Ɗansanda ya harbe matar ɗansanda tare da jikkata mutane 2 a Calabar

Ɗansanda ya harbe matar ɗansanda tare da jikkata mutane 2 a Calabar

Wani ɗansanda mai muƙamin sifeto da ke aiki a rundunar ƴansanda ta jihar Cross Rivers ya kashe wata mata tare da raunata wasu biyu bayan ya buɗe wuta a kan mutanen a jiya  Lahadi.

Kakakin rundunar ƴansanda na jihar, SP Irene Ugbo, ta tabbatar da faruwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa a Calabar a jiya Lahadi.

Ms Ugbo ta ce ɗansandan wanda ke aiki a caji-ofis ɗin ƴansanda na Atakpa, ya buɗe wuta ne jim kaɗan bayan ya dawo daga inda ya ke aikin gadi a wani banki.

Sai dai ta ce tuni ƴansanda su ka cafke jami'in da ake zargin yayin da mutane biyun da ya harba ke samun kulawar likitoci.

Ta kara da cewa ko sanya dawo, an ga ya rufe kofar shiga caji-ofis ɗin ya kuma hana mutane wucewa, inda duk wani yunkuri na kwace bindigan sa ta lumana ya ci tira.