Rikici ya kunno kai a masarautar Kontagora kan naɗin sabon sarkin Sudan

Sakataren Kwamitin Zaɓen Sarki Ya Ajiye Aikinsa, bayan mutum 47 sun bayyana aniyarsu ta zama sarkin Sudan na Kontagora, abin ya yi zafi ganin yanda manema suka yi yawa.

Rikici ya kunno kai a masarautar Kontagora kan naɗin sabon sarkin Sudan
'Yan Bindiga Suna Karɓar Shinkafa da taliya matsayin Kudin Fansa domin yunwa ta kama su a daji
Rikici ya kunno kai a masarautar Kontagora kan naɗin sabon sarkin Sudan
Sakataren Kwamitin Zaɓen Sarki Ya Ajiye Aikinsa, bayan mutum 47 sun bayyana aniyarsu ta zama sarkin Sudan na Kontagora, abin ya yi zafi ganin yanda manema suka yi yawa.
Daga Babangida Bisallah
Ranar alhamis 9 ga watan satumbar shekarar 2021 Allah ya dauki ran sarkin Sudan na kwantagora, Alhaji Sa'idu Umaru Namaska, sakamakon jinyar da yayi a wani asibiti mai zaman kansa a Abuja.
Mai martaba sarkin sudan, Alhaji Sa'idu Namaska an haife shi ranar 31 ga watan Disambar 1937, a garin kwantagora, da ne ga Malam Umaru Sarkin Kudu wanda shi kuma da ne ga Umaru Nagwamatse sarkin masarautar na farko da ya kafa masarautar kwantagora.
Marigayi Sa'idu Umaru Namaska jika ne ga Nupawa a bangaren mahaifiyarsa, mahaifiyarsa jika ce ga marigayi Malam Chado daga unguwar Nupawa cikin garin kwantagora, shi tabashi ne ga kabilar Nupawa da ya rike wannan zumuncin, domin har karshen rayuwarsa yana kyautata masu a matsayin su da abokan wasa.
Marigayi Sa'idu Namaska dan uwa ne ga Magajin Garin Kwantagora na II da III, wadanda jikoki ne ga Nupawa bangaren mahaifiyarsa.
Marigayi sarkin sudan cikakken jinin sarauta ne kuma jika ga Shehu Usman Danfodio, malami ne na addinin musulunci da ya gina rayuwarsa akan koyarwar addinin musulunci.
Masarautar Sudan ta Kwantagora, ita ce masarauta ta goma sha biyu a tsarin sarautun gargajiyar arewacin kasar nan.
Ya fara karatun zamani na elementary daga 1945 zuwa 1950. Daga nan ya tafi makarantar middle da ke Bida a shekarar 1953. Ya fara aiki a matsayin dan doka a lokacin mulkin mallaka, a dai karkashin tsarin kuma ya dawo a matsayin malamin daji a shekarar 1954, a shekarar 1957 ya samu wannan karin girman. Inda ya koma makaranta dan karo ilimi shari'ar musulunci, a bangaren tsangayar mulki a zariya. A shekarar 1962 ya kammala da kyakkyawar sakamako.
Bayan kammala karatunsa da dawo bakin aiki, a shekarar 1968 ya zama alkalin kotun yanki a garin Salka a shekarar 1968 din, a shekarar 1971 ya samu canjin wajen aiki zuwa masarautar Zuru ta jihar Kebbi a yau,  inda ya zauna a garin Mahuta ta karamar hukumar Fakai a yau duk dai a cikin masarautar Zuru.</div
A shekarar 1972 ya sake komawa Zariya dan karo ilimin addinin musulunci, bayan kammala karatunsa da shekaru biyu a shekarar 1974 ya zama sarkin Sudan na Kwantagora.
Kafin rayuwarsa, shi ne mataimakin shugaban majalisar sarakunan Neja, ya rasu yana da shekaru tamanin da hudu (84) a duniya.
Matarsa ta farko, itace marigayiya Hajiya Sa'adatu, yana da 'ya'ya sama da dari da jikoki da dama.
Shi ne sarki na biyu da ya dade akan karagar mulkin masarautar inda ya kwashe shekaru arba'in da bakwai (47) bayan Sarki Ibrahim Nagwamatse da ya share shekaru arba'in da tara (49) kan karagar sarautar.
Masarautar Sudan ta Kwantagora, tayi sarakuna shida tun daga kafa ta a shekarar 1859 zuwa yau 2021. A karkashin ikon marigayi Sa'idu Umaru Namaska, masarautar na da hakimai guda ashirin.
Sakataren kwamitin zaben sabon sarkin Sudan na Kwantagora,  Barista Ahmed Tijjani ya ajiye aikinsa. Wannan ya biyo bayan zargin da wasu ke masa na ra'ayin wani dan takarar kujerar sarautar.
Bincike ya tabbatar da cewar Barista Ahmed Tijjani wanda shi ne Shamakin Kontagora, baya cikin masu zaben sabon sarkin duk da cewar yana rike da sarautar Shamakin Kontagora.
Sakataren yace wasu yan takarar sun jahilci lamarin, saboda masu zaben sabon sarkin mutum biyar ne kuma ba na cikin su.
Masu zaɓen sabon sarkin dai sun hada da Galadiman Kwantagora, sai Waziri, da Madawaki wanda ke rikon masarautar a halin yanzu, da Kofan Kwantagora, na biyar din su shi ne Magayakin Kwantagora.
Tuni dai kwamishinan kula da masarautu da kananan hukumomi,  Barista Abdulmalik Sarkin Daji ya aika darakta na sashen kula da masarautu na ma'aikatar dan maye gurbinsa.
Zuwa yanzu dai 'yan takara arba'in da biyar ne suka aike da wasikarsu dan nuna sha'awar takarar wannan kujerar.
Al'ummar kasar Kwantagora dai sun zura idanu dan ganin wadanda masu zaben zasu zabo a matsayin wanda zai gaji kujerar tsohon sarki, marigayi Alhaji Sa'idu  Umaru Namaska da ya rasu cikin watan satumbar nan sanadiyar rashin lafiya.
Daga cikin ka'idodin tsayawa takarar, wajibi ne ya zama ka fito daga tsatson masarautar kuma ya zama ka gaji sarautar sannan tare da amincewa da yin biyayya ga dukkannin al'adun masarautar.