ƊANYAR GUBA: Fita Ta 13 & 14

Ba a fi mintuna biyu ba ko ta ji shigowar alert a wayarta. A hanzarce ta fita daga sansanin sada zumuntar ta buɗe ɗakin saƙunan kar-ta-kwana da ke wayarta. Ai kuwa nan maɗaukan hoton idanunta suka yi tozali da faɗowar Naira dubu ashirin a cikin asusun nata, wanda take da kyakkyawan yaƙini a zuciyarta cewa ya ba ta su ne a matsayin kyautar farko ga masoyiya don farauto zuciyarta ta amince masa bayan yana sane da cewa a haife zai haife ta.

ƊANYAR GUBA: Fita Ta 13 & 14
ƊANYAR GUBA:
page 13 & 14
"Ah! Ba fa komai Habibie wani status nake karantawa a nan ya burge ni."
Daga haka bai sake ce mata komai ba sai gajeren tsaki da ya ja a ransa yana faɗar 'Mata sai a barkus, shirmenku na dabam ne.' Ita ma ba ta ƙara magana ba ta fita daga kafar ta koma kan kafar sada zumunta ta WhatsApp bayan ta ƙudurce a ranta gobe ma za ta ƙara yin wani bidiyon da ya fi na jiya kyau don kuwa irin kalaman da ta tarar a sashen masu sharhi sun yi nasarar ƙara tunzira ta da saka ta jin cewa ita wata tsiyar ce a fannin kyau.
Tana shiga idonta ya sauka kan saƙon Alhaji Sani Jibiya sabon maneminta da mijinta bai san da wanzuwar shi ba.
"Ina so mu haɗu, yaushe kike da lokaci?"
Sai bayan mintuna bakwai da karanta saƙon nasa sannan ta mayar masa da amsa "Idan na samu lokaci zan ba ka masaniya."
Daga haka ta kashe datar gabaɗaya duk da ta ga yana ƙoƙarin yin typing sai dai tana son ta nuna masa cewa ita yarinya ce mai aji, duk da kuwa a zaƙe take da son ganin me zai rubuto, don tuni mahangar tunaninta ta hasko mata cewa lambar asusun bankinta zai nema. Amma duk da haka saida ta shafe mintuna goma kafin ta koma ta duba saƙon. Hasashen ta kuwa ya yi daidai don abin da ya nema kenan, a wannan lokacin ba ta tsaya jan aji ba kamar dai yadda ta saba ba ta jan aji a lamarin kuɗi gudun kada mutum ya canza ra'ayi da wuri. 
Ba a fi mintuna biyu ba ko ta ji shigowar alert a wayarta. A hanzarce ta fita daga sansanin sada zumuntar ta buɗe ɗakin saƙunan kar-ta-kwana da ke wayarta. Ai kuwa nan maɗaukan hoton idanunta suka yi tozali da faɗowar Naira dubu ashirin a cikin asusun nata, wanda take da kyakkyawan yaƙini a zuciyarta cewa ya ba ta su ne a matsayin kyautar farko ga masoyiya don farauto zuciyarta ta amince masa bayan yana sane da cewa a haife zai haife ta.
Duk da cewa ba wasu kuɗi ne masu yawa ba a idonta to amma duk da haka ya yi ƙoƙari, ba kowanne namiji ne zai iya yi wa mace irin wannan kyautar ba daga haɗuwar farko.
Da dare bayan Salis ya fice zuwa gidan ummansa don kai gaisuwa ta yi hanzarin rufe gidan ta ja motarta zuwa babban shagon kayan maƙulashe ta kaso dubu goma.
Rabin sayayyar tata duk kayan zaƙi ne dangin su cakulet da alawoyi da ice-cream sauran kuma snacks ne su ring donut, glazed puff-puff, Chocolate cake da su Onion rings da sauran su.
Aka zuba mata su a ledar packaging ta shagon ta sake hawo motarta a gaggauce ta nufo gida.
Daidai kan kwanar shiga gidan nata motar ta maƙale mata. Tsaki ta buga ta sauko a hanzarce tana duba agogon wayarta 9:30pm ta san zuwa yanzu koma meye Salis ya gama shi yana hanyar dawowa. Ba ta son tuhuma haka ba ta da niyyar sam mishi abubuwan da ta sayo, ga shi kuwa muddin ya dawo ta wannan hanyar zai biyo, idan ko ya riske ta dole sai ya ji dalilin fitowar da ma in da ta samo kuɗin sayayyar wannan ne ma babban abin da take ɓoye masa.
Ƙoƙarin duba matsalar take, kafin ta haska gaban motar ta lura fetur ne ya ƙare don haka ta fito tare da buɗe Boot tana jinjina gallons ɗin da suke ciki ko ta samu ragowar man da take saya a wurin yan Black market. Daidai nan ta ji ƙugin taka birkin babur a bayanta lokaci ɗaya kuma sautin shi ya ratso kunnuwanta "Nu'aymah me ya faru?" Saura kiris ta yada galan ɗin hannunta jin muryar namiji da ta so yi mata kama da ta mijinta. Numfashinta ne ya fara hawa da sauka lokaci ɗaya kuma ƙwaƙwalwarta ta yi linƙaya zuwa shekaru huɗu da 'yan watanni baya lokacin ba ta fi watanni biyar ba a gidansa, inda yake buga mata kashedin cewa koda wasa kada ta taɓa tunanin yin satar fita ba da izinin shi ba.
A iya yadda ya kausasa murya ta fahimci tsanar shi ga wannan ɗabi'ar ta kai geji, ballantana kuma zancen abin da zai zama hukuncin ta a lokacin da ta aikata hakan. A don haka cikin ladabi da tausasasshiyar murya ta amsa masa da "To in sha Allah yaya ba matsala ta ɓangarena."
"Ko ba Nu'aymar ba ce?" Wannan sautin da ya sake ratso majiyar sautukanta ne ya dawo da ita a duniyar zahiri.
A kiɗime ta waiga bugun zuciyarta na hauhawa har laɓɓanta na rawar disko alamar tana son cewa wani abu, sai kuma ta yi tozali da mai maganar cikin hasken solar da take tsaye a kan babban titin ta ratso cikin layin.
Makwafcinsu ne da bangon gidansu ke manne kuma miji ga Sadiya ƙawarta don haka ta ɗan yi murmushin yaƙe tana ƙoƙarin saita nutsuwarta kafin ta ce, "Wallahi man motata ne ya ƙare, shi ne nake ƙoƙarin dubawa ko zan samu na sakawa."
"Ayyah! Ai da kin ƙarasa gida, In ya so idan Salis ya zo sai ya siyo miki ya kai motar gida." Da mamakinta na son sanin yadda aka yi ya san Salis ba ya gida ta ce "Ka haɗu da shi ne?"
"Eh yanzun nan na baro shi a chemist ɗin Sumaila da ke nan saman mu, shi ma ya sanar da ni yana gama karɓo maganin gida ya nufo ko yanzu ma ki ga gan shi ba abin mamaki ba ne." Odar babur ɗin da suka jiyo a bayan su ne ya katse musu hirar, wanda sautin odar ya zama silar tashin lalurarta ta murɗawar ciki, 'yan hanjinta suka fara bada sauti ƙululu.
A take ta saki galan ɗin man da ta ɗauko ya faɗi ƙasa, a ɗan firgice ta juya don ganin ko shi ne. Ganin wata baƙuwar halittar a gabanta ya saka ta saki ajiyar zuciya tare da duƙawa ta ɗauko galan ɗin, a lokacin da Sani yake ɗan janye babur ɗinsa daga hanya don ya ba wa ɗaya mahayin babur ɗin damar wucewa ta hanyar da ya tare masan.
Ita kuma sai ta nufi kwararon zuba man a motar ta buɗe tana yunƙurin sakawa a gaggauce.
Sani ya kashe babur ɗinsa ya nufo ta yana faɗar "Kawo in taya ki sakawa." Ganin tana zubar da rabin feturin a ƙasa saboda yadda jikinta ke kakkarwa. A ran shi kuma yana mamakin abin da ya haifar mata da wannan ɓarin jikin 'Ikon Allah! Sai ka ce wata mara gaskiya?' ya faɗa a ransa lokacin da yake saka mata man a motar. Ita kuma ta ja gefe ta tsaya kamar 'yar doka sai waige-waige take don ta kiyaye ta inda Salis zai ɓullo mata. A ranta tana addu'ar Allah kar ya ba shi ikon ƙarasowa wurin ya tarar da ita.
A cikin abin da bai fi mintuna uku ba sani ya gama saka mata man ya yi mata sallama tare da tada babur ɗinsa ya bar gun. Ita ma a ɗari ta ƙarasa shigewa motar ta ba ta wuta.
Tun a farkon shigowar shi layin ya hango kamar motar matarsa tana karya kwanar da za ta sada ka da gidansa, hakan ya ɗan bayyanar da mamaki saman fuskarsa ya ci gaba da tuƙi yana was-wasi a ransa.
'Me zai fito da Nu'aymah da daren nan? Ko dai wurin yawon tazubar ɗin da ta saba fita ta je?' Kai da wuya idan ita ce ai ba ta faɗa mini za ta fita ba kuma ba ta satar hanya ban taɓa kamata da wannan laifin ba.' Haka ya ci gaba da karatun wasiƙar jakinsa yana yi wa tambayar da ta ziyarto zuciyarsa baiko da hasashensa har ya ƙarasa ƙofar gidan.
Kasancewar duka unguwar ta yi duhu ɗif a dalilin rashin wutar nepa, hakan ne ya ba shi damar hango hasken jajayen fitulu guda biyu da hasken su ya ratso ta ƙasan gyat ɗin gidansa waɗanda yake kyautata zaton hasken fitilun idanuwan motarta ne.
'Kenan satar hanya ta yi?' kafin ya gama zancen zucin ya ga ɗaukewar hasken cikin 'yan daƙiƙu. Wannan abin ne ya tabbatar masa da fita ta yi dawowar ta kenan. Dalilin da ya tura wankakkiyar zuciyarsa kenan ta rine da duhun ɓacin rai da ya ziyarce ta a lokacin.
A duniyarsa inda ɗabi'ar da ya tsana a cikin ɗabi'un matan hausawa ita ce satar hanya. Ya tsani wannan ɗabi'ar matuƙa gaya, mai yiwuwa kuma hakan ba ya rasa nasaba da fitinar da ɗabi'ar ta janyo wa yayarsa wanda hakan ya lalata wani ɓangare na kyakkyawan tarihin gidansu.
Idanunsa ne suka fara kaɗawa ya janyo babur ɗinsa a hankali yana ƙoƙarin haura ta ƙaramar ƙofar da yake kyautata zaton a buɗe take. Sai da ya je daf da ƙofar ya tura ta da hannu kamar yadda ya yi tsammani a buɗen take, abin da ya ƙara tabbatar masa da zargin shi, don haka ba jira ya kutsa kai cikin gidan. Tun bai gama daidaita tsayuwar babur ɗin ba ya sauko ya zira sakata kana ya nufi ɗakin gadan-gadan.
Ko sallama babu ya tura ƙofar falon ya afka sai dai bai riske ta a nan ba, kawai sai ya nufi uwar ɗakanta yana ƙoƙarin haska fitilar wayarsa. A lokacin da take kici-kicin ɓoye kayan a akwatinta da ta sauko da shi kan gado ta ji faɗowar mutum cikin ɗakin. Sa'ar ta ɗaya rashin wutar lantarki wanda hakan ne ya ba ta damar ƙara tura ledar kayan maƙulashen cikin akwati tare da hanzarin danne ta da wasu tufafi.
"Daga ina kike cikin daren nan Nu'aymah?" Wannan tambayar da ya watso mata ce ta sa ba shiri ta saki murfin akwatin ya dawo ya rufe kansa.
Cikin in-ina ta ce "Me....me ka gani ne?"
"Kar ki raina mini hankali,ni fa ba yaron goye ba ne, kuma na ga tsayuwar motarki a cikin gidan nan, daga ina kike?" Ya faɗa a fusace.
Sai da ta haɗiye wani yawu muƙut kafin ta aro kallabin jarumta ta ɗaura sannan ta ce "Da gaske ba inda na je fa."
Daga jin yanayin muryarta za ka fahimci a tsorace take matuƙa don tun da suke da shi za ta iya cewa ba ta taɓa ganin ɓacin ransa irin na yau ba. Duk da ba ta iya ganin fuskarsa amma yanayin muryarsa kaɗai ya ba ta tabbacin cewa a fusace yake ainun. A iya sanin ta duk girman laifin da ta yi masa ba ya fasa kiran ta da sunan Habibtie, amma yau sai ga shi ya kirawo sunanta gaya ba ko miya ballantana kayan haɗin armashi.
"Ba inda kika je shi ne na gan ki sanye da Hijabi?" "Sal...sallah fa na gama kafin na cire hijabin shi ne na tsaya aikin gyaran akwati...."
Kafin ta dire zancen ta mai fita da sautin in-ina ta rashin gaskiya ya katse mata hanzari da faɗar.
"Idan ma kin fita ɗin ki sani, daga yau sai yau, kar ki sake fita ba izinina, zan iya jure kowacce ɗabi'a ta matar Bahaushe amma ban da wannan. Kn ji ni?" Ta ɗaga masa kai alamun tabbatarwa kafin ya juya da zimmar ficewa daga daƙin nata yana faɗar "Idan kuma kin ƙi ji ba kya ƙi gani ba ai."
Ƙwafa ya yi a zuciyarsa yana faɗar 'Koma mene ne laifina ne da na biye wa son abin duniya na koya mata yawo, ga shi tana ƙoƙarin fin ƙarfina.' Da wannan zancen zucin ya faɗa nasa ɗakin yana banko ƙofa cike da ƙunar zuciya. Bayan ficewar shi ta faɗi kwance kan gadon ta baya tana mayar da numfashi tamkar wacce ta yi gudun famfalaƙi.
*********
Bayan kwana biyu ta aike wa Alhaji Sani Jibiya da saƙon inda za su haɗu da lokaci. Ya nuna mata cewa shi ya fi son ya zo gidan iyayenta su yi zancen, amma sai ta nuna masa tana jin fargaba da kuma kunya. Shi kuma rashin sanin takamaiman dalilin da yake saka ta fargabar ya saka ya amince mata kuma ya je inda ta zaɓar mu sun don ya ji shaƙuwar ta (ma'ana ya ji dalilin nata)
Bayan sun haɗu ya yi mata tayin aiki a kamfaninsa na shinkafa amma kuma kafin ya ba ta aikin yana da sharaɗai.
Da farko Nu'aymah ta zata sharaɗan masu sauƙi ne sai dai kuma abin ya zo mata da saɓanin haka. Sharaɗan da ya gindayo ba abu ba ne mai sauƙi ta iya cika su.
A hanyarta ta dawowa tafe take tana tunanin mafita, ta sani cewa tana tsananin buƙatar wannan aikin da matsayin kujerar da zai ba ta ko don burinta na zama hamshaƙiyar mai kuɗi kuma sananniya a duniya ya tabbata. A ɗaya ɓangaren kuma tana son tallafawa burin mijinta. To amma taya za ta iya cika sharaɗan? Kanta ne ya ɗauki caji sosai.
'Ki je wa Salis da zancen, zai taya ki nemo mafita tun da ba wannan ne karon farko da yake taya ɓera ɓari ba.' zuciyarta ta shawarce ta, ba ko musu ta karɓi shawarar tare da ƙarawa giyar motarta sauri, tabbas lokaci ya yi da za ta bayyana masa wannan manemin da take ɓoye masa. Bayan ta koma gida ba ta riske shi a gidan ba hakan ya saka ta zauna ta ci gaba da karatun wasikar jaki daki-daki.
Da ta ga hakan ba mafita ba ce a gare ta sai ta miƙe ta je kitchen don ɗora abincin yamma. Sai da ta duba ma'ajiyar kayan abincinsu ta lura da cewa sun yi ƙasa sosai don kuwa iya shinkafa kwano ɗaya ya rage kayan miyar ma babu, haka maggi sai fa ragowar guda biyu cikin wanda Salis ya sayo a jiya suka yi amfani da shi tun jiyan.
Kusan wannan abin ya ƙara ƙarfafa mata gwuiwa a kan ta aikata komai don samun kuɗi, don kuwa ba za ta iya rayuwar jin daɗi ba su ba. 'Ba zai yiwu na rayu da yunwa a lokacin tasowa ta yanzun ma na ci gaba da yin ta ba, bayan ina da cikakkiyar dama a hannuna.' da wannan zancen zucin ta saki buhun da ke riƙe a hannunta ta fito tare da ɗaukar jakarta purse da hijabinta da ke ajiye a kujerar falo ta rufe ƙofar falon ta fita tsakar gidan. Har ta taɓa ƙofar fitar da nufin buɗe wa ta fita kuma ta ja ta yi turus. Kamar a majigi sina-sinan dambarwar da suka sha shekaranjiya a kan ta yi satar fita suka ci gaba da hasko mata a idanuwanta.
Don haka sai ta yanke shawarar komawa ciki ta ci 'yan kayan maƙulashenta da ta ɓoye. Sai kuma ta sake tuna cewa rabon ta da abincin kirki tun karin kumallo ga shi ba ta san yaushe zai dawo ba, kuma tana da tabbacin ababen maƙulashen ba za su riƙe ta ba. Don haka ta zaro wayar daga ƙaramar jakar ta danna masa kira kamar yadda wani ɓangare na zuciyarta ya umurce ta da yi.
Bayan ta gabatar masa da uzirinta kuma ta samu amincewar shi sai kawai ta fice ta taka da ƙafa zuwa titi.
Ta sayo kayan miya, kabeji, bama da kifin gwangwani da sauran abubuwan da take buƙata. Duk wannan kuɗin da ta kashe ta yi ne a cikin tukuicin tagomashin da ta samu a wurin alaji Sani Jibiya.
Gidan ta koma ta yi musu lafiyayyen girki mai daɗin ƙamshi ta kwashe a kuloli masu kyau. Ba shi ya dawo gidan ba sai bayan azahar. Daddaɗan ƙamshin girkinta ne ya amsa masa sallama, ya ƙarasa ciki yana murmushi da bin kwanon abincin da kallo. Ɗagowa ta yi riƙe da tiren shinkafa a hannunta ta juyo ta kalle shi, sai da ta haɗe lomar da ke bakinta kafin ta amsa masa sallama.
Da ƙyar ta bari ya iya cin abinci kafin ta gabatar masa da zancen da zuciyarta ke azalzala mata yin shi.
Fuskantar shi ta yi sosai ta ci serious kafin ta ce "Habibie wani alhaji ne ya je wurin aikinmu ɗazu ya ce yana jin daɗin muryata kuma yana sona har ya yi mini tayin aiki a kamfaninsa sai dai a bisa wasu ƙwararan sharaɗai guda biyu."
Lokacin da ta ambaci wani ya ce yana son ta sai da ya ji wani tuƙuƙin baƙin ciki a ransa ya ji kamar ta soka masa kibiya a ƙahon zuci. To amma ba yadda ya iya dole ya danne kishin kamar yadda yake yi lokuta da dama da yake sakarwa son zuciyarsa linzamin da yake sarrafa shi. Don shi a ganin shi ba shi da wata hanya mai sauƙi da maƙudan kuɗi za su riƙa shigo shi ban da ta wannan free idea ɗin, don haka ya saka wasu duwatsu masu nauyi ya danne tuƙuƙin kishin da ya yi hanƙoro yake yunƙurin biyo wasu magudanan jini ya bayyana a fuska da laɓɓansa ya ce da ita. "Ina jin ki mene ne sharaɗan?"
Ta ƙara bayyanar da damuwa a fuskarta kafin ta ce "Sharaɗi na farko sai na gabatar da shi a wurin magabatana a matsayin manemin aurena, sharaɗi na biyu sai na yi masa alƙawarin aure nan da wata shida, kuma duk a ranar da na karye alƙawarin to a bakin aikina."
"Shin a hasashenki nauyin aljihunsa ya kai yaya?" Salis ya tari numfashinta da wannan tambayar.
"Ba zan iya cewa ga adadi ba, domin a iya 'yar gabatarwar da ya yi mini kamfani uku ya bayyana mini a matsayin nasa, ban da hannun jari masu ƙarfi da yake da su a ƙasashen ƙetare da ya ɓoye mini." Ya ɗago tare da zuba mata fararen idanuwansa masu ɗauke da baƙar ƙwaya a cikin su.
Irin kallon da yake yi mata kallo ne mai nuna tsantsan mamaki. 'Taya ya mutum zai kunce wa mace manyan sirrukan shi haka daga haɗuwar farko? Ai komai daƙiƙantakar mutum ya yi lissafi kafin faɗar wannan saboda gujewa abin da ka je ya zo.' Duk da cewa ta iya karantar saƙon da ke kan fuskarsa sosai, amma sai ta yi shiru ta ba shi damar tambayawa da kansa."Taya ya duk kika san wannan?"
Ƙayataccen murmushi ta yi sannan ta baro kujerar da take zaune zuwa wacce yake kai riƙe da waya a hannunta. Sai da ta yi 'yan danne-danne a wayar kafin ta miƙo masa tana faɗar "Kalla ka gani?"
Amsa ya yi ya duba bai gane komai ba, ba tare da ya ɗago ba bai kuma yi nauyin baki ba wurin tambayar "Miye wannan ɗin?"
"Wata manhaja ce ta bindiddigi a waya. Ni ma wani course mate ɗina ne ya koya mini aiki da ita. A duk lokacin da muka haɗu da mutum nakan yi ƙoƙari na karɓi wayarsa idan yana amfani da Gb WhatsApp sai na yi connecting. Daga nan kuma komai yake tattaunawa da abokan hulɗarsa manhajar zan iya gani, koda voice ne zan iya saurara kamar ma tare da ni ake hirar. Idan na yi rashin sa'a mutum wayayye ne mai wayau da ya lura yake dakatar da ni. Amma shi wannan alhajin da alama irin shige-shigen nan ba sabgoginsa ba ne zubin mutanen da ne da shi. To ta haka nake jin duk wata harƙallar kuɗi da yake da ma shige da fice na dukiyarsa."
Miƙewa tsaye Salis ya yi a lokacin da murmushi ke bayyana a fuskarsa. A zuciyarsa kuwa har ya gama ƙissima abubuwan da zai yi da kuɗin da za su tatsa gun alhajin. Ta ɗayan ɓangaren kuma yana tunanin jifar tsuntsu biyu da dutse ɗaya, don haka ya fara takawa gaba kaɗan kafin ya ce "Kawai ki gabatar da ni a matsayin yayanki, sai ki bar sauran lamarin a hannuna."
Saukar kalaman nasa a kunnuwanta ne suka dasƙarar da ita a zaune. Yanzu kam ba ko tantama dole ta yarda da zargin da wani ɓangare na zuciyarta ke yi mata a kan cewa Salis ba ya ƙaunar ta kawai yana amfani da ita ne don cika muradan zuciyarsa. Amma idan ba haka ba taya za a ce shi kwata-kwata ba ya kishin ta a cikin zuciyarsa. Taya ne ma za a ce miji ne zai shigewa matarsa gaba a lokacin da wani yake ƙoƙarin neman aurenta? 'Lallai lamarin Salis ya zo mata da saɓanin hankali.
Jin ta yi shiru ba ta ce komai ba ne ya saka shi waigowa ya ce da ita "Ya ba ki ce komai ba?" "Uhmm! Na ji ka ina ɗan wani nazari ne."
"Me kenan?" Ya tambaya.
"Ka san dai dole zai buƙaci a yi zaman da iyayenmu ko da ba yanzu ba a gaba kaɗan zai neme zuwa gidanmu don ganawa da su, ina kake tunanin za mu samo ababen nan guda biyu?" Ta nisa kafin ma ya yi magana ta sake cewa,
"Ba ma wannan ne abin damuwar ba, taya ya kake ganin zan yi aure cikin aure abin da yake haramun ne a addinance? Shin za ka iya sallama ni ga wani saboda abin duniya? Gaskiya ina ga mu dai sake shawara."
"Hahaha.." ya sheƙe da wata mahaukaciyar dariya kafin ya tsagaita ya ce "Habah Habibtie! Sai ka ce ba ke ba ce baby Nu'aymah wacce ta ƙware a bada shawara irin wannan? Ina kaifin ƙwaƙwalwarki ya tafi ne?" Ya numfasa kafin ya ɗora da faɗar
"Kar ki wani damu, kawai ki faɗa masa cewa iyayenki sun yi tafiya ƙasashen ketare ba za su dawo ba sai bayan shekara biyu don haka za ki haɗa shi da yayanki su gaisa idan ya so zancen auren sai a yi shi idan iyayen namu sun dawo. Kin ga kafin sannan mun tatiki abin da muka tatika mun saita masa hanya."
"Idan ya nemi mu haɗu a gidanmu fa? Sanin kanka ne dai ba zai yiwu mu kawo shi nan ba." Ta faɗa da sauran ragowar damuwa a fuskarta.
"Wannan ma ba wata matsala, da ma hausawa kan ce ajiya maganin watarana. Ina wannan gidan naki da kika saya bayan kin wanko wani Gara a Bauchi shekara ɗaya baya? To da shi za mu yi amfani."
"Akwai 'yan haya a ciki fa ko ka manta ne?" Ana ba ki kina roƙo Habibtie, ke za ki san dabarar da za ki yi wa 'yan hayar su ara miki gidan na tsawon wuni ɗaya ba tare da sun fahimci hakan ba. Babbar harka ce fa za ta fashe."
Sai a lokacin ta ƙyalƙyale da dariya sai da ta yi mai isar ta sannan ta ce "Kanka na kawo wuta fa Habibie, sai yanzu na fahimta amma da duk na tsorata da na ji kana shirin sallama ni ga wani." Ta ƙarashe batun tana taɓe baki alamun shagwaɓa.
"Tab! An faɗa miki hauka nake da zan bar wa wani zuƙeƙiyar mace irin ki?"
Ta yi murmushi jin daɗi tana kai masa dukan wasa da faɗar "Kai ko?" Ya goce shi ma yana dariya sannan ya fice daga gidan.
Ita kuma ta koma ta zauna daga inda ta tashi tana ta murmushi ita kaɗai da yabawa fikrar mijin nata.
********
Kamar dai yadda ya faɗa hakan ce ta faru bayan sati ɗaya Alhaji Sani yana takura mata da son zuwa gidansu, ta gayyace shi zuwa wannan sabon gidan nata da yake a sabuwar unguwar da ba ta cika ba, haka kuma ba a san su a can ba. Ta caɓa ado na kece raini cikin tsadadden leshin da zai kai dubu ashirin da biyar kalar golden yellow da ratsin baƙi, ta yi kyau sosai a cikin shigar.
Da misalin ƙarfe huɗu na yamma alhaji Sani Jibiya ya ci burki a ƙofar gidan da aka kwatanta masa. Bayan sun gaisa Nu'aymah ta gabatar masa da Salis da sunan shi ne babban yayanta Sadik. A mutunce suka gaisa ya gabatar da kansa a matsayin masoyi kuma manemin auren Nu'aymah. Salis ya nuna masa farincikinsa muraran sannan ya gabatar da uzurin tafiyar mahaifansu da neman alfarmar a jinkirta neman auren har lokacin da za su dawo, domin yana da yaƙinin a yanzu ba za su amshi batun auren ba. Ba haka alhaji Sanin ya so ba, amma ganin yadda ya samu karɓuwa a wurin yayanta sai ya ce "uhmm! To ba komai malam Sadik, Allah ya sa jinkiri ya zame mana alkhairi. Sannan ina mai maku albishir da cewa in Sha Allah nan ba da jimawa ba zan ba ta aiki a ƙarƙashin kamfanina."
Salis ya masa godiya sannan ya fice zuwa ƙofar gida don ya ba su damar zantawa. Da suka gama zancen ne ya raka shi bakin mota, har ya shiga motar kuma kamar wanda ya tuna wani abu ya ciro kuɗi a gaban motarsa ya ba wa yayan. Godiya Salis ya yi sannan ya juya cikin gidan bayan ya ɓoye kuɗin a aljihun shi.
Daga shigar shi ciki ya yi mata zancen raba kuɗin da ta samu ita kuwa ta kafe a kan cewa ai ta san an ba shi na shi kason don haka kowa ya riƙe na hannun shi.
Da dai ta ga ran Salis ɗin ya ɓaci har hakan na shirin janyo musu rikicin da suka saba yayin kasafin kuɗin da suka samu sai ta ce da shi.
"Ka kwantar da hankalinka yayana idan aikin nan ya tabbata kuwa ka fara shirin zama hamshaƙin attajiri don zan nemo mana hanya mafi sauƙi ta mallake dukkan abin da ya tara, kuma kana sane da cewa kai ne za ka maye gurbin shi." Da wannan dai ta samu ta lallaɓa shi bayan ta yaga masa wani abu kaɗan ta nufi gidan su na asali shi kuma ya tafi gararambarsa a gari.
*******
Can da bayan magariba ta zauna ta ɗauko wayarta ta shiga jadawalin jerin sunayen numbobin mutanen da ke ajiye a ciki tana rage tsofaffi kuma waɗanda amfanin su ya ƙare a gare ta. Tana zuwa kan Ma'aruf har ta wuce kuma sai ta dawo kan number tasa ta tsaya tana tunanin ya dace ya bi ayari ko a'a. 'Idan abin sha ya ƙare fasa kwalbar ake yi don ba ta da amfani.' Zuciyarta ta jefo mata wannan azancin da ya ƙarfafa mata gwuiwar aikata abin da ta yi nufi.
'Uhm! Uhm fa Nu'aymah! Ma'aruf ya taka muhimmiyar rawa a rayuwarki, musamman da ya nema miki ilimin da a yanzu kike tutiya da shi har kike jin kin fi karfinsa, kuma ba wanda kike cin amfaninsa sama da shi fa, aikin ma da kike taƙama da shi a silar wa kika samu?' Wata zuciyar ta tunatar da ita, duk da haka da ta tuna cewa ta yi sabbin kamu a ciki har da Alhaji Sani da ba ya jin shakkar kashe ko nawa ne a kanta ba tare da ya taɓa furta mata koda kalmar banza ba, kawai sai ta biyewa zugar zuciya ta jefa number Ma'aruf a black list alamun ta gama da babin rayuwarsa a littafin tata rayuwar kuma ba ta tsammanin wannan babin zai kuma maimaituwa a cikin littafin har ƙarshen rayuwarta. A haka ta ci gaba da rage numbobi sai da ta goge lamba sama da ashirin da biyar kafin ta ajiye wayar da tunanin dabarar da za ta yi a samu wani ya canza mata waya zuwa wacce ake ya yi.
Share it pls
ƊANYAR GUBA.