Ɗan majalisa ya baiwa Gwamnan Sakkwato wa’adin Sati biyu ya bayyana yawan kuɗin ƙananan hukukomi da ya karɓa

Ɗan majalisa ya baiwa Gwamnan Sakkwato wa’adin Sati biyu ya bayyana yawan kuɗin ƙananan hukukomi da ya karɓa

Ɗan majalisar waƙillai dake waƙiltar kananan hukumomin Gudu da Tangaza Honarabul Sani Yakubu ya baiwa gwamnan Sakkwato Dakta Ahmad Aliyu wa’adin sati biyu domin ya bayyana yawan kuɗin ƙananan  hukumomi da ya karɓa a hannun gwamnatin tarayya.

Honarabul Sani Yakubu ya faɗi hakan ne a wurin taron baiwa ɗalibai takardar samun gurabun karatu a Indiya wanda Sanata Ibrahim Lamiɗo ya ɗauki nauyin yara 100.

Ya ce kuɗin da ƙaramar hukumar Sabon Birni ta samu kaɗai ya isa a ɗauki nauyin karatun yara matasa 'yan asalin Sakkwato zuwa ƙasar waje amma ba wani abin a zo a gani da aka yi.

Sani Yakubu ya ga laifin jagororin gwamnatin Sakkwato yadda suka tura ɗiyansu karatu a ƙasar waje irin su Ingila amma suka kyale 'ya'yan talakawa ba su samu irin wannan gatan ba.

Ɗan majalisar ya godewa Sanata Lamiɗo kan kokarin da yake yi wajen ganin ya kyautatawa al'ummarsa da yake wakilci.