Abin Da Babba Ya Hango:Fita Ta Hudu

Karo na farko tun bayan aurensu da ta nufi kitchin da niyar ɗaura girki.

Abin Da Babba Ya Hango:Fita Ta Hudu

ABINDA BABBA YA HANGO.......!


RUBUTAWA; DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.

بسم الله الرحمن الرحيم

Fitowa ta huɗu.


```Sai bayan ta sauke Hajiya Turai a ƙofar gidan ta ne, sannan  ta fara tunanin ta yadda za ta samu damar da za ta aiwatar da ƙudirinta.

Sosai ta shiga tunani, ta dai san tsawon shekara ɗaya da wata uku da aurensu da Kasim sau ɗaya ne kachal ta taɓa zuwa gidansu.
Nan kuma wani tunanin ne ya koma tarbonta, ta tuna ko rasuwar mahaifinsa bata je gaisuwa ba.

Sosai ta shiga cikin ruɗani sai can kuma ta ce "dole ne ma yau ɗin nan mu shirya da Kasim.

Cike da ƙwarin gwiwa ta shiga gidan, parking space ta nufa ta yi parking kana ta yi cikin gidan.

Karo na farko tun bayan aurensu da ta nufi kitchin da niyar ɗaura girki.

Sai da ta gyara kitchin ɗin sama sama ta wanke wadansu kwanukan suma, sama-sama, kana ta ɗaura girki.

White-fice da stew wace ta ji kayan lambu, ta girka sannan ta janyo sabbin kuloli ta sanyawa megidan sannan ta sanywa Hajiya Umma a cikin wata haɗaɗɗiyar kula kana ta kawo maganin ta sanya a cikin miya ta motse.

Bedroom ta nufa ta cire kayanta ta ɗaura towel ta nufi ban ɗaki, ta silalo wanka wanda rabonta da wanka ta yi 2weeks kullum sai dai a feshe jiki da turare a bi hanya.

Gaban mirror ta zauna kana fara fente fuskarta da kayan shafawa iri-iri, daga bisani kuma ta janyo wata doguwar riga roba mai adon stone stone ta sanya ta janyo wani baƙin ɗankwali ta buga ɗauri ta feshe dukkanin ilahirin jikinta da turare.

Sosai kyaunta ya fito ta yi fess da'ita kamar a sace ta a gudu.

Parlour ta koma ta harɗe cikin kujera ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya.

Sai bayan sallar magrib sannan ya shigo gidan gabansa na faman buga wa.

A Parlour ya tarar da'ita ta harɗe sai faman ƙyalli takecyi, da saurinta ta miƙe ta tarbo shi.

Kana ta taimaka masa ya yi wanka , shi dai duk mamakin canjin da ya sa mu ya cika masa ciki, amman ba damar tambaya yanzu.

Parlour suka fito ta gabatar masa da abinci , wannan karon mamakinsa kasa ɓoyuwa ya yi saida ya fito fili.

Ganin yana batun yi mata magana ne ya sanya ta saurin ɗaura farcen ta a kan bakinsa, kana ta zuba masa abincin.

Sai da ya cika cikinsa maƙil kana ta gabatar masa da abincin Hajiya Umma cike da tsantsar mamaki haɗi da murnar ta fara kulawa da lamarinsa har dana mahaifiyarsa ya fice da abincin daga gidan ya nufi gidansu.

Sashen Hajiya Umma ya nufa hannunsa ɗauke da basket bakinnan nasa ya kasa rufuwa dan tsananin murna.

Zaune suke a Parlour Hussaina da Maimunatu sai Hassana dake bedroom ita da Hajiya Umma.

Sallama ya yi  amsawa suka yi su dukansu suna masu zubawa ƙofar shiga ɗakin idanuwa.

Karafff idanuwasa suka faɗa cikin nata, da hanzarinta ta miƙe tana me yi wa Hussaina sallama yayinda gabanta ya dinga faɗuwa.

Gaida shi ta yi da hanzarinta kana ta fice daga ɗakin ta nufi sashen su.

Gaida shi Hussaina ta yi , amsawa ya yi yana tambayar ina Hajiya da Hassana?.

Nuna masa bedroom ta yi da hannunta kana ta ce "suna ciki kayan guga suke jerawa."

Harya miƙe da niyar shiga ɗakin saiga Hajiya Umma ta fito daga cikin ɗakin ,mace mai tsananin kwarjini haɗi da kamala.

Ɗan basarwa ta yi sannan ta ce "au kai ne a tafe da daren nan?."

Hassana ce da ta fito daga bedroom ɗin ta sanya dariya sannan ta ce "oh ba'a fadan sunansa sai dai ace kai ne?".

Filon dake gefensa ya janyo haɗi da wurga mata shi, da sauri ta kauce tana faman ƙumshe dariyarta.

Gaisawa suka yi sosai da mahaifiyar tasa da 'yan ƙannen nasa, sannan ya ya ce "Hajiya ga saƙonan inji ZULFA'U ta ce tana gaida ku."

Riƙe baki Hajiya Umma ta yi sannan ta ce "yau kuma?, Ikon Allah, ashe ina da rabo da abin gidan ka."

Sosai kalaman suka girgiza shi sai dai ba halin nuna wa, yanzun nan Hajiya Umma ta wanke sa.

Ɗan basarwa ya yi sannan ya kalli Hussaina ya ce "Husy yaushe za ki kawowa Matana ziyara?, ina kuke da ku  sau biyu kawai kuka taɓa zuwa gida na."

Kallonsa ta yi ta ce "sorry big broz za mu zo insha Allahu karatu ne ya sanyo mu gaba wallahi."

"Tau Allah ya taimaka" ya faɗa yana me miƙewa tsaye, sallama suka yi sannan ya fice daga cikin gidan.

Buɗe kulolin abincin Hajiya Umma ta sanya Hassana ta yi, sannan ta ce "ban yarda da abincin nan ba, don haka ɗauke sa ki ji ki bawa alamjirai shinkafar miyar ki zubar da ita a magudanar ruwa."

Jiki a sanyaye ta miƙe ta yi abinda aka sanya ta, ita kanta bata lamunta da abincin ba.

Kallon Hussaina Hajiya ta yi ta ce "ina Uwata ?".

"Yaya na shigowa ta fice".
Gyaɗa kai kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba.

Bayan ya koma gida ta ke tambayarsa "Hajiya ta ci abincin kuwa?."

Gudun fitinarta ya sanya shi ce mata "eh".

Murmushin gefen baki ta saki kana ta ce "okey", haɗi da nufar bedroom.

Shi ma miƙewa ya yi yabi bayanta jikinsa sai faman rawa yake yi.

Washe gari.

Allah Allah ta ke yi ta ji ankira sa a waya, amman har ya fice daga cikin gidan zuwa gurin aiki ba wani kira daya shigo cikin wayarsa.

Yana ficewa itama ta zari mayafi ta nufi gidan Hajiya Turai.

Yau kam duk wanda ya ganshi ya san yana cikin annushuwa kasan cewar fuskarsa a sake ba kamar kwanakin da suka shuɗe ba.

Yana tashi daga gurin aiki kai tsaye gida ya nufanto ransa wasai da shi, har matsuwa ya yi ya ganshi a gidan.

Sai dai me?

Tun a parking space ya fahimci babu mota ɗaya, ransa ne ya yi masifar ɓaci , kifar da kansa ya yi a saman sitiyarin motar yana mai furzar da iska a bakinsa.

Ya jima a gurin kana ya ɓalle murfin motar ya fice daga ciki.

A Parlour ya zube yana mai ƙara jin tsantsar tsanar halayen ZULFA'U a karo na farko da ya fara daya sanin bijirewa maganar iyayensa.

"Tabbas sai yanzu na ƙara tabbar da karin maganar nan ta malam ba haushe da yake cewa "ABINDA BABBA YA HANGO YARO KOYA HAU TSAUNI BAZAI GANSHI BA" ya faɗa a bayyane yana mai ƙara miƙewa a saman kujera.

Har wuraren ƙarfe tara na dare(9pm) ba ita ba labarinta, zuwa wannan lokacin ya daina mamakin abin har ya zo yana bashi tsoro "kar dai ace 'yar mutane wani abu ne ya same ta", ya faɗa yana mai firi-firi da idanuwa.

Wayarsa ya fiddo ya lalubo numbar wayarta ya danna mata calling sai dai harta tsinke ba ta ɗaga ba.

Sosai hankalinsa ya ƙara tashi, yana mai cigaba da danna wa wayar calling.
Haka ta yi ta ringing ba a ɗaga ba.

A dai dai wannan lokacin kuwa suna can suna faman cashewa a tsakiyar maza, sosai take juya mazaunai cikin wata yar figegiyar riga wacce iya kacinta cibi, sai wando data sanya fensir wanda ya kai har kan ƙafafuwanta.

Gashin kanta wanda yake a kwance ko yaushe sai faman reto yake yi.

Gaba ɗaya bata ji bata gani a wannan lokacin, cashewa kawai take yi.

Yayin da Hajiya Turai ke zaune gefe sai faman kwankwaɗar Win take yi lokaci-lokaci tana sakin wani murmushi wanda na rasa gane na miye.

Ratsowa ya fara yi ta cikin mutanen dake tsaye suna faman yi mata liƙin kuɗi yayin da wadansu suke ta faman ɗaukan video a wayoyinsu.

Jin an riƙo hannunta ya sanyata saurin kallon wanda ya riƙe ta.

Saurin shigewa jikinsa ta yi tana mai sauke nishin gajiya.

Glass cup ɗin da ake miƙo mata ya sanya hannu ya ƙarɓa kana ya aza mata shi a saman bakinta.

Sha ta yi sosai kamin ta yi gefe da kanta.
Miƙa wa wanda ya miƙo masa cup ɗin ya yi sannan ya sangame ta suka fice daga filin....

Za mu ci gaba a gobe...


'YAR MUTAN BUBARE.