WATA UNGUWA: Fita Ta 39
BABI NA TALATIN DA TARA
Sai bayan awa biyu da rabi sannan Maisha ta kunna wayarta, zuwa lokacin dare ya fara kawo kai don har an yi sallar Isha.
Tuni Ja'afar ya fara ruɗewa ganin har dare ya yi ba ya da madafa ga shi su Abba sai mita suke masa a kan ya zo da su garin da bai san kowa ba don ya wahalar da su.
Wuri suka nema suka zauna, sauƙinta ɗaya da rogawar kuɗin mota a hannunsa, da su ne ya siyar musu ruwa sannan ya gyara zamansa a jikin bango yana karatun wasiƙar jaki, a ransa ya ce 'Allah Ya Sa wannan baiwar taka ba yaudarata ta yi ba, Allah kai ne masanin sirrin da ke taskace a cikin tsokar zuciyata, ka san ina sonta. Allah kada ka kama ni da laifin yaudarar bayinka salihai ta hanyar ƙwace Mardee daga gare ni.'
Yana tsaka da jero wannan addu'ar a zuciyarsa kamar a mafarki ya jiyo wayarsa na ƙugin neman agaji. Cikin azama ya zaro ta daga aljihunsa har hannunsa na rawa wurin ɗaga kiran ganin cewa abar sonsa ce
"Mun iso tun ɗazu fa, muna babbar tashar nan garin Baby." Ya faɗa da zumuɗi, da alama ba ya zarginta ko ganin laifinta a kan abin da ya faru.
Ta yi narau-narau da murya ta ce
"Ka yi haƙuri baby wayar ce bata kusa da ni, kuma chajina ya yi ƙasa shi ya saka ta ɗauke. Yanzun za a turo a ɗauke ku. Sannu da hanya"
Ya yi murmushi ya ce da ita "Bakomai wallahi Baby da ma na kawo hakan a raina, na san ba zaki guje ni ba."
Daga nan suka yi sallamar suka sauka a layi, sai a lokacin ya tuna da cewa akwai wasu masu ran a tare da shi, kiran masoyiyarsa ya mantar da shi hakan.
Mummunan kallon da ya ga Abbansa ya watsa masa ne ya saka shi kauda kai gefe ba shiri yana faɗar "Allah huci zuciyarka Abba yanzu za a zo a ɗauke mu."
*****
A can gidan Mahee kuwa bayan kashe wayar Maisha ta tuntsire da dariya tana faɗar "Allah Ya kawo ku, zaka ci gidanku ne."
Suka tafa sannan ta cire layin ta saka a ƙaramar waya ta ba wa Liyos (tsohon sarauyinta da ya kasa daina bibiyarta duk kuwa da halin da ta jefa kanta a ciki) ta yi masa umurni da zuwa babbar tasha don ɗauko su ta nuna masa lambar da zai kira idan ya ƙarasa tashar don haɗuwa da su Ja'afar.
Bayan cikar mintuna talatin Liyos ya shigo da hancin motar Mahee a cikin compound na gidanta sa'annan ya dakata ya kalli matashin da ke zaune a gefensa ya ce "Mun iso gidan, bari na muku iso."
Ya nufi cikin gidan yana ƙara mamakin waɗannan dattijan guda biyu, 'Sun girma amma ba su kama mutuncin su ba, dubi wannan ɗayan dattijon kamar mutumin arziƙi a fuska. Koda yake ba a gane abin cikin ɓaure sai an tona shi, tunda ba a fuska ake zana hali ba a zuciya ne.'
Da wannan tunanin ya isa falon ya sanar da Maisha sun ƙaraso, lokacin tana sanye da wasu arnayen kaya riga da dogon wando skin tight.
Ta dube shi a ɗage "Zaka iya tafiya, fatan baka yi wata doguwar magana da su ba."
Ya gyaɗa mata kai alamar eh.
Ta ce "To shi kenan, idan ka fita ka ce su shigo sa'annan kada ka sake ka sake shigowa falon nan, iyakaci ka nuna musu ƙofar shiga ka koma abinka."
Ya yi murmushin yaƙe ya juya da baya a zuciyarsa yana yi wa masoyiyar tasa fatan shiriya. Yasan ba a kan dai-dai take ba amma yawan ƙaunar da yake yi mata ya saka ya kasa nisantarta duk da iyayensa sun masa auren da ba ya so, amma bai daina tarairayar Maisha ba, fatansa ta lura da nusarwar da yake yi mata ta dawo hanya ya aure ta.
Yana isa ya sanar da su saƙon tare da nuna musu ƙofa har Ja'afar ya fara takawa cike da zumuɗi yana nufar hanyar da za ta sada shi da ƙofar, Liyos ya matsa kusa da shi ya ce "Ka bi a hankali fa."
Daga haka ya sa kai ya fice ba tare da ya ba wa Ja'afar damar tambaya ba.
A dai-dai lokacin ne kuma Jafsee ya ji ƙirjinsa na tsananta bugawa, duk taku ɗaya da yake yi sai ya ji kamar takun na ƙara saurin bugun ƙirjinsa ne.
Duk da haka sai ya ƙarfafa zuciyarsa don ganin irin gidan da suka zo.
Ashe yarinyar 'yar babban gida ce haka, ba mamaki shi ya sa zuciyar ta aminta da ita farat ɗaya.
Shi ne a sawun gaba yayin da iyayensa ke take masa baya. Da sallama ɗauke a bakinsa ya saka ƙafa cikin tanƙamemen falon. Yana takawa santsin miyar ƙubewar da aka yaryaɗa a wurin haɗi da santsin tiles ɗin da ke ɗakin ya ja shi take ya baje ƙasa bakinsa ya ƙumu da ɗaya daga cikin manyan royal chairs da suke ɗakin.
A take bakin ya fashe lokaci ɗaya sai ga jini yana fesowa daga laɓɓansa, ya yi jarumta sosai da ya riƙe kansa bai yi ihu ba.
Kafin ya yi wani yunƙurin tuni Abbansa da ɗan'uwan nasa sun sanyo ƙafa a falon don ganin me ya same shi. Suma sai ga su a ƙasa rikicaa! Dukkan su suka faɗa kan Ja'afar da yake kwance a ƙasa magashiyan yana mayar da numfashi saboda yana kyautata zaton karyewa ya yi a ƙafa tsabar raɗaɗin da take yi masa.
Sai kuma ga shi sun faɗo masa da ma abu ga mai neman kuka sai ga shi an jefe shi da kashin awaki. Tuni ya manta inda yake ya kwarara wani uban ihu.
Jin ihunsu ya sanya wasu dattijai guda biyu maza suka ɓullo ta ƙofar falon ta ciki har suna haɗa baki wurin faɗar "Sannu bayin Allah! Ku tashi."
Suka miƙa wa su Abba hannu kowannensu ya kama hannun mutum ɗaya sai ga shi sun miƙe, duk sabbin kayan da ke jikinsu sun ɓaci da miyar yauƙi.
Kunyata-tai-kunyata-tai suka wuce zuwa ga kujerun falon inda dattijan gidan suka musu umurni da zama suna ƙara yi musu sannu.
Jafsee kuwa cike da ƙarfin hali ya dafa kujerar ya samu ya miƙe da ƙyar ya iso cikin falon shi ma ya zauna, kayan jikinsa da fuskarsa duk sun ɓaci.
Ganin hakan ya saka ɗayan dattijon ya miƙa tare da buɗe musu wata 'yar ƙofa sai ga toilet ya bayyana.
Ɗaya bayan ɗaya suka wanke jikinsu, Jafsee ya wanke fuskarsa ya dawo falon yana takawa a hankali da alama ya samu targaɗe a ƙafar.
Kafin su fito har an goge wurin tamkar wani abu bai zuba ba.
Inda ya tarar har sun gama gaisawa tare da gabatar da kansu.
Daga nan tsofaffin alhazan nan suka ja su Abba zuwa wani ɗaki da ke waje don su ci abinci su huta kafin zuwa gobe su yi zancen da ya tara su.
Kafin su tafi Bala da Tukur suka kira Maisha don ta fito su gaisa da baƙon nata, kafin shi ma a kai shi masauki.
Ta kalli Mahee da sorfina suka tuntsire da dariya da yake a kan idon su komai ya faru, sun dasa camera a falon ta yadda za su iya kallar komai da ke faruwa kai tsaye a falon.
Wannan zumbulelen hijabin da Mahee ta yi mata umurnin sakawa shi ta ɗauko ta zuba a kan ɗamammun kayan da ke jikinta, ta fara takawa a hankali tana yin gwajin yadda za ta isa gare shi.
London girl da Mahee suka tafa tare da haɗa baki wurin faɗar "Kin iya tafiyar kamilai kuwa."
Ta fice hannunta yana cikin hijabin da alama akwai abin da ta riƙo bata son a gani. Ta isa falon
"Assalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu." Ta yi sallama cikin sanyayyiyar muryarta mai narkar da zukatan samari.
Ya ɗago cike da shauƙi yana wani irin murmushi da faɗar "Wa'alaikumus Salam tauraruwata farincikina, ƙaraso gare ni."
Ta ɗan tsaya daga nesa tana sunne kai cikin hijabi.
Ya sake sakar mata murmushi
"Ki iso gare ni abar ƙaunata, tazara mai yawa na shafe don isowa gare ki muradina."
A hankali ta tako tana ƙara nutsuwarta, kafin ta iso ya miƙe don tarbar ta. Yayin da take ƙoƙarin zaunawa a ƙasa ta faki idonsa ta tsira abu a jikin kujerar dai-dai inda ya tashi kuma inda take da yaƙinin zai sake zaunawa.
Yana kai mazaunansa saman kujerar ba shiri ya miƙe yana fitar da wani siririn ihu "Wayyo Allahna!"
Ta ɗago a karo na farko tana cewa "Me nene masoyi? Akwai wani abun ne?"
Ta kafe shi da mayun idanunta, kawai sai ya tsinci kansa da faɗar "Bakomai masoyiya." Yana ƙaƙalo murmushi.
Yadda ya yi zancen cike da karyayyiyar murya abin ya bata dariya amma sai ta gimtse.
Sarai ta san cewa allura guda biyu ta kafa masa ya zauna a kai ba tare da ya sani ba, jin azabar tsirar alluran ne ya saka ba shiri ya miƙe.
Kawai sai ta yi murmushi ta ce "To ka zauna mana, bari na saka sisterna ta kawo maka abin taɓa wa."
Ta miƙe, damar da ya samu kenan ya matsa ta ɗayan ɓangaren yana daidaita zamansa yayin da yake sosa mazaunan shi.
'Wai meke shirin faruwa da ni ne? Tun da na sako ƙafa a gidan surukan nan nawa nake cin karo da tsautsayi, abin kunya duk na gama aikata shi ga shi duk jikina tsami yake yi, ga suturata a lalace ko.'
Jafsee ne ke wannan zancen yayin da lokaci ɗaya ya zabura ya miƙe kamar wanda aka tsikara da tsinke ganin wacce ta shigo ɗakin riƙe da farantin lemo da ruwa.
Ba kowa ya gani face Maheerah da ta fito sanye da uniform ɗinta na makaranta tun a wancan lokacin ta ɓoye su, bata sake tunanin sanya su ba sai yau da take so ta shayar da shi mamaki.
Duk da cewa kayan sun matse ta sosai a yanzu amma ta tabbatar ko a cikin duhu ta je masa a hakan dole ya shaidata. Ba iya shekara ɗaya ba ko da shekaru goma ya shafe bai saka ta a ido ba, ya ganta a cikin wannan shigar dole ya shaida ta. Bare ma a shekara ɗaya jal.
Tana so ta ga irin reacting ɗin da zai yi idan ya ganta.
"Ke... ke ce?" Ya faɗa a dabarbarce yana nuna ta yayin da ta ƙaraso ta ajiye farantin a gabansa.
Mardee (Maisha) ta miƙe tana kallo sai cikin mamaki tana cewa "Ita ce wa? Masoyi kasanta ne? Sista na ce fa."
Ta faɗi haka ne don ta kara raina masa hankali ta saka ya fice daga hayyacinsa gaba ɗaya.
Har zuwa lokacin innocent Mahee ba ta ce da shi komai ba, bayan gaishe shin da ta yi ta ci gaba da ƙoƙarin tsiyaya masa lemon a glass cup.
Shi kuwa saukar muryarta a kunnensa ya sanya shi ƙara ruɗewa ya dasƙare a wajen
"Mahee! Ke kika shirya duk wannan...?"
UMMU INTEESAR CE
managarciya