cin magani. A maimakon ya yi magana sai kawai ya kashe Babur ɗin ya sauko ya je gaban su ya yi musu tsaye kamar dogari. Tambayar shi suke ba amsa a ƙarshe dai suka saka bulala suka zane shi tsaf yadda doka ta tanada. Ita kuma tana gefe tana kallo kasancewar ta mace ya sa aka tausaya mata ba a hukunta ta ba.
Bayan sun gama hukunta shi ya ɗauki abin hawansa cike da ƙuncin rai ya goya ta suka nufi gida ta layuka gudun ya bi babban titi a sake hukunta shi a gaba. Har suka je gida bai ce uffan ba sai ƙara haɗe girar sama da ƙasa da yake yana ta kumburi kamar fulawar da aka zuba ma yis.
Bayan isar su gida ya kashe Babur ɗin ko kallon ta bai yi ba ya shige ciki. Ta bi bayan shi tana tambayar "Amma Habibie Me ya sa ba ka yi musu bayanin cewa daga asibiti muke ba ka bari suka dake ka?"
Nan ma bai ce mata ci kanki ba ya shige banɗakin ɗakinsa ya maido ƙofa ya rufe. Ba ta daddara ba yana fitowa ta sake cewa "Me ya sa ka yi hakan?"
Kukan kura ya yi ya yo cikinta kamar zai rufe ta da suka yana faɗar "Tambayata ma kike? Ke me ya sa ba ki faɗa musu daga inda muke ba? Kin gama ƙona mini rai. Kin san ya na ji a lokacin da nake sauraren jawaban likita kan munafunta ta da kika yi?"
Jan jiki ta yi ta ƙara matsawa baya fuskarta na bayyanar da alamun tsoro tama kasa yi masa magana sai shi ne ya sake cewa "A lokacin ji na yi kamar in rufe ki da duka. Gudun kada a yi abin kunya ya saka ban sake furta wata kalma ba, hakan ne ya hana ni yi wa jami'an kan hanya magana don idan har na ce zan buɗi baki tabbas zan iya zage su tas ko don na huce haushina a kansu."
Ganin yana ƙara durfafo ta da rinannun idanunsa da suka kada suka yi ja ya sa ta ƙara yin baya tana faɗar "Don Allah ka yi haƙuri Habibie."
In ji hausawa suka ce wai haƙuri zuga ne, ta tabbata don kamar kada ta yi magana ya ƙara hayyaƙo mata. Ai kam ranar ta sha ruwan masifa ya zazzage mata buhu-bubun rashin albarka ko banza ga yunwar azumi ga zafin dukan da gardawa suka masa bai da halin ramawa.
Ƙari da waɗannan abubuwan ne suka saka shi ya ci gaba da kumfar baki da faɗar "Ki ji ni da kyau ina son haihuwa, lokaci ya yi da za ki sarara da wannan iskancin. Kin dai gama karatu yanzu ba wani uzuri da zai hana ki son haihuwa. Idan kuma kika yi wa kanki illa ruwanki, ni namiji ne ina da wata mafitar."
Wani irin kallo ta watsa masa sarai ta gane nufin shi yana nufin zai iya ƙaro aure, amma dai tana ta baza kunnuwa tana saurarar tatsuniyar tasa.
Da wane kuɗin zai iya aure? Ina zai saka matar? Sanin cewa labarin aure kamar ba mai yiwuwa ba ne a gare shi ya saka ba ta wani ɗaga hankalinta ba kawai sai ta ƙara ba shi haƙuri da tunanin ko zafin bulolin da aka masa ne yake hucewa a kanta.
Bai sake cewa uffan ba ya fice daga ɗakin ransa na ƙuna ya kwanta kan carfet yana sauke hucin ɓacin rai.
Haka aka gama watan yana fushi da ita sama-sama har suka je gidan malam (mahaifinsa) da gidan zamansa don yi musu barka da shan ruwa bai daina fushi da ita ba.
Sai bayan dawowarsu daga gidan ya haƙura da yake nasihohin da malam ɗin ya musu sun ratsa shi sosai don haka ne ma ya sake mata ya dawo kamar da. 
Bikin sallar wannan shekarar dai bai yi wa ɗaukacin musulmin duniya daɗi ba don ko sallar idi ba a fita ba, haka za an saka dokar hana fita yawon sallah da shagulgula da ake gudanarwa. Sai dai an sassauta dokar fita a wani yanki na wuni, shi ma sai an bi dokokin da aka tanadar. Don haka a ranar uku ga watan Sallah Nu'aymah ta shirya ta je Rikkos don gaida iyayenta.
 
 
 
Share it pls
 
ƊANYAR GUBA Book 1