Mahara Sun Sace Mai Jego Da  Mata 3 A Neja

Wani mazaunin unguwar da shima ya zanta da Wakilinmu, ya ce sai dai daga bisani maharan sun sake daya daga cikin matan mutumin tare da danqa mata jaririn daya matar da sunan ta rene shi, a yayin da su ka wuce da mahaifiyar jaririn. Ya ce 'yan bindigan sun sace mata aure ta biyun ne daga wani gida da ke maqotaka da na jami'in na kwastam, sai kuma wata budurwar daban daga cikin gidan. Tini ami'in wanda ke aiki a Lagos ya garzaya gidan nasa a yau Alhamis, kamar yadda a ka bayyana.

Mahara Sun Sace Mai Jego Da  Mata 3 A Neja
Mahara

Masu garkuwa da mutane sun auka unguwar Kwamba da ke Garin Suleja na jihar Neja a daren Laraba, inda su ka sace matan aure biyu da 'yan-mata biyu. Wani jagoran al'umma a yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaidawa Aminiya a yau Alhamis cewa, daya daga cikin matan mai jego ce da a ka yi wa aiki a yayin aihuwa qasa da wata guda.

Ya ce a na zargin 'yan bindingan da adadinsu ya kai 30, su na neman wani babban jami'in kwastam ne amma kasancewar ba su same shi ba, sai su ka xauki matansa biyu da ya haxa da mai jegon, da kuma wata yarsa budurwa.

Wani mazaunin unguwar da shima ya zanta da Wakilinmu, ya ce sai dai daga bisani maharan sun sake daya daga cikin matan mutumin tare da danqa mata jaririn daya matar da sunan ta rene shi, a yayin da su ka wuce da mahaifiyar jaririn.

Ya ce 'yan bindigan sun sace mata aure ta biyun ne daga wani gida da ke maqotaka da na jami'in na kwastam, sai kuma wata budurwar daban daga cikin gidan. Tini ami'in wanda ke aiki a Lagos ya garzaya gidan nasa a yau Alhamis, kamar yadda a ka bayyana.

Wasu majiya sun ce maharan da su ka isa yankin da misalin qarfe dayan dare, sun shafe kamar sa'a guda su na ta harbe-harbe kafin su ka bi ta wani rafi da ke kusa da kasuwar zamani ta Auwal Ibrahim da ke unguwar ta Kwamba da ke kan hanyar Suleja zuwa Minna.

"Bayan tafiyarsu ne jami'an tsaro su ka je unguwar bayan shigowa ta kan titi, sai dai barayin kuma sun fice ne ta gefen rafi da ke bayan unguwar, inji wani mazaunin yankin. Wakilinmu ya tuntubi lambar babban kwamandan 'yan sanda na shiyyar Suleja ACP  Sani Badarawa, sai dai bai amsa wayar ba har izuwa lokacin aikawa da wannan labarin.