Bayan Raba Tallafin Awaki, Gwamna Abba Ya Ware Biliyoyi don Auren Gata

Bayan Raba Tallafin Awaki, Gwamna Abba Ya Ware Biliyoyi don Auren Gata
 
Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ware biliyoyin kuɗi domin shirya bikin aure. Gwamnatin ta ware N2.5bn domin gudanar da bukukuwan aure a cikin ƙananan hukumomi 44 na jihar a shekarar 2025. 
Kwamishinan tsare-tsare da kasafin kuɗi na jihar, Musa Shanono, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai, cewar rahoton jaridar Leadership.
Musa Shanono ya yi bayani kan abin da kasafin kuɗin na 2025 wanda majalisar dokokin jihar ta amince da shi ya ƙunsa, rahoton Daily Post ya tabbatar. A cewarsa, gwamnati ta shirya kashe N91.32bn a fannin gudanar da mulki da samar da ingantattun ayyuka, wanda ciki har da shirya bukukuwan aure. Ya ce wannan ƙudiri yana da nufin ƙarfafa shugabanci, kare haƙƙin bil’adama, tare da ƙarfafa adalci domin ci gaban al’umma mai dorewa da kuma kyautata rayuwar jama'a. 
Musa Shanono ya bayyana cewa daga cikin adadin da aka ware, an tanadi N1bn domin rabon abinci a lokacin azumin Ramadan, an ware N955m domin gudanar da bincike kan ƙididdigar ma’aikata, binciken yanayin gidaje, da kuma yawan yaran da ba sa zuwa makaranta. Haka nan kuma, an ware N1.049bn domin siyan na'urarorin gurzo takardu, gyaran tsarin samar da ruwa, da kuma siyan kayan aiki na ɗakin karatu. 
Ya kuma ƙara da cewa an tanadi N267.6m domin samar da kayayyakin more rayuwa da kuma tallafawa aikin Da'awa tare da buga kalandar Musulunci da tallafawa sababbin shiga Musulunci. Sauran abubuwan da aka ware kuɗi domin su sun haɗa da N589m don gudanar da bincike kan tsaro da ba da tallafi, tare da dakile bara a tituna. An kuma ware N200m domin siyan kujeru da kayayyakin aiki na ofishin Akanta Janar, gyare-gyare, da sauran abubuwa.
Kwamishinan ya bayyana cewa jimillar kasafin kuɗin da aka amince da shi na 2025 ya kai N719.75bn, wanda hakan ke nuna samun ƙarin N170.59bn ko kaso 31%, fiye da asalin kasafin N549.16bn da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gabatar.