Ina Son Zama Sanata Ne A Sakkwato Ta Gabas Domin Na Bunkasa Yankin----Alhaji Sirajo Sa'idu Mai Fata

Ina Son Zama Sanata Ne A Sakkwato Ta Gabas Domin Na Bunkasa Yankin----Alhaji Sirajo Sa'idu Mai Fata

 

Alhaji  Sirajo Sa'idu Mai Fata 'Yarbulutu wanda an ka fi sani da MD dan Sokoto Mai Allah ya fito neman zama Sanata don ya wakilci yankin Sakkwato ta gabas a majalisar dattijai ta Nijeriya a jam'iyar PDP a zantawarsa da Managarciya ya fadi dalilin da ya sanya yake neman wannan kujera ya ce abin da ya jawo hankalina na fara neman kujerar Sanata a yankin Sakkwato ta gabas, naga manyanmu sun wakilce mu tsawon shekarru ba wani cigaba da suka kawo na azo a gani, sun ce za su baiwa matasa aikin yi da kare lafiyar mutane da ruwan sha da hanyoyin mota a gaskiyar magana ban ga daya da aka yi ba.

MD ya cigaba da cewa  abin bakinciki da yafi tayar min da hankali yanda aka bar matasanmu suka zama cima kwance, ga shi kuma ina da damar da zan nemi wannan kujearar domin na kare su hakan ya sanya na fito don mu samu kwanciyar hankali da zaman lafiya matasan nan sun gani manyan nan alkawalin banza kawai suke yi masu, ba  za mu ci gaba da zama koma baya ba dole ne mu farka. 

"Abu na biyu yakamata wadanda ke ganin sai a gidajensu ake neman kujera su sani Allah ne ke bayarwa, kuma duk abin da suke iya kashewa nima zan yi gwargwadon nawa hali, abin da duk za su yi zan iya yinsa don haka kowa ya zo ya gwada sa'arsa in mun yi zaben fitar da gwani na fadi na yarda, balle bana tsammanin faduwa zabe," a cewar MD mai Allah.
Ya fadi wani abu da ya taba zuciyarsa ya ce "Na kai ziyara a asibitin Sabon birni sai da na yi hawaye majiyantanmu,   maganin da za su sha ya gagare su, ba gado ba katifar da za su kwanta, kan haka na yi alkawalin gyara wannan asibitin a kankanen lokaci na sanya gadaje da katifu."
Ko za ka iya karawa da wanda ke sama? ya ce "gani ya kori ji APC dake saman kujerar nan miye ta yi mana a kasa, kan mage ya waye ina da tabbacin zan ci zabe a yankin Sakkwato ta gabas in Allah ya yarda."
Ko za ka janywa wani a gaba ya ce "Gaskiya yanda na fito neman kujerar nan ba maganar janyewa wane an daina wannan mun fito ne domin bayar da gudumuwa, duk wanda ya sanni kaifi daya nake, ina fatar na gaji mai gidamu, zan samarwa mutanena ruwan sha  da lafiya da wutar lantarki da ilmi matukar muka samu nasara ko da duk abin da na samu zai kare in Allah ya yarda, yankinmu ne mafi koma baya a Sakkwato dole mu fito don bunkasa shi. 
"Ina kira ga matasa su zo su kwaci kansu su dawo daga  zama 'yan amshin shata.
"Magoya baya su taya ni da addu'a wanda baya da rijistar zabe yaje ya yanka katin zabe, kar su yarda dan siyasa ya rude su da kudi, duk dan siyasar da ke rudar mutane da kudi ba masoyinsu  ba ne, in kun bi shi kun saida mashi 'yancinku da kimarku da darajarku ba ka tunanin ya yi maka abu na cigaba, mutuncinmu mu daure mu hade kwadayinmu, mu kwaci 'yancinmu. Allah ya ba mu zaman lafiya da kwanciyar hankali, Kalmomin MD mai Allah.