WATA UNGUWA: Fita Ta 17

WATA UNGUWA: Fita Ta 17

BABI NA SHA BAKWAI

 

_RANAR WANKA BA A BOYON CIBI_

 

Tafiya take cikin ƙuncin da raɗaɗin zuciya, tuni idanunta suka makance bata ganin kowa bata ganin komai a gabanta sai muradinta, a yanzun ta yarda da cewa bata da wanda yafi shi a rayuwarta. Tana da yaƙinin cewa idan duk duniya ta juya mata baya shi ba zai ƙyamace ta ba balle ya guje ta, shi kaɗai ne bangon da ya rage mata wanda zata jingina da shi ta ji sanyi a zuciyarta da garwashin wutar ƙiyayya ke ruruwa a cikinta.

 

Mintuna kaɗan suka sada ta da titin unguwar wanda tsabar ruɗanin da take ciki bata ma san ta zo ba, sai da ta ji ƙarar ababen hawa da order wasu daga ciki sa'annan ta ankara.

 

Tun a cikin layinsu mutane ke ƙare mata kallo ganin yadda take tafe cikin yanayin fitar hayyaci ga kuma Uniform ɗinta sun lalace da jini haka fatarta duk ta yi ruɗu-ruɗu shacin bulala ko ina kwance a fatarta har a gefe-gefen fuskarta kasancewarta fara ya saka raunin suka bayyana ƙarara.

 

Haliru Maishago yana zaune ta gifta shi ta wuce, girgiza kai kawai ya yi cikin alamun tausaya duk da bai san me ya faru da ita ba.

 

Tare Napep ta yi tare da faɗawa ba tare da ta tsaya yin ciniki ba.

Sai da matuƙin ya tada Napep ɗin sannan ya ce "Ina zamu.?"

 

Da ƙyar ta iya buɗe baki kamar wacce aka yiwa dole ta ce "Dagarma." Daga haka ba ta sake furta komai ba har suka isa unguwar.

 

Jakarta ta buɗe ta ciro kuɗin ɗazu da Baba ya bata ta miƙa wa mai Napep ɗin, bai ce komai ba ya cire kuɗinsa ya bata canji a ƙasan zuciyarsa yana jimamin abin da ya sami wannan kyakkyawar yarinyar haka.

 

Cike da ƙarfin gwuiwa da saka rai ta nufi cikin gidan da take tunanin yanzu nan ka dai ne madogararta, ta saka kai tare da shigewa cikin gidan.

 

Jama'ar gidan sai ƙare mata kallo suke, wasu daga cikin karuwan suka kasa haɗiye gulmar da ta zo masu, biyu daga cikinsu ne suka haɗa baki gurin faɗar "Bariki alalen gero idan baka iya ba sai ta kwaɓe maka."

Gayen ɗazu wanda ya nunawa Sadiƙu ɗakin da suke ciki ya kalle ta. Ganin yanayin da take ciki ya bushe da dariya ya ce "Duniya ta miki a tishawar jaki ne shi ya sa kika dawo nan? Ko da yake kin zo inda ya dace domin nan gida ne na kowa, kawai ki zo mu jone don bana tunanin wanda kika zo domin shi zai saurare ki."

 

Duk wannan maganganun da suke faɗa ta ji, sai dai kalma ɗaya bata yi nasarar shiga ƙwaƙwalwarta ba balle ta iya haddace ta.

Wucewa ta yi ba tare da ta tamka musu ba ta nufi ɗakinsu Jafsee.

 

Zaune ta same shi akan katifa yana jinyar jiki domin shaƙar da Sadiƙu ya mi shi ɗazu bata wasa ba ce, har ya jiyo ƙamshin mutuwa a ɗazun.

Duddoo ne zaune kusa da shi yana masa jajen abin da ya faru ɗazun, ɗago kan da zai yi ya ganta a tsaye, cikin rawar murya ya ce

 

 "Mahee ke ce?" Sai a lokacin Ja'afar ya ɗago kai ya kalli abokin nasa sannan ya sauke dubansa akan fuskarta.

 

Ras ras! Ƙirjinsa ya buga da ƙarfi ganin yanayin da take ciki, da ƙyar ya ce "Mahee me kika dawo yi a nan.?"

 

Wani busasshen murmushi ta masa sa'annan ta zauna a saman carpet na ɗakin tare da faɗar "Ina mai maka albishir cewa na dawo ne domin mu rayu tare har ƙarshen rayuwa."

 

Kallon baki da hankali ya yi mata tare da hangame baki.

Sarai ta fahimci ƙarin bayani yake nema don haka ta koma yin murmushi ta ce "Na dawo nan ne domin mu yi aure, wallahi ko a nan gidan ka ajiye ni zan zauna, yanzu ba ni da kowa daga Allah sai kai."

 

Kallonta kawai yake, kallon da ba zaka iya fahimtar ma'anarsa kai tsaye ba 'Lallai wannan bata da hankali, a yadda suka farfasa mata jikin nan a matsayinta na jininsu, kenan ni me zai faru da ni idan suka kama ni karo na biyu?' ya faɗa a ransa.

 

A fili kuwa miƙewa tsaye yayi idonsa ƙyar a kanta yana faɗar

 

 "Mahee ki rufa min asiri ki tashi ki koma gida, ko so kike wannan mahaukacin yayan naki ya kashe ni ne?"

 

Hawayen da suka ƙafe mata tun ɗazu ne suka yi nasarar sake ɓallewa ta ce "Abba ya kore ni daga gidansa da ma rayuwarsa da ta iyalansa ga baki ɗaya, yanzu ba ni da kowa sai kai, kai kaɗai ne na yi imani zaka zauna da ni cikin kowanne hali saboda soyayyar dake tsakaninmu."

 

Kallon sakarya yake binta da shi yayin da ya ji maganar tata ta zo masa a banbarakwai. Dariya ya sheƙe da ita sannan ya tsuke fuska kamar bai taɓa dariya ba ya ce

"Sakaryar ina ce ke Mahee? Iyayenki ma suka guje ki balle ni? Shin wai ke har a cikin zuciyarki baki taɓa zargin yaudararki zan yi ba? Lallai zuciyarki gafalalliya ce kuma ta shagala da duniya da yawa."

 

A ruɗe take binsa da wani irin kallo mai nuni da tsantsar mamaki. Tarjamar kalamansa ta shiga yi a ƙwaƙwalwarta kafin ta iya buɗe baki da ƙyar ta ce "Ban fahimce ka ba, kana nufin baka sona, ba zaka aure ni ba?"

 

Jinjina mata kai ya yi alamun tabbatarwa kana ya ce "Idan kika zaci ni Ja'afar zan aure ki to kin yaudari zuciyarki, ba zan taɓa auren gafalalliyar yarinya irinki ba wacce zuciyarta ta fi ƙarfinta, iyayena suna kyautata min zato ba zan saka masu da auren wacce ta zubar da ƙimarta a waje ba."

 

Yanzu kam lissafinta ya gama ƙwacewa, fatan take yi ta buɗe ido daga cewar a mafarki wannan abin ke faruwa, amma sai dai da alama wannan zahiri ne ya zo a cikin littafin ƙaddarar rayuwarta.

 

Tana kuka ta tsugunna a gabansa tana roƙon ya rufa mata asiri ya aure ta, faɗar take "Ka min rai masoyina, kai ne silar gurɓacewar rayuwata, ka yi sanadin raba ni da ahalina da mutuncina, shin idan ka kore ni ina na nufa?"

 

Sosai tausayinta yake ratsa jijiyoyin jikin Duddoo duk da kasancewar shi ɗan iska amma ya tausayawa rayuwarta.

 

Duban Ja'afar ya yi cikin sanyin murya ya ce "Jafsee ka tausaya wannan rayuwa da take cike da ƙunci a yau, don Allah ka zauna da ita ko da ba zaka aure ta ba."

 

A zafafe ya juyo da dubansa ga Duddoo "Ashe fa kai baka da hankali ko? So kake wannan mahaukacin yayan nata ya kashe ni, ko so kake banzan mahaifinta ya je ya tonan asiri a gun mahaifana?"

 

Duddoo zai sake yin magana kenan ya daga masa hannu da cewa "Bana son jin komai daga gare ka, ka sani sabo da kaza bai hana a yanka ta, idan tausayinta kake ji kai ka aure tan mana, dama can ni ba ita nake so ba jikinta nake so kuma na samu, me ya rage?"

 

Wani wahalallen kuka ne ya kufce mata da gudu ta tashi tana gyara zaman hijabinta da jakarta ta bar ɗakin domin ba zata juri sauraren waɗannan kalaman ba.

 

Duddoo ya so ya bi ta ya lallashe ta ko ta ji sassauci a zuciyarta na wannan yaudarar da ta zo mata kwatsam daga inda bata yi tsammani ba, sai dai babu Wadataccin kalmomi a bakinsa da zai iya amfani da su, da yana da yadda zai yi da ya taimake ta, amma inah....

 

A waje ta wuce Gayen ɗazu ya yi ƙoƙarin dakatar da ita da cewa "Dama na faɗa miki, kawai ki dawo mu jone haka bariki ta gada." Ko saurarensa bata yi ba ta bar gidan cike da ƙuncin zuciya.

 

Takawa kawai take amma bata san inda ƙafarta ke sauka ba, kamar yadda bata san inda ta nufa ba, duniyar ta mata duhu ga baki ɗaya, jinta da ganinta sun yi nisa ta yadda bata iya hange ko jin abin da ke faruwa a kusa da ita ba.

 

Haka ta ci gaba da nausawa cikin layukan unguwar kamar taɓaɓɓiya, bata ma san da wanzuwar mutane a gun ba balle ta fahimci kallon tausayi da mamakin da suke binta da shi.

 

 

Sai da ta yi nisa sosai har ma ta fice daga unguwar Dagarman kafin ta samu gindin wata bishiyar ta zauna, tana son bawa ƙwaƙwalwarta damar yin lissafi da sanin abin da ya kamata ta yi.

 

Sai da ta yi iya ƙoƙarinta kafin ta haɗa zarrukan tunaninta da suka gama kuncewa kafin ta samu mafita.

 

Zumbur ta miƙe kamar an tsikare ta da allura ta nufi titi mafi kusa abin hawa ta tare, tare da shiga "Tasha zamu Malam." Shi ne kaɗai abin da ta ce yayin da take gyara zamanta a cikin abin hawan.

 

"Wace tasha yar'uwa?"

 

"Koma wacce." Ta amsa cikin ƙosawa.

 

Bai sake cewa komai ba ya ja zuwa tasha mafi kusa.

Bayan ta biya shi hakkinsa ta sauka ta ƙara nausawa cikin tashar, 'yan union ne  suka yi mata caa! Kowanne yana tambayarta garin da zata je.

 

Rashin amsar bayarwa ya saka ta tambayi ɗaya daga cikinsu, wace jihar ce tafi nisa da nan?"

 

"Balgori."

 

"Tafiyar awa nawa ce daga nan?"

 

"Awa goma Hajiya, amma ki yi haƙuri zan miki katsalandan, don Allah me ya same ki haka? na ga jikinki a farfashe."

 

Wani malalacin tsaki ta ja, a harzuƙe ta ce "Zaka sama min mota ko na ƙara gaba? Gari da yawa maye baya ci kansa ba."

 

Cikin ɓarin baki ya ce "Afwan Hajiya mu je in kai ki gun motar garin.

 

*************

A ɓangaren Irfan kuwa ya kasa jurar rashin ji daga Mahee kwana biyu, duk yadda ya so taushe zuciyarsa abin ya ci tura, dalili kenan da ya saka ya shirya da yammacin ranar Laraba ya nufi unguwarsu. Tuni ya manta da alƙawarin da ya yi wa Ma'eesh na cewa zai yi iya ƙoƙarinsa ya ga ya manta ta, kuma zai daina kula ta na ɗan lokaci.

 

Bai zame ko'ina ba, sai inda ya saba parking motarsa fitowa ya yi ya taka zuwa bakin ƙofar gidansu.

 

A haka ya ƙaraci sallamarsa ba kowa a zauren, da alama kuma Umma dake ciki bata jiyo shi ba.

 

Ya fi mintuna biyar tsaye a gun ko yaron da zai aika ciki bai samu ba, dalili kenan da ya sanya bisa tilas ya juya ya nufi motarsa zuciyarsa ba daɗi. Sadiƙu da yake shirin karyo kwanar gidan nasu yana hango Irfan ya yi saurin laɓewa, domin har ga Allah bai shirya amsar tuhumar da Irfan ɗin zai masa akan Mahee ba. Domin shi kansa har lokacin yana cikin jimami da danasanin sanar da iyayen nasu halin da ake ciki.

 

Da ya san abinda zai biyo baya kenan tabbas da bai faɗa ba.

 

 

Irfan ya ci gaba da tafiya jiki a saɓule yayin da ƙwaƙwalwarsa ke cunkushe da tunani iri-iri. Ya zo daf da shagon Haliru kenan kamar daga sama ya jiyo ance "Irfan!"

 

Cikin hanzari ya waiga inda ya jiyo sautin don ganin mahaluƙin da ya kira shi.

Bai iya ganin kowa ba sai maishagon dake zaune a ƙofar shagonsa, don haka yake kyautata zaton shi ɗin ne ya kira shi. Dalili kenan da ya sanya ya ƙura masa ido.

 

Ya lura cewa da magana a bakin mutumin ganin yadda bakinsa ke motsi tamkar mai lazimi, amma kuma sai ya kawar da kansa gefe.

 Hakan ya saka Irfan ya ci gaba da taka sawayensa kai tsaye zuwa inda maishagon yake zaune.

 

Da isarsa ya miƙa mishi hannu suka yi musabaha sannan ya zauna kan teburin da maishagon ke zaune.

 

"Ɗan'uwa ka kira ni kuma baka ce komai ba, da alama akwai magana a bakinka."

 

Irfan ya faɗa.

 

Haliru ya kalle shi, sai ya yi kamar zai ce wani abu kuma sai ya yi shiru.

 

Can ya ce "Gaskiya ina son na faɗa maka wani abu amma ina tsoron abin da zai je ya dawo, ka san ance _baki shi ke yanka wuya._"

 

"Karka damu ka faɗa min koma miye Insha Allah a nan gurin zamu yi wa zancen ƙabari mu binne shi ba mai ji."

Ya yi mi shi murmushi.

 

Haliru ya gyaɗa kai alamun gamsuwa ya gyara zama ya ce "ka yi mamakin kama sunanka da na yi ko?"

 

Irfan ya gyaɗa kai ba tare da ya yi magana ba domin zuciyarsa ta zaƙu da son jin me bawan Allah nan zai gaya mi shi.

 

"Ko ba kai ba ne Irfan saurayin Maheerah ta gidan malam Isa?"

 

Nan ma sake daga kai ya yi bai yi magana ba, tamkar dai wanda cutar kurumta ta kama shi.

 

Haliru ya ɗora zancensa da faɗar "Ina tunanin daga gidan kake yanzu, kuma da dukkan alama baka samu wacce ka je nema ba."

 

"Eh haka ne, na yi sallama amma gidan kamar ba kowa shi ya sa na juyo ko wani abin ya faru ne?" Ya tambaya da yar damuwa a fuskarsa.

 

"Gaskiya ina ji a jikina ba lafiya a gidan, domin kwana biyu da suka shuɗe ina zaune a nan na ga wucewar Mahee cikin wani irin yanayi, jikinta duk ya yi ruɗu-ruɗu da shacin bulala, ga dukkan alamu dukanta aka yi bana raba ɗayan biyu ba, ko dai a makaranta aka dake ta ko kuma a gida domin da uniform a jikinta ta wuce kuma tun lokacin ban sake ganinta ba. Duk da cewa idan gari ƙalau ne kusan kullum sai ta zo shagon nan siyayya."

 

Zaro ido waje Irfan ya yi ya kiɗime

 

"Me ka ce? Don Allah faɗa min meke faruwa da masoyiyata?."

 

"Nima ban sani ba sai dai ina ji a jikina ba lafiya a gidan, domin yayanta Sadiƙu mutumina ne kusan kullum sai ya zo mun gaisa mu ɗan taba hira sannan ya shiga gida. Amma yau kimanin kwana biyu kenan ban gan shi ba, dalili kenan da ya sanya na ɗiga alamar tambaya a al'amarin gidan."

 

Irfan ya miƙe tsaye tare da cire hular kansa cike da damuwa ya ce "Inna lillahi wa Inna ilaihir raji'un! Meke faruwa ne?"

 

Ganin ba zai sami amsar ba ya wuce ba tare da ya tsaya yi wa Haliru sallama ba, zuciyarsa ta ci gaba da tsinkayo mi shi abubuwa marasa daɗi da za su iya faruwa a gidan.

 

A haka ya ja motarsa ya bar unguwar bayan ya ɗaukar wa zuciyarsa alƙawarin cewa sai ya binciko abin da ke faruwa.

 

Washe gari tun da sassafe ya yi wa gidansu Maheerah zobe. Yana isa ƙofar gidan Baba yana fitowa daga cikin gidan.

 

"Assalamu alaikum Baba ina kwana."

Irfan ya faɗa cikin ladabi yana rusuna kai.

 

Baba ya miƙo masa hannu yana faɗar

"Wa'alaikumus Salam, malam Irfan sannu da zuwa."

 

Bayan sun gaisa Baba ya kalle shi fuskarsa ba yabo ba fallasa ya ce

 

"Yawwa malam Irfan dama ina nemanka."

 

"To Baba Allah Ya Sa dai lafiya."

 

"Lafiya amma ba ƙalau ba, so nake na sanar da kai daga yau ka hutar da kanka zuwa gidan nan, domin wacce kake zuwa don ita ta yi maka nisa, nisan da ba zaka iya kamo ta ba."

 

A razane ya dago rikitattun idanunsa muryarsa na rawa tamkar signal ta  ɗauke a gidan tv ya ce "Ban... Ban fahimta ba Baba."

 

"Ina nufin ka cire ranka da auren Maheerah, domin babu ita a gidan nan yanzu, na gode maka da duk dawaniyar da kake damu. Haƙiƙa da ina da 'ya mace a yanzu ko wacece da na baka aurenta domin na yarda da nagartattun halayenka da tarbiyyarka. Ka je kawai Allah Ya musanya maka da mafi alkhairi."

 

Daga haka ya wuce ya bar Irfan nan tsaye ya sake baki kamar wani gaula.

 

Tarin tambayoyi ne cunkushe a ma'adanar tunaninsa, amma ya rasa mai karɓa mi shi su.

 

Tamkar mutum-mutumi haka ya ƙame a wajen ya kasa motsa ko da yatsansa.

 

Yana cikin wannan yanayin sai ga Sadiƙu ya fito daga zauren gidan suka yi kiciɓis da juna.

 

Sadiƙu da ya ga ba shi da wata mafita tun da Irfan ya riga ya gan shi hakan ya saka ya matso kusa yana murmushin yaƙe ya ce "Aminci Allah ya tabbata a gare ka."

 

Rashin sani yafi dare duhu, da Sadiƙu  ya san cewa Irfan ya zurfafa a kogin tunani kuma bai lura da shi ba. Da ya yi amfani da kyakkyawar damar da ya samu gurin tserewa domin hausawa sun ce  _hankali ke gani ido gulu-lu ne."

 

Wannan sallamar da ya yi ita ta dawo da Irfan daga duniyar tunani zuwa duniyar da yake rayuwa a ciki.

 

A maimakon ya amsa masa sallamar sai cewa ya yi "Yaya Sadiƙu don Allah meke faruwa a gidan ne?"

 

Zuciyar Sadiƙu ta buga da ƙarfi dam! Domin da  _alama wuƙa zata tono garma_ abin da ya daɗe yana ɓoyewa dole ya bayyana shi a yau.

Ya kalli Irfan da fuskar shi da yake ƙoƙarin shimfiɗa yanayin mamaki a maimakon damuwar da yake ciki ya ce "Me kake magana ne a kai?"

 

"Baba ne ya min wasu irin bauɗaɗɗun jawabai da na kasa gane kansu, wai in je in manta da Mahee." Ya yi maganar a birkice.

 

Sadiƙu ya ɗago kai "_Ranar wanka ba a boyon cibi_ Irfan, na yi iya kokarina domin in ɓoye daga ganinka ta yadda ba zaka yi tozali da ni ba bare ka tambaye ni ɓoyayyen sirrin da na yi sakacin bayyanawa har ya zama linzamin datse farin cikin gidanmu."

Ya sauke zancen a kasalance.

 

Irfan ya ɗago a hartsigi "Ka fito da ni duhu don Allah, na ga kana neman ƙara hargitsa min hargitsattsiyar ƙwaƙwalwata da Baba ya yi nasara kunce notikanta."

 

"Ka yi haƙuri Irfan Baba ya kori Maheerah daga gidan nan gaba ɗaya haka ma ya cire ta daga cikin ahalinsa gaba ɗaya."

 

Wani guf, Irfan ya ji tamkar ya kwaɗa masa guduma a tsakar kai. Take jikinsa ya hau rawa kamar an kaɗa mazari.

 

Saɗiku ya wuce jiki a saɓule ya bar Irfan nan tsaye yana firfita da hular kansa. Duk da cewa kuwa har lokacin ana tsakiyar sanyi ne amma gumi ne ke tsattsafo masa ta ko wace kafar gashi dake jikinsa