Yakin neman zabe: Tinubu, Shettima, da gwamnoni 5 sun yiwa jihar Borno tsinke

Yakin neman zabe: Tinubu, Shettima, da gwamnoni 5 sun yiwa jihar Borno tsinke
 
Daga Muhammad Maitela, Maiduguri.
 
Dan takarar Shugaban kasa a jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu tare da mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima da gwamnoni biyar sun yiwa birnin Maiduguri ta jihar Borno tsinke domin gudanar da yakin neman zaben shugaban kasa.
 
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, hadi da takwarorinsa na jihohin Yobe da Gombe, hadi da jiga-jigan gwamnatin jihar Borno, sune suka yiwa tawagar dan takarar da kusoshin jam'iyyar APC maraba zuwa jihar da ranar yau Asabar.
 
Jim kadan da saukarsa a Maiduguri, Tinubu da jiga-jigan jam'iyyar APC suka shiga tattaunawa ta musamman ds masu ruwa da tsaki a babban dakin taro na Multi-Purpose Hall dake gidan gwamnatin jihar a Maiduguri, kafin zuwa filin da za a gudanar da gangamin yakin neman zaben.
 
Bugu da kari kuma, tawar yakin neman zaben ta kai ziyarar ban-girma a Fadar Mai Martaba Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai, kafin zuwa filin wasa na El-kanemi Warriors wajen da za a yi taron gangamin. 
 
Gwamnonin da suka halarci gangamin yakin neman zaben sun hada da Mai Mala Buni na jihar Yobe, Dr. Abdullahi Ganduje na jihar Kano, sai Inuwa Yahaya, jihar Gombe, tare da Engr. Abdullahi Sule na jihar Nasarawa.
 
Al'ummar jihar Borno sun yiwa manyan bakin gagarumar tarba, yayin da jama'a ne make gani ta kowane bangare sun yi dafifi kan tatin da ya shiga zuwa Fadar Shehun Borno tare da daga wa tawagar manyan bakin hannu, a sa'ilin da mawaki Rarara yake rera wakokin siyasa.