DUHU DA HASKE: Fita Ta 22
DUHU DA HASK
Na
*Jiddah S mapi*
*Chapter 22*
~Murmushi tayi tace "ba zan kara dawowa nan ba sai ranan da za'a shiga kotu, fahad ne zai rinƙa kawo maka abinci"
zaunar dashi tayi sannan itama ta zauna tasa hanu ta shafa gashinshi tace "Imran be strong"
gyaɗa kai yayi, ɗaukan flask da goran tayi sannan tace "na tafi"
ta juya zata tafi taji ya rike hanunta, jikinta yayi sanyi bata juyo ba tace "me kuma Imran? karka karyamin zuciya dayawa, yadda na ganka ma kaɗai zuciyata ta karye"
a hankali yace "na gode kinyi kokari a rayuwarmu, ko shi ya man ɗin ya samu jin daɗin da yake ciki ne ta dalilinki, na gode Ameesha"
murmushi tayi ta juyo ta durkusa kusa dashi tace "Imran babu godiya tsakanin yaya da kani, kai kanina ne kamar fahad kake a wajena duk abinda zanwa fahad shi zanyi maka kaji?"
gyaɗa kai yayi, a hankali tayi mishi kiss a gefen kumatu, kallonta yayi ta nuna mishi gefen kumatunta tace "oya"
kiss yayi mata tace "good boy, gaba ɗaya ka kara girma kana fita anan zamu nema maka budurwa kayi aure"
rufe fuska yayi alaman kunya, tace "to yaushe kuma muka fara haka?"
kin buɗe fuska yayi tace "nikam na tafi wannan halin daka aro bada niba"
tashi tayi ta fita zuciyanta a karye harta isa gida, fahad ta gani rike da waya a hanunshi yana game, da sauri tace "kai waya baka waya?"
yace "na yaya yazeed ne"
da mamaki ta kalleshi yana kallo bai ko kalli inda take ba, a ranta tace "to haka yake ne ko kuma ni ɗin akwai laifin dana mishi?"
sum sum ta bar wajen ta tafi ɗakinsu da hanan, cire hijabin tayi ta faɗa kan gadon tace "oh my god na gaji"
hanan dake sa kayan Dr akan leshin dake jikinta blue black ɗinkin fited gown, tayi kyau sosai, telescope tasa a wuyanta sannan tace "sis nifa zan wuce hospital inada patient akwai operation ni kaɗai ake jira"
tace "okay Allah ya bada sa'a"
tace "ameen darling ki kula da yaya yazeed please kinga baison yunwa baison zama da yunwa ko kaɗan, idan ba kin ganeshi ba bazaki gane ba, yanada mugun miskilanci ko yunwa yake ji sai yayi shiru har sai an bashi abinci, sannan kin san tunda momynmu ta rasu baya kula kowa sai Abba sai kuma ni, yanada matukar wuyan sha'ani dan Allah kiyi hakuri dashi kinji?"
tashi tayi daga kwancen da take ta zauna tana kallon hanan wacce duk ta zama wani kala saboda maganan tace "haba hanan ko me zaimin ai ya cancanci yamin, taimakon da gidanku sukamin sunfi karfin komai a wajena, ku kura gyaramin rayuwata kuka sa na zama mutum, kodan Abba wanda baya ganin banbanci tsakanina dake yaci ace nayi muku komai"
tace "ki daina faɗan haka Allah ne yayi hakan ba muba"
tace "kwarai Allah ne amma ai da sanadi, koma dai menene kije kada kiyi late"
tace "to sis bye"
makullin motarta ta ɗauka sannan ta fita da gudu, stair ɗinma da gudu ta sauka, kallonsu tayi shida fahad suna game tace "yaya na tafi"
yace "saikin dawo"
da Abba sukayi karo da sauri ta durkusa kasa tace "sannu Abba"
yace "mamana asibiti ne haka da gudu?"
murmushi tayi tace "eh Abba"
yace "to abi a hankali"
tace "to Abba"
da gudu ta fita tana danna remote na motan, shiga tayi ta fita sai asibiti.
Abba ya kalli yazeed yace "ya akayi ɗan albarka?"
tashi yayi ya zauna yace "lafiya lau Abba"
yace "fahad ya kake?"
yace "lafiya ƙalau Abba"
yace "ina ameesha?"
"tana ciki"
Abba ya kalli agogo yace "kirata"
tashi yayi da sauri ya nufi ɗakinsu, knocking yayi kafin yayi sallama, da sauri ta share hawaye ta maida fuskanta kamar ba komai tace "yes shigo"
shigowa yayi yace "Anty ameesha Abba yace a kiraki"
da sauri ta tashi tana ɗauko mayafi, tace "muje"
tana ganin Abba taje ta durkusa kasa kusa da kafanshi tace "Abba ina kwana"
ya kalleta yadda take birgeshi shine tana bashi respect sosai, yace "ya kike?"
a hankali tace "lafiya ƙalau"
kanta a kasa take maganan, yace "mahaifiyarki data ɓata ameesha ya zamuyi da nemanta na faɗawa gidajen rediyo ne da gidajen tv?"
hawaye ya fara bin fuskanta tana sharewa tace "Abba ina cikin damuwa"
ganin tana kuka yace "my daughter you are very strong bai kamata ki zama weak ba"
kukan da take rikewa ta fashe dashi, kanta ta ɗaura akan kafar Abba tana rusa kuka, shiru Abba yayi yana ɗan tapping bayanta alaman tayi hakuri ta daina kuka, yazeed dake zaune yayi shiru yana kallonta, yadda ta rike Abba tana kuka zaka san tana cikin damuwa, Abba yace "tashi"
tashi tayi ya nuna mata gefenshi yace "zauna anan"
zama tayi yace "share hawayen"
share hawaye tayi yace "tabbas nasan kina cikin damuwa amma Inaso ki nutsu a yadda nasan labarinki keba raguwa bace, rashin mahaifiya zai iya saki a cikin wani hali amma Inaso ki sani anyi hakan ne sabida a ɗauke hankalinki daga case ɗin Imran, yanzu ke lawyer ce kula da wannan case ɗin yana hanunki kuma kinyi alkawari zaki kare me gaskiya, idan har kin gama wannan case ɗin tareda Imran damu zamu nemi inda take, karki zama raguwa kinji?"
gyaɗa kai tayi tace "insha Allah Abba"
yace "Allah miki albarka"
a hankali tace "ameen"
kallon agogo yayi yace "naso na miki surprise amma naga kina cikin damuwa gara na faɗa miki, momynku tana hanya yanzu jirginsu ya kusa landing"
da sauri ta waro idonta dake jiƙe da hawaye tace "really?"
yace "yes"
rungumeshi tayi tace "yeee naji daɗi Abba"
yana son ganinta cikin murmushi, karan text yaji yana dubawa yace "sunzo yanzu tana airport muje tare muzo da ita ko? sabida sai tambayanki take tace ta kira wayarki baki ɗauka ba"
da sauri ta tashi ta haura sama da gudu domin canja kaya, wani fited gown na atamfa tasa sannan ta rike karamin mayafi tasa takalmi flat da wayarta a hanu a fito da gudu, ido yazeed ya zuba mata ganin yadda take gudu ga rigan ya kama jikinta duk taku ɗaya sai jikinta ya girgiza, da sauri ya ɗauke kai, tana zuwa tace "Abba let's go"
yace "gaskiya kinason momynku dayawa dake da hanan bansan waye yafi sonta ba"
murmushi tayi ta rike hanunshi tace "muje Abba"
Abba ya kalli yazeed yace "bari muje"
da mamakin Abba sai yaji yace "zan biku"
Abba yayi mamaki domin yazeed bayason damuwa bayason shiga mutane, baisan wacece ma momyn ba sabida rashin shiga harkan mutane, kallon Fahad yayi yace "muje"
da sauri fahad ya tashi ameesha tana gaba da Abba hanunta ta rike nashi, yazeed da fahad suna baya, motar Abba tsadadde black color suka shiga, yazeed yaki zama a gaba sabida yana hira da fahad, ita ameesha a gaba tana ta cika Abba da surutu, sai eh da a,a yake amsa mata da haka har suka isa airport, Abba yace "ku fito mana"
yayi maganan ganin ameesha ce kaɗai ta fito ta nufi wajen momy wacce tayi tsananin kyau cikin leshi me matukar tsada fari sal da mayafi fari, balarabiya ta fito kamar ka saceta ka gudu, murmushi tayi ganin ameesha tazo da gudu ta rungumeta tace "oyoyo momy"
cikin muryanta me zaƙi tace "oyoyo ameesha ta, nayi kewarki sosai ƴata"
cikin jin daɗi tace "nima nayi kewarki momy"
tace "ina hanan?"
tace "ta tafi hospital akwai operation"
tace "okay"
matsawa tayi domin Abba ya samu daman ganawa da matarshi, yazeed ya kalli fahad dake ɗauke kai yana kallon gefe, yace "fahad me yasa baka farin cikin ganinta? ka santa ne?"
girgiza kai yayi yace "no ban santa ba amma kawai naji bana santa, sai naji gabana ya faɗi ma dana ganta"
murmushi yayi yace "nima naji faɗuwan gaba dana ganta"
fahad yace "haka naji lokacin dana fara ganin manal"
ya kalleshi ganin hawaye ya cika mishi ido yana kokarin mayarwa kada ya gani, hanunshi ya rike yace "wacece manal?"
cikin hawayen yace "watace data shigo rayuwarmu ta tarwatsa duk wani farin cikinmu, tazo ta lalata komai ta ɓata komai, har yau bamu kara samun farin ciki ba"
shiru yayi yana ganin yadda yaron yake kuka yana share hawaye da bayan hanunshi, a hankali ya janyoshi jikinshi yace "stop crying"
cikin kuka yace "bazan iya daina kuka ba, itace tayi sanadin mutuwan umma, itace ta raba ya Abdool da anty ameesha ta karyawa aunty ameesha zuciya saida ta gudu ta bar garin, ta hanamu zaman lafiya"
shiru yayi yana kallon yaron, yana magana kana ganin ɓacin rai ƙarara a tare dashi, yazeed yace "kayi hakuri"
bai tambayeshi abinda ya faru ba sabida yaga kukan yayi yawa, buɗe kofan ameesha tayi ta zauna a kusa da fahad, momy ta zauna a gaba kusa da Abba, juyowa tayi tace "yazeed? Fahad? ya kuke?"
yazeed ciki ciki yace "fine welcome"
fahad kam bai amsa ba ya ɗauke kai, taɓashi ameesha ta fara ganin bai gaisheta ba tayi kasa da murya "zaka gaisheta ko saina ɓata maka rai?"
yazeed yana jinta, fahad a takaice yace "ina wuni, welcome"
murmushi tayi dan taga basuyi maraba da ita ba, da haka suka isa gida suka fito da jakanta a hanun ameesha suka shiga, ɗakin momy da Abba ya nuna mata ta kai kayan ta kalli ɗakin me kyau sosai, momy tana kallonta tana shirya mata kayanta a wardrobe ta kai mata ruwan wanka tace "momy kiyi wanka bari na kawo miki abinci"
momy tace "Allah miki albarka"
tace "ameen"
fita tayi ta jima kaɗan kafin ta shigo da abinci da juice ta aje mata a gaban gadon, momy tasa kaya mara nauyi ta zauna tana cin abincin, saida ta koshi tace "ameesha ya kuka karasa a kotu? ina fatan kunyi nasara?"
a hankali tace "a,a momy babu nasara kuma an sace mamana..."
tayi maganan tana so tayi kuka, momy ta dafa kirji tace "yaushe?"
kuka ta fashe dashi tana bata labari, momy ta jata jiki tana bata hakuri tace "kowa da irin kaddaran da Allah ya ƙaddara mishi ki karɓi ƙaddara hanu biyu watarana sai de ki bada labari kinji?"
a hankali tace "to momy, saura sati biyu mu koma kotu zakije kema ko? zakiga manal da nake ce miki kunyi kama sosai"
ɓata rai tayi tace "ki daina cewa nayi kama da ita ameesha, babu wacce za'ace ina kama da ita naji daɗi sai ke, dan Allah ki daina wannan maganan, na tsani wannan yarinyar manal, sam banson koda na ganta ne, ta cutar da hanan a lokacin da suke kanana sannan ta cutar da rayuwarki a lokacin da kuka girma, wace irin shaiɗaniya ce? wace irin mara albarka ce ita?"
a hankali tace "momy ki huta bari naje na cigaba da binciken da nake"
momy tace "Allah ya baki sa'a ya ɗauraki akanta yasa kifi karfinta duniya da lahira ƴata"
murmushi tai tace "ameen momy na gode"
fita tayi ta koma ɗakinsu ta ɗauko laptop da kuma wayarta ta fara dube dube tana cigaba da binciken, koda hanan ta dawo tayi farin ciki sosai ganin momy tazo itama zasu zauna tare anan.
*Two weeks later*
yau ake shirye shiryen shiga kotu domin karasa case ɗinsu manal da Imran, kamar koda yaushe tare suka zo a motarsu Abdool ne ya fito da ammi wacce tayi kyau cikin baƙin lifaya yana turata manal ta fito daga motan sanye da pink na leshi anyi mata ɗinkin daidai jikinta riga da skirt tasa wani arnen takalmi kamar zai karye tsaban tsayi, glass baƙi tasa a idonta kamar kullum sannan ta rike karamin mayafi jessy pink a hanunta, duk wanda ya kalleta a kotun saiya kara juyawa ya kalleta, tafiya take hanunta akan wayarta bata kallon kowa, man yayi kyau sosai cikin shadda ruwan kasa da hulanshi me kyau, takalmi me kyau sahu ciki yasa, sai kamshi suke, tsadadden mota ne yayi parking duk suka juyo suna kallonsu itama ta daina danna wayan ta juyo domin kallon waɗanda sukayi parking kusa da motarta, Ameesha ce ta fara sa kyakkyawan farin kafanta ɗaya zuwa waje, takalmi dogo ne baƙi a kafar hakan yasa farin fatarta ya kara fitowa, ɗayan ƙafan tasa zuwa waje sannan ta fito, masha Allah wani irin masifaffen kyau tayi cikin uniform nata na lawyer, ta kame gashinta da ribbon sannan tasa hulan ta bar kasan gashin a waje har gadon bayanta ya bayyana da kitso ɗaya data yiwa gashin, fuskanta babu walwala kamar bata taɓa dariya ba, hanunta rike da wasu takaddu da waya a ɗayan hanun, bakin glass tasa a idonta, hanan ce ta fito itama tayi masifan kyau cikin baƙin kaya da wayarta da jaka a hanu, Abba ma ya fito sanye da tsadadden shadda fari kat da hula fari, fahad ya fito sanye da shadda dark blue yayi kyau sosai haskenshi ya dawo ya zama fari sol amma har yanzu a rame yake, yazeed wanda yake waya ya fito rike da wayan a hanunshi shima yasa farin shadda yayi kyau sosai, momy wacce take cikin motan ta kalli manal wacce take latsa waya, ko basu faɗa mata ba ta gane wannan itace manal, ido ta zuba mata, Abba yace "driver ka maidata gida tunda tace ba zata iya zama ba kanta na ciwo"
driver yace "to Alhaji"
hanun hanan ta rike sannan suka jera a tare suna tafiya, ɗauke kai manal tayi ganin sunzo dab da ita, wucewa ameesha tayi ko kallon inda Abdool yake batayi ba, a daidai lokacin aka shigo da Imran cikin motan ƴan sanda, tsayawa ameesha tayi tana murmushi ganin an fito dashi, da sauri taje yana ganinta ya rungumeta yace "kinzo?"
murmushi tayi tace "da ka zaci ba zanzo bane?"
ya girgiza kai yana sanye da ankwa yace "Allah yasa muyi nasara Allah ya rabamu da rashin sa'a, Ameesha ba zan iya barinku ba na tafi wani duniyan"
murmushi tayi tace "karka damu nasrun minallah"
yace "to"
wucewa akayi dashi suna biye dashi a baya, ko kallon inda su Abdool suke baiyi ba, nan take aka taru a kotu kowa ya samu waje ya zauna, ciki harda ameesha dake kallon takaddun, har alkali ya shigo kowa ya tashi saida ya zauna kafin suka zazzauna, nan take aka fara gudanar da shari'a, wannan karon ameesha ta hango rashin nasara tare dasu domin kamar manal ta shirya sosai, tana tsaye a gaban kotu tana kallon manal dake tsaye tana mata tambayoyi, murmushi ameesha tayi ganin manal tana amsa mata da gatse, tace "manal umar maidawa a ranan da Imran yaje gidanku kin san cewa mijinki ne ya tura mishi saƙo?"
a firgice ta ɗago kai tana kallon ameesha, ameesha tace "yes shine ya tura sako"
Abdool dake zaune yace "ban tura saƙo wa kowa ba"
murmushi ameesha tayi sannan ta ɗauko wayar Imran daya jima a hanunta ta buɗe tace "wannan sakon ne yasa Imran zuwa gidanku a cikin ke da mijinki duk wanda ya tura sakon shine ya gayyato Imran zuwa gidanku, domin tunda kuka zauna bai taɓa zuwa ba bale yasan gidanku"
rarraba ido manal ta fara, man ya kalleta yaga jikinta ya fara rawa, ganin tayi shiru kowa yayi shiru a kotun, Abdool ganin zufa a fuskan manal jikinta yana rawa ta fara rasa control ya kalli barrister fadeel wanda shine lawyer ɗinsu yayi mishi alman ya kirashi, barrister fadeel yace "ya mai girma me shari'a zanso a kira abdool mijin manal ayi mishi tambaya"
me shari'a yace "an baka dama malam Abdool bismilla"
abdool tashi yayi da sauri yaje ya tsaya a gaban kotu yayi shiru yana kallonsu, sai kuma yace "inada magana"
kowa ya bashi attention harda manal da jikinta ke ɓari, yace "matata tanada taɓin hankali duk abinda ta faɗa karya ne harda faɗuwan ammi duk karya ne ta faɗa ne sabida tsorata da tayi lokacin da ammi tayi missing step da take tafiya"
shiru sukayi, alkali yace "ina takaddun shaidan taɓin hankali da take dashi?"
da mamaki taga yasa hanu a aljihu ya mikawa alkali takadda, dubawa alkali yayi yace "tabbas haka ne tanada taɓin hankali, kotu ta kori wannan karan sannan ta wanke Imran daga zargin da ake mishi"
murmushi haɗe da hawaye suka suɓucewa Imran tare da ameesha da fahad, cire ankwa akayi a hanunshi aka buɗeshi daga inda yake, da wani irin gudu yaje ya rungume ameesha, shiru sukayi suna hawaye su duka, fahad ma ya rungumesu su ukun suna hawaye tare, manal jikinta yana rawa musamman hanunta, idanunta sukayi jajur kamar jan gauta, bakinta yana rawa ta ɗago ta kalli abdool da wani irin mugun kallo, yaki yadda su haɗa ido, ameesha tana rike da Imran suka kama hanyan fita, ammi tana ta kallonsu tana murmushi kana ganinta kasan tana cikin farin ciki, ameesha da mugun mamaki take kallon ammi ganin tana murmushi, zasu wuceta tasa hanu ta rike gefen rigan ameesha, a hankali ta juyo tana kallonta, da kyar ta ɗaga hanunta tayi mata alaman welldone kinyi kokari, da mugun mamaki ameesha take kallonta, gani tayi Ammin tayi saurin sakin gefen riganta tana kallon manal wacce take mata wani irin kallo ta kasan ido, sai taga kamar Ammin ta tsorata sosai, shiru tayi tana rike da hanun Imran da fahad suna tafiya tana juyawa tana kallon ammi, har suka fita bata daina kallonta ba, a ranta tace "something is fishy, tabbas akwai wani abu a kasa"
har suka shiga mota da Imran bata daina lekawa tana kallon ammin ba, Abdool yazo yaja hanunta sannan yaja wheelchair ɗin ammi bai yadda tayi mishi tambaya ba suka shiga mota zuwa gida, tana zuwa gida ta zauna akan sofa ta zubawa Abdool ido, murmushi yayi mata bai bata fuskan tambaya ba, kawai yace "gobe zamu tafi kasar libya domin yi miki aiki"
a hankali ta buɗe baki zatayi magana ya tashi kawai zai tafi, ammi ce ta rike mishi hanu ya kalleta tayi mishi alaman ya kaita ɗaki, murmushi yayi mata sannan ya kaita ɗaki baice komai ba ya juya ya fita, manal har dare idonta akan Abdool amma ba taga wani alaman komai a tare dashi ba, saima shirya musu kaya da yake na tafiyarsu gobe.
Ameesha ruwa me sanyi da abinci ta kawowa Imran wanda yake zaune a ɗan tsorace a falon yana rarraba ido, tace "Imran ci abinci"
a ɗan tsorace yace "anty ameesha"
murmushi tayi rabon daya kirata da unty ameesha tun ranan da sukayi faɗa a hanyan school yace ya daina kiranta da unty, itama tace idan ya fasa sunanshi ba Imran ba, tace "na'am"
yace "na gode"
rufe mishi baki tayi tace "babu godiya tsakanin yaya da kani"
abincin yaci, Abba ya kalli fahad yace "kaishi ɗakinka yayi wanka yasa sabon kaya sannan zan kira me aski yazo yayi mishi aski har gida dan naga kamar har yanzu a tsorace yake"
fahad yace "to Abba"
tare suka tafi da Imran, Abba yace "ki barshi ya huta kafa ki nuna mishi damuwan rashin mama ki nemeta da kanki sai idan ya warware sosai kafin mu fara nemanta dashi kinji?"
tace "to Abba mun gode"
*Duhu da haske is ₦400 via 8144818849 hauwa shuaibu mapi opay, evidence via 08144818849*
_Jiddah Ce_
managarciya