Gwamna Dauda Ya Fadi Halin da Turji da Yan Bindiga Ke Ciki bayan Kisan Halilu Buzu

Gwamna Dauda Ya Fadi Halin da Turji da Yan Bindiga Ke Ciki bayan Kisan Halilu Buzu

Gwamna Dauda Lawal Dare na jihar Zamfara ya nuna farin cikinsa game da kisan Halilu Sabubu. Gwamnan ya yabawa jami'an tsaro game da kokarin da suka yi na kawo karshen kasurgumin dan bindiga. 

Dauda Lawal ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a jiya Litinin 16 ga watan Satumbar 2024.
Gwamna Dauda Lawal ya ce yanzu haka Bello Turji da sauran yan ta'adda sun rikice bayan kisan Sabubu. Ya ce duk sauran yan ta'addan ba su da jajaircewa kamar yadda Sabubu ya ke da shi. 
"Ina daga cikin wadanda suka fi farin ciki game da halin da ake ciki a Zamfara kan ta'addanci." 
"Kamar yadda ka sani Sabubu na daga cikin hatsabiban yan ta'adda da ke addabar al'umma musamman a Arewacin Najeriya." "Abin ya sauya yanzu saboda mabiya Sabubu ba su da kwarin guiwa kamarsa, a yanzu haka duk sun rikice ciki har da Turji." - Gwamna Dauda Lawal Dare Gwmanan ya ce kisan Sabubu ya kawo kwanciyar hankali a Zamfara da makwabtanta.