DA AURE NAH:Labarin Cin Amana Mai Muni, Fita Ta Uku

DA AURE NAH:Labarin Cin Amana Mai Muni, Fita Ta Uku


DA AURE NAH

*NA* *HAUWA'U SALISU*

Page 3

Ba zan gaji da miƙa godiya ta da jinjina ga my M K ba Allah yabar tare Ameen.

Huwailat Abdullahi Samaru shi ne cikekken sunana mahaifina Alh Abdullahi ya kasance ɗan asalin garin Adamawa ne wanda yawon neman na kai ya kawoshi jahar Kaduna har Allah yasa ya zauna a cikin Samarun Zariya inda yasamu wani bawan Allah ya ba shi shago ya dinga jire masa don yaga yana da amana, cikin ikon Allah kuwa akaita samun alkhairi nan da nan, ko anbashi sallamarsa bai amsa, dan yana masa duk abun buƙata, da Alhajin yaga haka bayan wasu yan shekaru sai ya buɗe wani shagon ya danƙasa ga Abdullahi yace "Ga shi nan kaima ka tsaya da ƙafafuwanka kamar kowa, kuma kaje gidana ku daidaita da Zuhrah na baka ita zaman haka nan ba aure ya isa."

Cikin matuƙar farin ciki yai 'godiya matuƙa har yana jin kamar almara wai shi ne zai auri Zuhra yarinya mai kyau da kamala koda yaushe cikin shigar mutunci gata da daraja manya, gaskiya ya yi dace Allah yasa taso shi da yafi kowa murna da jin daɗin rayuwa.

Abdullahi ko kana da wadda kake sone naima shigar sauri? Cewar Alhaji Mamuda. 6cikin washe baki Abdullahi yace "Ko kaɗan, Wallahi ina matuƙar godiya Allah Ya saka da alkhairi ya ƙara girma, amma inba damuwa zan shirya naje can wajenmu dan na fada masu su zo N'neman auren." yana magana yana qara sunne kansa Qasa Alhaji yace ba damuwa indan wannan inka shirya kaimun magana yai godiya sosai yatashi ya tafi yana tunanin yanda xai fuskanci Zuhra da wannan almari ko xata Amince koko baxata Amince ba fargaba ta samu xuciyarsa karfa taqi yarda hakan baqaramin tada masa hankali xaiba amma dai xai jaraba xuwa anjima da dare gunta yaji ta bakinta fatansa yaji khairan daga gareta Dare nayi Abdullahi ya shirya tsab yacaba kwalliyarsa ya fesa turarensa yaje gun Zuhra Dan yagabatar mata da kansa da abunda yakawosa abun farin ciki Zuhra tafada masa ita mahaifinta yafara fadamawa kafinshi kuma ta yarda ta Amince fatanta yariqeta da mutunci Sundan taba hira yafada mata xaije garinsu Adamawa yataho da iyayensa su naima masa Aurenta taimasa fatan alkhairi suka rabu Bayan sati Abdullahi yakama hanyar Adamawa ya fadama yayyensa da Mahaifiyarsa don Mahaifinsu Ya rasu sun jinjina lamarin inda suka dinga nuna masa yahakura yai Auren gida yafi yaje wata uwa duniya yai Aure ga kuma yan uwansa mata cike da gari amma saiya tsallaka wata Jaha can shidai yadinga kwatanta masu qima da darajan Alhaji Mamuda harmada son da yakema Zuhra Akan dole suka yarda suka shiryo suka biyoshi da duk abunda yafada masu anayi na al adar samarun Sai dai suna xuwa labarin yasha banban

Dan Alhaji Mamuda yace baxai amshi komiba sai sadaki naira dubu goma wannan karamci ya birgesu sun kuma yarda da maganar Qaninsu daya fada kan Alhaji Mamuda Dan haka cikin mutunci akai komi da komi suka tsaida biki nan da sati guda kacal Da daddare Alhaji Mamuda ya kira Abdullahi yatambayesa kana da inda xaka aje matarkane Yace mun magana da Abokina Isiyaku xai nema mun gidan haya kafin nayi nawa in Allah ya hore Alhaji Mamuda yai murmushi yace to tawa gudummuwar itace gidana dake qasan layin shagonka yasa hannu ya dauko takardun gidan yamiqa masa Allah ya Baku xaman lafiya Kasa magana yayi Dan Alhaji ya gama masa komi ga mata ga jari ga matsugunni lallai Alhaji mutum ne harda rabinsa ma Godiya yafara xubawa

Alhaji ya dakatar dashi ya shige gida yabarsa cike da farin ciki yaje ya gwadama yan uwansa suka sake Aminta da Dan uwansu yasamu ubangida nagari mai alkhairi dabaya da qyashi Anan suka dinga masa nasiha da kwatanci kan yariqe matarsa da qima yaqara daraja Alhaji Dan ya gama masa komi ya guji son xuciya duk da ba halinsa bane amma xuciya batada kashi Ranar juma a yakamata daurin Aure bayan an sauko sallan juma a aka daura Auren Zuhra Adamu Samaru da Angonta Abdullahi Garba Adamawa Amarya ta tare gidanta cikin kwanciyar hankali da lumana Ahankali Arxiqinsu keta habaka a gefe guda kuma Yakoma karatunsa inda yasamu damar shiga jami ar Xariya cikin nasara da taimakon Allah ya kammala karatunsa Sirikinsa ya nema masa aiki a cikin Zaria Asannan Zuhra tana da yaranta Hudu Abba ne Babba Mamuda shiyaci sunan Alhaji sai Mustapha nabi masa Garba da suke cema Malam saini Autah Huwailat Tunda nafara wayau na girma nake da burin karatu mai xurfi Dan akwai wani makwabcinmu Alhaji Sanusi Dr naji ana kiransa amma bantaba ganinsa da kayan malaman Asibitiba Dan haka nake tambayar yah Abba waishi Dr dama basaiya saka fararen kaya bane kuma ba sai yayi alluraba Sabodame kika tambayen saboda naga Alhaji Sanusi baya sasu amma ana kiransa Dr Dariya yayi kincika Tambaya Autar Mama Aiba dole saika karanci Likita ake kiranka Dr ba shi akan karatunsa ne yazama Dr dariya nayi to Yah Abba kenan nima xan iya xama Dr Ashe nan gaba ammafa ni nafison naxama Dr din Dalibai manya Sanin halina da tambayoyi yasa yace to kidage xan saki makarantai kuwa Ina gama primary naci ta kwana nan kuma Mama tace bata yardaba natafi wani uwa duniya saboda karatun boko naita kwana kodai asakemun ko kuma nabar makarantai Da Qal akasamo min Jeka ka dawo dake nan cikin garinmu nafara xuwa Ina Class 3 nafara samari abunda yajamun fada sosai a gidanmu Wanda har kuka yinakeyi in anamun fada Amma duk da hakan acikin samarina ina matuqar son wani Habeeb a bayan Anguwarmu yake so tari inxani islamiyya ina kamasa yana kallona da mun hada ido xai murmushi baitaba min magana ba amma fuskansa baya raboda murmushi duk sanda muka hadu Tofa yakenan jama a managarciya.com