An Binne Gawarwakin Mutum 71 Da ’Yan Bindiga Suka Kashe A Katsina
An binne gawarwakin mutum 71 da ’yan bindiga suka kashe a wasu kauyuka bakwai na Karamar Hukumar Bakori da ke Jihar Katsina.
Kauyukan da lamarin ya shafa sun hada da Jargaba, Gidan Gago, Gidan Alhaji Audu Gari, Gidan Shirai, Gidan Baushe, Unguwar Gogai da Dicika da ke Karamar Hukumar Bakori.
Wadanda lamarin ya rusta da su sun yi artabu da ’yan bindigar yayin da suka fita karbo dabbobinsu da ’yan bindigar suka sace musu.
Mummunan artabun da har yanzu ba a kammala tattara adadin wadanda suka rasu ba, ya auku ne a kauyukan Gidan Gwanki da Gidan Damo da ke Karamar Hukumar Kankara.
Kananan hukumomin biyu dai na fama da hare-haren ’yan bindiga, da satar mutane da shanu da sauran miyagun laifuka.
Guda daga cikin ’yan sa-kan da ya nemi a sakaya sunansa ya ce sun samu nasarar hallaka akalla ’yan bindiga 100, amma ba su da masaniyar guda nawa aka kashe musu.
Wani da ya rasa dan uwansa yayin artabun mai suna Abdullahi ya ce suna cikin alhini.
managarciya