'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari Kauyen Katsina, Sun Hallaka Mutane 5 

'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari Kauyen Katsina, Sun Hallaka Mutane 5 

 

Wasu ‘yan bindinga sun hallaka mutane biyar tare da raunata wasu hudu a unguwar Barebari da ke gundumar Dukke a karamar hukumar Funtua ta jihar Katsina. 

Wani mazaunin yankin, wanda ya ce an kashe ‘yan uwansa a harin ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa, ‘yan ta’addan sun shiga kauyen ne da misalin karfe 8:30 na dare. 
A cewarsa, sun yi shiga ne kamar na mutanen kirki, inda suka shiga jama’a tare da aikata mummunan aikin. 
Ya kuma shaida cewa, a lokacin da suka shigo kauyen, sun rarraba kansu ne a zagayen garin don samun damar aikata barnar. 
“Daga nan ne suka fara harbin kan mai uwa da wabi tare da razana mazauna. 
“Akwai wani wuri da muke kira Gidan Ruwa, inda mutanenmu ke buya duk lokacin da aka kawo hari. "Sai dai, a wannan karon ‘yan ta’addan sun toshe wurin tare da kiran mutane kamar mutanen kirki. A nan aka kashe dan uwana."
Ya kuma bayyana ‘yan ta’addan da suka kashe sauran mutanen a wurare daban-daban tare lalata abubuwa da yawa. 
A cewar wani mazaunin yankin na daban, ‘yan ta’addan sun jikkata mutane hudu, inda suka samu raunukan harbin bindiga a harin. A cewarsa, wannan ne karon farko da aka kai hari irin wannan da aka kashe mutane a kauyen, inda yace galibi ana sace mutanen yankin ne tare da neman fansa.