Ƙabilu Mazauna Zamfara  Sun Tabbatar Da Goyan Bayan Su Ga  Matawalle

Ƙabilu Mazauna Zamfara  Sun Tabbatar Da Goyan Bayan Su Ga  Matawalle

Daga Hussaini Ibrahim.

 Tawagar  shugabanni Kabilun mazauna cikin Jihar Zamfara, sun jadda goyan bayan su ga gwamna Bello Matawalle ,ga sabon  mai ba  wa gwamnan Matawalle shawara a hukumar da Alumma,Hon Aliyu Suleman Dansadau.

Tawagar Shugabanin al'ummar da ba 'Yan asalin jihar ba, karkashin jagorancin Shugaban su na Jihar, Enginiya Joel Thomas ,sun ziyarci , sabon mai ba gwamna Matawalle shawa ne ,Hon Aliyu Suleman Dansadau domin jadda goyan bayan su ga Gwamnatin jihar da kuma tayashi murnar zamowa mai ba gwamna Matawalle shawara hukumar.

Shugaban Joel Thomas,ya bayyana cewa, gwamna Matawalle ya sanya wanda ya dace ,akan jagorancin hukumar .kuma muna mai tabbata maku cewa,zamu baka goyan baya da kuma hadinkai wajan cigaban wannan Ma'aikata tama.inji Joel Thomas.

" Jole ya kuma tabbatar da cewa, Gwamnatin jihar Zamfara na basu hakokin su yadda ya kamata bata nuna banbanci wajan bada tallafi tana daukar mu tamkar 'yan Jihar muna godiya akan haka.inji shugaba Jole.

A jawabin,Mai ba gwamna Matawalle shawara a hukumar,Hon Aliyu Suleman Dansadau ya tabbatar masu da cewa, gwamna Matawalle na kowane kuma baya nuna banbancin al'umma ko yare.indai mutum yana cikin jihar Zamfara daya ya ke da kowa da kowa.inji Hon Dansadau.

Hon Aliyu Dansadau ya kuma tabbatar masu da cewa, Ofishinsa a bude yake ga kowa da kowa dan amsar shawara da koken akan abunda ya shafi al'ummar da ba 'Yan asalin jihar ba.

Kuma Gwamnatin jihar Zamfara zata Samar wa al'ummar da ba'Yan asalin jihar dawamamen zaman lafiya wanda dama yawaicin su 'yan kasuwa ne , sakamakon magance matsalar tsaro yanzu haka kasuwanin da basa ci yanzu ana hadahada su ,kuma Babu irin al'ummar da bata zuwa cikin kasu . wannan babbar nasarace a garemu.

A karshe Daraktan hukumar ,Kabiru Muhammad Maradun ya bayyana godiyarsa ga tawagar Shugabanin al'ummar Jihar Zamfara akan jadda goyan bayan Gwamnatin gwamna Matawalle .

Kabiru Maradun ya kuma tabbatar da cewa,duk wani tallafi ko taimakon da Gwamnatin ke badawa al'ummar da ba 'Yan asalin jihar na cin gajiyr sa a wannan Ma'aikata.dan hakama insha Allah yadda aka saba haka zaidore tunda ga sabon mai ba wa gwamnan Matawalle shawara a hukumar Hon Aliyu Suleman Dansadau ya shigo wannan Ma'aikata kowa zai dara da yarda Allah.