Wamakko Ya Yi Ta'aziyar Rasuwar Mutum 29 Da Jirgin Ruwa Ya Nutsar A Sakkwato

Wamakko Ya Yi Ta'aziyar Rasuwar Mutum 29 Da Jirgin Ruwa Ya Nutsar A Sakkwato

 

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya yi ta'aziyar mutum 29 da jirgin ruwa ya nutsar da su a kauyen Gidan Magana karamar hukumar Shagari a jihar sakkwato.

Ya mika sakon ta'aziyar ne ga mahaifa da dangin  margayan a wani bayani da maitaimakwa Sanatan kan harkokin yada labarai Hassan Sahabi Sanyinnawal ya fitar ya ce ya nuna matukar kaduwarsa ga faruwar lamarin ya roki Allah ya gafartwa mamatan ya baiwa danginsu hakurin rashinsu
Jirgin ruwan wanda ya kife a wannan Laraba a Gidan Magana ya yi sanadin mutuwar matasa 29 a jirgin da ya dauko fasinjoji da yawa.
Halin da ake ciki ana cigaba da neman wasu mutanen a ruwan da ba a gani ba.