DA AURE NAH
*NA*
*HAUWA'U SALISU*
Binta da kallo kawai nake bakina bude Dan inban mantaba sainaji tana sun rasa Habeeb wane Habeeb kenan Husna a fili nake duk maganar danake Dan haka taban amsarda har yau nagaxa mantata
Yah Habeeb naki na gidanmu mijinki daxaki aura shine yarasu Ikon Allah kawai ya xaunai dani gun idanuwana suka fito kuru kuru nadinga kokowa da numfashina amma ina da gaske soyake yaimun yajin aiki Nikam nace sai hakuri Huwailat
Bin kofar gidansu da kallo nai kawai naga Habeeb ya fito rai bace yanata maxurai cikin gudun bala I na fada kirjinsa taya xa aimun wasan ka mutu bayan Kaine yanxu haka gabana nakamasa nariqe gam
Husnah xo ga yah Habeeb na kamasa duba ki gani yanada rai gama shaida na sake qwaqwumesa gam karma tsautsai yasa ya sullemin
Bansan ya akaiba nagasu Baba kaina yana tofamun addu a nikam janyo Habeeb nake ina kaima Baba magana yasan kana raye Dan Allah kace wani Abu Dan Allah yah Habeeb kataimaki xuciyata kai magana kanafa raye Cikin juriya Babansu Habeeb yaxo ya kama hannuna yajani cikin gidansu Habeeb amma ina riqe gam da Habeeb dina mutane cike fal gidan sunata karatun Qur ani naita binsu da idanuwana dake jajir har muka shiga Dakin Babansu anan naga makara kwance da mutum cikinta Qara damqe yah Habeeb nayi sosai na rakube bayansa cikin jarumta Babansu Habeeb ya Yaye likkafanin waxan gani
Yah Habeeb ne kwance kamar yana barci cikin raxana nadubi Habeeb dinda na riqe gam a hannuna Saina tsinkayi muryan Babansu Habeeb nafadan wannan yayan Habeeb ne Sulaiman dake aikin soja nariqe Innalillahi wa inna ilaihirraji un
Haka xuciyata ke ambata amma gaba daya komi nawa ya tsaya ya daina aiki Cikin wani bahagon yanayi nasaki Yah Sulaiman na isa kan gawai Yah Habeeb idanuwana suka bushe nagaxa xuboda hawaye ko qanqani nagaxa magana bin gawai da ido kawai nake Dan abunda jikina xai iya kenan
Kidaure kiyi masa bankwana muryai Babanmu kenan Nagado na kalli Babanah sainaga kamar bashiba kallonsa nake sosai nakeson naji ya maimaita maganarsa amma ina sadda kansa kasa yaima na maida idona kan Wanda aka kira yah Sulaiman shima kansa kasa Wani banxan murmushi nasaki Wanda yafi kukan jini axaba na Dora kaina saman fuskan gawai yah Habeeb nayi tsit
Baba ne yace ajanyeni mutane najira waje kafin yah Sulaiman ya xo gun nadaga gawan yah Habeeb nakoma gefe guda natakure ina riqe da saitin xuciyata daketa wata suka ba sukaba bansan kalan abunda nakejiba Ahankali suka maida masa likkafaninsa suka daga makarai suna kabbara sukai waje Yasalam da gaske narasa yah Habeeb kenan minayi masa da xafi haka daya tafi ya barni Wata xuciyar tace kul Huwailat karki sabama Allah kan abunda kinsan ya wajaba kan kowa Ban ankaraba naji andafani nadago kwala kwalan idanuna da suka bushe Dan ganin waye Mamansu Habeeb ce kiyi hakuri kidau dangana duk mai rai mamaci ne
Diyata Sannan na ankara da bakowa dakin saini da ita kaddai suntafi da yah Habeeb da hanxari natashi nai waje da gudu ina kwadamasa kira
yah Habeeb
yah Habeeb
yah Habeeb
Dai dai sannan aka daga makarai xa a fara tafiya cikin saurin baxata na iskesu nariqe makarai gam ina bai mutuba kutaimaka zai farka wasa yakemun munyi alqawarin aure dashi wallahi ba wasa nakeba Kutambayi su mama saura wata uku bikinmu taya xakuce ya mutu gashi naga yana motsawa kuxo ku gani ma da gaske nake
Bansan wadanne marassa tausan bane suka daukeni xuwa cikin gidanmu akatafi kai gawai Yah Habeeb makabarta
Wayyo rayuwa ba tabbas haka na kwana tunanin kodai wasane yakemun To idan wasane hada sauran jama a xaimawa Banci bansha sai bin mutane da idanuwa na rame na bushe a cikin kwana guda Haka akagama xaman gaisuwa aka watse akabarni da daci a xuciyata Bayan wata biyu da rasuwan Habeeb abubuwa sun jagule mun sosai aka kirani falon Baba na iske duka iyayenmu na gun
Babansu Habeeb yakirani diyata alfarma naxo nema gunki Dan Allah ki amince a daura auren da Sulaiman Dan uwan Habeeb din Ras gabana ya fadi sai aranai wani marayan kuka ya kwacemun sosai hakan yasa suka tafi ba amsa mai kyau daga guna sai kuka To mai karatu Huwailat xata amince kuwa da wannan hadi.
Ku biyo Haupha da amsarku.
Nagode