ƘADDARA TA: Fita Ta Bakwai
ƘADDARA TA
Na
*Jiddah S Mapi*
*Chapter 7*
~Jikin kaseem yana rawa yace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un me yake faruwa?"
hameed ma jikinshi rawa yake sai kallonsu yake ya kasa yin komai, minat kallon Amnah tayi yadda ta bushe a tsaye, da sauri taje ta riketa cikin tashin hankali tace "kija numfashi amnah"
girgiza kai tayi alaman ba zata iya ba, tace "Amnah kija numfashi"
girgiza kai kawai take ta kasa magana, meenat da karfi tace "ya kaseem Amnah fa bata numfashi"
da sauri yazo ya riketa, wani irin rikeshi tayi ta kwala ihun daya amsa gidan gaba ɗaya, mai martaba wanda ya shigo yanzu ya zuba musu ido ya kasa cewa komai sai zufa da yake, Amnah da Ammi ihu kawai suke meenat tana tayasu, cikin kuka tace "Amrah meya kawomu? Amrah tarefa mukazo meyasa zaki tafi ki barni?"
hameed ɗaga Aneeta dake kwance yayi ya ɗaurata akan sofa, ruwa ya ɗibo ya watsa mata, da sauri ta buɗe ido tana kallon shi, kallon Amrah dake kwance tayi sai kuma ta rungumeshi tana kuka tace "wa yayi haka? waye ya kashe ta ranan aurenmu ayi kisa hameed? hameed na fara tsorata da wannan gidan wallahi akwai wani abinda yake faruwa"
mai martaba ne yayi karfin halin yin magana yace "ayi jana'iza kada a ɓata lokaci"
kaseem yace "Abi a bari ayi bincike"
Ammi dake kuka idonta ya jika da hawaye tace "kaseem a birneta babu wani bincike da za'ayi a bari sai an birneta komai ma za'ayi sai ayi daga baya"
yace "sabida bakiso a gano wanda ya kasheta?"
da mamaki ta kalleshi sai kuma ta share hawayen tace "banaso kuma? me kake nufi kaseem?"
murmushin gefen baki yayi yace "ai kinfi kowa sanin me nake nufi..."
a fusace ta mike tana kallonshi da tsananin ɓacin rai akan fuskanta tace "me kake nufi kaseem? kana zargin zan iya kashe ƴar kanwata? ko kana nufin zan bada goyon baya a kasheta?"
shima yana huci yace "to meyasa zaki hana?"
cikin raɗaɗin mutuwan Amrah da haushin maganan da yakeyi tace "sabida nice na saba kisa? ko ka manta kaine...."
mai martaba a tsawace yace "ya isa haka!!! nace ya isa haka!!! wai meyasa kullum ba zaku faɗi alkhairi bane? meyasa kullum cikin zargin juna kuke? maimakon ku maida hankali akan mutuwan da akayi ayi bincike me kyau domin a hukunta wanda yayi amma kuna wannan banzan maganan mara am....."
rike kirjinshi yayi yana salati jin wani zafi da kirjinshi yake, idonshi ya rufe kasa ya faɗi da mugun gudu hameed yazo ya rikeshi, kallon kaseem dake tsaye yayi ya kalli jakadiya sannan ya nuna mata kofa alaman ta buɗe mutane su fita, da sauri tace "to yarima"
zuwa tayi ta buɗe kofan mutane suka fara fita, saida ya tabbatar mai martaba ya farfaɗo kafin hankalinshi ya ɗan kwanta.
har aka fita da Amrah kanwarta Amnah bata cikin hayyacinta, gidan ya zama shiru babu me magana, amnah tana zaune a gefen meenat da ammi tayi tagumi har hawayenta sun tsaya yanzu sai kukan zuci take, Aneeta kuma tunda ta faɗa zazzaɓi ya kamata tana ɗaki kwance, kaseem ne ya shigo sanye da jallabiya yayi shirin kwanciya amma yace bari ya dubasu, da sallama ya shiga sannan ya zauna a kusa dasu yace "sannu Amnah"
a hankali tace "yawwa yaya"
yayi shiru har na ɗan lokaci, cikin nutsuwanshi yace "dama akwai wanda suke gaba ne?"
girgiza kai tayi sannan cikin muryanta daya dishe tace "ko ɗaya Amrah batada abokin gaba, maganan bakinta ma baida yawa kaima ka sani, bata fiye shiga harkan kowa ba..."
kuka ta kara fashewa dashi, yace "kiyi hakuri na san zafin da kikeji Amnah kiyi hakuri kuma na miki alkwari saina samo wanda ya aikata wannan mummunan abin"
yayi magana yana kallon ammi, itama kallonshi tayi, tun daga kasa suke jiyo karan buga kofa, sunan Amnah ake kira babu kakkautawa, Amnah dake zaune tashi tayi farat tace "Dady ne"
tare suka fita yana tsaye sanye da babban riga da alama daga tafiya ya dawo hulanshi ya cire ya wurgar jijiyoyin kanshi sun tashi, hameed dake ɗakin Abi yana bashi malt yaji hayaniya da sauri ya kalli Abi sannan ya kalli kofa, tashi yayi ya fita Abi yabi bayanshi, Aneeta dake zaune akan stool tana kallon kanta a madubi taji hayaniya murmushi tayi ta shafa fuskanta da yayi jajur sabida kukan karya da tayi, rigan bacci ne a jikinta milk color ya bala'in karɓan jikinta, murmushi tayi tace "haka nakeson ji, ko kaɗan banason ganin gidannan babu tashin hankali, ko kaɗan banaso naga ana zaman lafiya a wannan gidan, idan ana hayaniya da tashin hankali ji nake kamar na zuba ruwa a kasa nash"
tashi tayi tana kallon jikinta da kayan baccin ya matukar karɓanta, hijabi tasa dogo har kasa sannan tace "bara naje naga me yake faruwa"
fita tayi ta maida fuskanta kalan tausayi, tana ciza baki kamar mara lafiyan gaske, dadyn Amnah cikin tsananin fushi yaje yaja hanunta yace "ko kwana ɗaya ba zaki kara a wannan gidan ba, saida na faɗa muku keda Amrah wannan ba gidan zuwa bane, na faɗa muku har mahaifiyarku ta mutu bata magana da wannan matar duk da uwa ɗaya uba ɗaya suke amma kunki jina, saida kuka zo Amnah gashi yanzu sun kashe ƴar uwarki"
Ammi tace "amma salisu daka bari ta kwana idan yaso zuwa gobe...."
cikin masifa da zafin mutuwar ƴarshi yace "gobe? gobe fa kikace, to nasan me zai faru da ita da darennan idan ta kwana? wannan gidan naku da yake ɗauke da mummunan tarihi an gaya miki ban san komai bane? kuma wallahi ku sani ƴata ba zata mutu a banza ba, na rantse da Allah saina ɗau fansa, ke kuma....."
ya nuna ammi jikinshi har yana rawa, Abi wanda ya gama cika yace "an gaya mata itace tayi kisan da zaka zo kana gaya mata bakaken maganganu?"
ya kalli Abi da idanunsa da sukayi jajur yace "a cikin gidannan waye baya kisa?"
kaseem wanda shima ranshi ya gama ɓaci yace "ka daina yi mana kuɗin goro ai laifin wani ba zai shafi wani ba"
jan hanun Amnah dake kuka yayi yace "muje babu ke babu su daga yau ba zasu sake ganinki ba kema kin rabu dasu"
meenat tana kuka tace "dady dan Allah kada kayi haka dan Allah ka barta mu zauna tare, ka barta mu ɗibe mata kewan ƴar uwarta data mutu, dady yanzu haka Allah ne kaɗai yasan zafin da Amnah take ji dady kada kayi haka"
yace "meenat na gommace Amnah ta mutu yau a gidana sabida zafin mutuwan Amrah data kwana a wannan ƙazamin gidan naku"
fita yayi da ita tana tirjewa tana cewa "dady ka bari na kwana anan"
suna fita kaseem ya kalli ammi dake rusa kuka yana huci yace "mutum ɗaya ba zai ɓata mana suna ba nasan wanda yayi wannan kisan"
Aneeta saida jinta da ganinta suka ɗauke na lokaci, yana kallon Ammi yace "kema kin sani hakeem ne zai iya wannan mummunan kisan..."
tace "ya isheka kaseem ya isheka nace"
jikinshi yana rawa yace "meyasa zaki danne gaskiya? meyasa zaki ɓoye abinda yake a bayyane? hakeem shine ya kashe Amrah"
marin data ɗaukeshi dashi yasa yayi shiru yana kallonta hanunshi dafe da kuncinshi, ta nunashi da yatsa tace "inaso ka san nice na haifeka kaseem ba kai ka haifeni ba, kaseem zan iya yin komai idan ka kara sa sunan hakeem a cikin abinda yake faruwa a gidannan"
murmushin da yafi kuka ciwo yayi sannan yace "okay kina nufin hakeem baida laifi?"
tace "hakeem baida laifi kuma ko za'a kasheni ba zan taɓa yadda cewar yanada laifi ba"
yace "to waye me laifi?"
hameed dake tsaye ta nuna tace "hameed shine babban me laifi, yarima hameed shine da laifi ba yarima hakeem ba"
hameed dake tsaye ya kalleta da manyan idanunshi a hankali ya fara yin baya jin abinda ta faɗa, Aneeta dake tsaye ta kasa karasowa ta zuba mishi ido tana gani jikinshi yana rawa, showglass dake cike da turare ya buɗe, kwalban turare ya ɗauka sannan ya fasa, aneeta tana tsaye tana kallonshi murmushi take a ranta tana kallo yadda kwalban yayi tsini, ganin hankalinsu baya kanshi sunata faɗa tsakaninsu yasa itama bata ankarar dasu ba domin so take taga gawanshi kwance baya motsi hakan zaisa taji ranta yayi sanyi hakan zaisa ta yafewa kanta, daɓa kwalban yayi a cikinshi, tana kallonshi har ya faɗi kasa jini ya fara bin tiles, sai a lokacin tayi wani irin ihu tareda kiran sunanshi ammi da kaseem waɗanda suka kai karshe wajen fushi suka juyo a tare suna kallon hameed dake kwance hanunshi akan cikinshi jini ya ɓata inda yake kwance idonshi a rufe da alama ya mutu.
Meenat hanu ta ɗora a kanta tana ihu, kaseem da sultan da kuma fadeel tare sukaje suka ɗaukashi jikin kaseem yana rawa yama rasa wani taimako zai iya mishi kawai yace "mu tafi hospital"
tare suka fita dashi a hanunsu Aneeta da meenat suka bisu a baya, ammi itama binsu tayi, a mota ɗaya babba suka tafi asibiti a cikin daren da yayi nisa basu sani ba, babu mutane dayawa akan titin sabida dare yayi sosai ba kaɗan ba, banda kuka babu abinda aneeta take yi, tana cewa "dan Allah kada ka mutu ka barni hameed dan Allah ka buɗe idonka kada ka mutu ka bar marainiyar matarka"
a hankali meenat ta rungumeta tana bubbuga bayanta tareda kwantar mata da hankali, shiru tayi a ranta tace "inama ace ya mutu, inama ace da gawanshi muke tafiya"
suna shiga asibiti kaseem ya fito babu takalmi a ƙafarshi ya ɗaukeshi, shiga ciki yayi dashi duk masu aikin night sukayo kanshi suna bashi taimakon gaggawa, jikin kaseem banda rawa babu abinda yake yi, gani yake hameed ya riga ya mutu tun kafin suzo asibitin, zama yayi akan dakali ya rike kanshi da hanunshi, kukan da bai shirya ba ya fashe dashi, sultan dake safa da marwa ya kasa zaune ya kasa tsaye yazo ya durkusa a gabanshi, rungumeshi yayi yana bashi hakuri yayi shiru.
Aneeta a bakin kofan ta tsaya kamar zata shiga kofan da aka rufe tana kuka tana addu'a, Ammi kam tsaban tashin hankali bin kowa kawai take da kallo kamar kanta ya taɓu.
Aneeta cikin ranta tana addu'a tace "Allah kasa ya mutu ya rabbi kasa baya raye"
a fili kuma cewa tace "Allah kada kasa hameed ya mutu ya barni dana sani da banyi wannan auren ba matukar zai kawo tashin hankali"
Ammi da jikinta ya gana sanyi tace "saida nace kada ayi wannan auren nasan babu mu babu kwanciyan hankali matukar hameed ya samu yarima kuma yayi aure amma sunki jina, kowa baya jin maganata"
kuka take yi sosai, bayan lokaci dayawa suka buɗe kofan, har rige rige suke wajen tambaya ammi tace "ya mutu?"
da mamaki dr ya kalleta yace "kinaso ya mutu ne?"
shiru tayi, ya kallesu su duka sannan yace "yana raye bai mutu ba amma yaji mummunan rauni"
hamdala kaseem yayi sannan ya ɗago kai ya share hawayen, farin ciki ya bayyana a fuskanshi yace "Alhmdllh hameed bai mutu ba"
shiga dakin yayi hameed yana kwance akan gadon hanunshi ɗauke da jini sun san jininshi kuma ya zubar da jini sosai, fuskanshi yayi fayau sosai, a hankali ya zauna a gefenshi ya rike hanunshi dake free, murza yatsunshi yake hawaye suna wanke mishi fuska yace "hameed kayi hakuri ka yafemin ban zama yaya na gari ba na zama yaya mara amfani a wajenka, kullum cikin ciwo kake baka taɓa samun kwanciyar hankali koda na kwana ɗaya bane"
shafa kanshi yayi yace "ka yafeni hameed"
shigowa sukayi aneeta ta tsaya a bakin kofan tayi shiru, kallonta kaseem yayi sai yaji ta bashi tausayi, yace "aneeta zoki zauna kusa da mijinki"
cikin jin kunya ta sunkuyar da kanta, tashi yayi yace "kizo"
a hankali tazo ta zauna kusa dashi, shiru tayi, kaseem yace "zaku iya tafiya gida idan yaso gobe saiku dawo zamu kwana da aneeta anan tare dashi"
duk sukayi shiru basason tafiya, yayi kamar bai taɓa dariya ba yace "kuje mana"
tashi sukayi ba dan sun so ba harda Ammi suka fita, kallon Aneeta yayi yace "kiyi hakuri da duk abinda yake faruwa sannan ki kula da mijinki ko sau ɗaya banaso ki tambayeshi abinda yake faruwa a wannan gidan, ko su meenat dasu sultan banso ki tambayi kowa, kici gaba da zama mutuniyar kirki kamar yadda kike"
a hankali tace "to ya kaseem insha Allah"
shiru yayi yana kallon hameed dake bacci, ya tashi yace "zanje office ina zuwa"
tace "to"
fita yayi, ta kalli hameed a ranta tace "meyasa baka mutu ba? nace me yasa baka mutu ba hameed?"
ta kalli jinin dake tafiya a jikinshi, fizge canulla ɗin hanunshi tayi ta bar jinin baya tafiya, murmushi tayi tace "ko kaɗan banso naga kana rayuwan farin ciki, so nake naga kullum kana kuka hameed, na tsaneka na tsani ƴan gudanku hameed na tsaneku"
rashin jinin dake jikinshi yasa jikinshi ya fara zafi, fizgewa ya fara yana neman karya gadon, tana ganin yadda yake jin zafin ciwon a jikinshi da yadda yake fizge jikinshi sabida rashin jini, tace "ka mutu hameed ka mutu mana hameed"
knocking akayi da sauri ta fara rike hanunshi tace "shigo"
ya kaseem ne ya shigo da juice a hanu, ya kalleta ya kalli hameed wurgar da juice ɗin yayi yazo yana rikeshi, yace "ya akayi jinin ya fita?"
tace "wallahi fizge fizge ya fara kuma na rasa yadda zan yi"
ganin tana kuka yace "karki damu babu abinda zai sameshi"
gyara mishi jinin yayi yana jin jini a jikinshi ya koma luf ya kwanta akan cinyarta.
shiru tayi tana kallonshi, juice ɗin kaseem ya mika mata yace "gashi kisha nasan rabonki da abinci tun safe"
girgiza kai tayi tace "bana jin yunwa, ba zan iya cin komai ba"
yace "ki daure kisha dan Allah"
shiru tayi tana girgiza kai hawaye yana wanke mata fuska, da kyar ya lallaɓata tasha kaɗan, a wajen tana zaune bacci ya ɗauketa.
_jiddah ce...
08144818849
managarciya