Gare Ku Mata:Matakan Farko Da Mace Za Ta Yi Don Samun Nasarar Aurenta

Gare Ku Mata:Matakan Farko Da Mace Za Ta Yi Don Samun Nasarar Aurenta

MOMMYN MUS'AB   CLASSIC FOOD
                 & 
  GYARAN JIKI
 
SPECIAL GROUP TRAINING 
 
 
*GARE KU YAN MATA*
 
Assalamu Alaikum, barka da warahaka kaman yadda na fada muku za mu fara rubutunmu namu da alokacin da mace  take budurwa   take tashenta kaman shekarru 15, zuwa  sama. 
 
Tau awannan lokacin za mu yi magana yadda ake neman aure, amatsayinki na budurwa,yadda za'a fara neman aurenki 
 
Yadda ake neman aure:
 
Amatsayinki na yarinya budurwa ,maijin tashen budurcu,mai ilimi na addini dana zamani, gidanku anbaki tarbiyya wadattace, da za ta sa ki kare mutuncinki har zuwa gidan mijinki. 
 
A wani lokaci kina tafiya sai ki ka ji ana kiranki ana  "ji mana" ke kuma kin share kin cigaba da tafiyarki, wani zai sha gabanki  ya ce haba malama ya ina miki magana kin share ni , abu daya kawai za ki ce masa in yana son ki yaje gidanku ku yi magana ba a hanya ba,
 
In da gaske yake yi zai zo, a lokacin da ya zo gidanku ki ce ya samu iyayenki, saboda su su ke da hakki aurar dake ga mijinki kasancewarki budurwa saboda za ki iya tsayuwa da shi kufara soyyayya baki san ko iyauenki akwai wanda za su zabar miki ba.
 
In iyayenki sun bashi dama shikenan idan kuma ba a ba a shi ba dama bai zo ya yi miki ƙarya ki ka shaƙaba.  .
 
To idan an ba shi dama ya zo ya za ki yi????
 
To idan an ba shi dama ya zo ya ganki anan ne gyale zai yi aiki, anane riga mai bress cove za ta yi aiki, anan ne scart zai yi aiki,
 
Ki yi wankanki ki yi simple make up kisha rigarki da scart ki yafa gyale kitaho kina taku 
.dalilin da ya sa aka ce kisa kaya me nuna surarki saboda yasan mi zai aura Alokacin kam yana da daman da zai kare miki kallo.
 
To wani kallan hira za ku yi????  
 
Amatsayinki na budurwa akwai kalan hirar da za ki yi da saurayi a zuwan shi na farko  abubuwan  su ne:
 
1️⃣Ya gabatar miki da kansa 
 
In ma yana da mata 'ya'yansa nawa, kuma da mi ya miki bayani, sannan ya fada miki sana'arsa da dai sauransu. 
 
2️⃣Abubuwan da yake so 
Kama  daga hallayar matar da yake so ya aura ,abincin da ya fi so, kalan da ya fi so ,da dai sauransu
 
3️⃣ Sannan sai ya gabatar miki da soyayyarsa .
 
 
Lokacin daya gama ke ma zaki yi kaman yadda ya yi 
 
1️⃣ Kigabatar da kanki 
 
In ma ke bazawara ce ko budurwa in ma tsautsayi ya taba fada miki kaman fyade duk ki fada masa  kar ki boye masa. 
 
 
 
2️⃣Abubuwan da kike so da wanda bakyaso in ma bakyason kishiya ne, in ma bakyason ku zauna wuri daya, kama daga abubuwan da suke burge ki a gun namiji duk ki fada. 
 
3️⃣ Sannan. Kafun ki amshi soyyarsa ki bari sai kin yi tunanin abubuwa kamar haka: 
1.Dawane siga Ya bayyana  miki  soyayyarsa akwai  Soyayyarki a maganarsa 
 
2.Kin san maganar mai ilimi daban take, to amaganarsa da kwai ilimi ko dai jahili ne 
 
3.Yanayin wadatarsa, ba wai nace sai yana da kudi ba ina nufin yana da sana'ar yi, zai iya ciyar da ke ya shayar da ke ya biya miki dukkan hakkokin ki na rayuwa da Allah ya daura masa, daidai gwargwadon halinsa. 
 
4.Adiininsa alokacin da kika shirya zabansa ya zamo abokin rayuwarki na har abada, dole ki duba addininsa saboda matukar bai da addini zai shagaltar da ke daga bautawa ubangijinki, sannan kar mu manta, Allah madaukakin sarki bai aminta ba, a neman yardan halitta cikin sabbawa mahalicci, kuma Allah da manzonsa su suka fi cancanta a yarda da su in mun kasance muminnai. .
 
Idan kin auri jahilin miji na farko ba zai barki ki gabatar da ibada ba, 
Sannan ba zai nunawa 'ya'yanki zuwa masallaci da sauran ibadu ba. 
5.'Yan uwansa, matikar  ba sa sonki a gaskiya ki fasa aurensa  saboda za ki yi zama ne na Ƙunci. 
 
6. Ki sanar da shi amincewarki idan kina da sharudda ki sanar. 
7.  Ki fada masa kaman yadda zai rika  zuwa hira da lokacin
 
Sannan daga wannan lokacin in zai zo ki rika saka hijabi babba saboda ya yi shaawar sake kallon wannan surar taki a lokacin da ya zama halal gare ki.
 
A rubutunmu na gaba za mu yi magana kan abubuwan da budurwa za ta yi a rayuwarta kafun dakin miji.
 
Share fissabillillah 
Mommyn Mus'ab
 
07041105956
 
Share✅
Edit❌
Comment✅
Mun gode.