Kowane Yanki A  Sakkwato Zai Iya Samar Da Gwamna A 2023----- Shugaban PDP

Kowane Yanki A  Sakkwato Zai Iya Samar Da Gwamna A 2023----- Shugaban PDP

 
Shugaban jam'iyar PDP na jihar Sakkwato Alhaji Bello Aliyu Goronyo ya bayyana cewa kowane yanki a Sakkwato za a iya tsayar da ɗan takarar gwamna a 2023 domin kowane yanki ya yi kuma su cancanta suke kula da ita ba yanki ba.
Shugaban a zantawarsa da manema labarai a satin da ya gabata ya ce "A dimukuradiyyance mu a jam'iyyar PDP muna biyayya ne ga kundin tsarin jam'iyya," a cewarsa.
Bello Goronyo ya ce in kana maganar  a jihar Sakkwato "mun damu ne kawai mu samar da shugabbanin da suke da ƙwarewar jagoranci,  kowane yanki a Sakkwato sun yi gwamna ana iya farawa da kowane yanki in ma karɓa-karɓa za a yi, tun da kowa ya yi a matakin farko, a zagaye na biyu ana iya somawa da kowane yanki shi ne daidai, magana ce ta fahimta.
Ya ci gaba da cewa za a dubi waɗanda ke takara ne a ƙwarewarsu da karɓuwarsu ga jama'a da an yi haka za ka ga ba a  samu ba wata matsala ba.
Shugaban ya juya kan sirrin da ya sa suke da haɗin kai a jam'iyarsu ya ce "PDP bayan zamanta tsohuwar jam'iya tafiya ce ta msu akida ba kamar APC da uzuri ya samar da ita ba, ai ka gani an samu mulki amma an kasa yanda za a rike mulkin, mutanen ƙasar nan sun fahimci hakan a bangaren tsaro da yanda tattalin arziki ya taɓarɓare. 
 
"A Sakkwato mun tsare taken jam'iyarmu na cewa shugabanci na mutane ne ba wanda zai ce shi kaɗai ke da jam'iyar PDP hakan ya sanya muke samun cigaba da hadin kai a tafiyarmu, don haka kar ka yi mamakin PDP domin ita ke da ƙwarin guiwa da sinadaran iya tafiyar da mulki, da ikon Allah za ta karɓi mulkin Nijeriya. 
Kira na ga mabiyanmu da mu gaba ɗaya mu ji tsoron Allah, a yi tafiya tare da kowa ba bambanci, kowa ya ba da tasa gudunmuwa ba tare da nuna fifiko ba, tafiyar takowa ce, mu ɗaure da  sauaren shawara da girmama ra'ayin kowa hakan zai sa  haɗin kanmu ya ɗaure har bayan zaben 2023.
 
"Kan cika alƙawullan da muka ɗauka gaba ɗaya, nake da ƙwarin guiwar cewa mutanen jihar Sakkwato za su sake zaɓarmu, don  cigaba da aiyukkan da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya  soma da kuma tsarin mulki da ake da shi a yanzu, don haka mutane su zaɓi PDP a kowane mataki a jiha da kasa. Nan gaba kadan za mu fara karbar masu sauya sheƙa daga wasu jam'iyyu zuwa namu.