WATA UNGUWA, Fita Ta Bakwai

Karɓe icen ta yi daga hannunsa, har ya juya zai tafi ya dawo daga baya ya fuskanci Maheerah cikin kumfar baki ya ce "Ki ji ni da kyau, ni ne dai mahaifinki, damar zaɓa miki miji tana hannuna, don haka na ba ki nan da sati biyu ki yankewa kanki hukunci, in har ba za ki auri Irfan ba to ki samo madadinsa a tarbiyya da nagarta in ba haka ba zan aura miki duk wanda na ga dama." Yana gama faɗa ya fice cike da damuwa da suyar zuciya ya yi waje, sai da ya zo soron gidan ya tuna da ya bar baƙonsa a waje, don haka ya yi ƙoƙarin saita nutsuwarsa tare da ƙarasawa gunsa.

WATA UNGUWA, Fita Ta Bakwai

page 7

 

 

BABI NA BAKWAI

 

Jibgarta yake ba ji ba gani, ko gani ba ya yi sosai tsabar ɓacin ran da yake ciki, zuciyarsa sai zaɓalɓala take. Tuni ya makance da hango duk wani aibu dake tattare da dukkan da yake yi mata, sai buga mata icen yake duk inda ya samu a jikinta.

Umma da ta ga abin bana ƙare ba ne, kuma idan har ta zuba ido komai zai iya faruwa ga tilon 'yarta mace, hakan ya sa ta ƙarfafi zuciyarta tare da shiga ɗakin cikin hanzari tana ƙoƙarin ƙare Maheerah

"Don Allah Malam ka dakata haka, idan rai ya ɓaci bai kamata hankali ya gushe ba, za ka iya raunata ta fa."

Fuskarsa a murtuƙe kamar kunun kanwar da ya yi gardama ya kalli matar tasa a fusace "Ki bari in mata dukkan kawo wuƙa Indo, ta yanda zamu raba raini, kin ga gobe in har na ɗora mata doka ba za ta tsallaka ba." Ya sauke yana huci kamar kumurci.

Icen dake hannunsa umman ta riƙe tana faɗar "Don girman Allah ka yi haƙuri malam.  Idan ka ce za ka daka ta yaran zamani to lallai sai dai ka illata su ka janyo wa kanka abun faɗa."

Karɓe icen ta yi daga hannunsa, har ya juya zai tafi ya dawo daga baya ya fuskanci Maheerah cikin kumfar baki ya ce "Ki ji ni da kyau, ni ne dai mahaifinki, damar zaɓa miki miji tana hannuna, don haka na ba ki nan da sati biyu ki yankewa kanki hukunci, in har ba za ki auri Irfan ba to ki samo madadinsa a tarbiyya da nagarta in ba haka ba zan aura miki duk wanda na ga dama."

Yana gama faɗa ya fice cike da damuwa da suyar zuciya ya yi waje, sai da ya zo soron gidan ya tuna da ya bar baƙonsa a waje, don haka ya yi ƙoƙarin saita nutsuwarsa tare da ƙarasawa gunsa.

Daga cikin gida kuwa malam na fita Umma ta kalli Maheerah da takaici zane a allon fuskarta ta ce "Kin dai ga abin da kika ja wa kanki ko? Ga irinta nan, a karon banza da wofi kin ja wa kanki jibga. Ina faɗa miki tun wuri ki ajiye wannan girman kan ki yi biyayya gare mu ko kya samu tsira a gobe ƙiyama. Kodayake ma ai jiki magayi."

Yunƙurawa ta yi da ƙyar ta tashi, don duk jikinta ya yi tsami faɗar ta ke "Umma ba wai ina bijirewa zancenku ba ne, a cikin zuciyata ne bana son kowa sai Ja'afar a yanda nake ji zan iya shan guba idan na rasa shi." Umma ta kama haɓa tana tafa hannaye tare da faɗar

"La'ilaha illallahu! Har abun naki ya kai da mummunan ƙuduri haka Mahee? Lallai kin yi nisa ba kya jin kira, Allah ya shirye ki."

Da gama faɗa ta juya zuwa ɗakinta tana mamakin wannan al'amari na Mahee, ko dai yaron nan asiri ya mata ne? To wannan abin in dai ba asiri da sharrin jinnu a ciki. Wai yau da su ne Maheerah take musayar yawu a kan namiji? Ba ta yi tsammanin haka daga gare ta ba.

Bayan kamar mintuna arba'in Maheerah na kwance tana jinyar jikinta da ya mata nauyi, ji take kamar wasu gaɓoɓin jikin nata sun karye. Ta tsunduma kogin tunanin abin sonta ko me Baba ya masa? Mummunan faɗuwar gaba ce ta ziyarce ta, hankalinta ya kasa kwanciya. Saurin bugun zuciyarta ne ya ƙaru, ta rasa abin da ya kamata ta yi. Can wani ɓangare na zuciyarta ya shawarce ta da ta kira shi, domin ta ji a ranta cewa tabbas ba lafiya, shirun ya yi yawa.

Hannu ta miƙa ta janyo wayarta da ke nesa da ita kaɗan, ta hau dubawa. Kamar dai yanda ta yi tsammani bai kira ba, bai turo saƙo ba.

Jikinta ne ya yi sanyi laƙwas kamar wacce aka zarewa lakka ta ɗaga wayar tare da kiransa, sai da ta kira sau biyar bai ɗaga ba.

Hankalinta ya kai ƙololuwar tashi, domin tun da take da Ja'afar bai taɓa ƙin daga wayarta ba sai yau, babu shakka ko ba a faɗa mata ba tasan fushi ya yi don kuwa idan har ka ga Goɗiya da sirdi to tabbas wani ta kayar.

Tana nan cikin tashin hankali da tunanin mafita sai ga saƙonsa ya shigo wayar.

Da sauri ta shiga ciki ta fara karantawa kamar haka

    "Ke malama! kada ki takura mun a daidai lokacin da nake tsakiyar shauƙin soyayya da Sahibata. Tun da har Abbanki ya kore ni shi ke nan, na yi masa alƙawarin ba zai kuma gani na ba a gidansa in dai ni ɗan halal ne."

Nan da nan alamomin tashin hankali suka bayyana a taswirar fuskarta bayan da ta gama karanta saƙonsa, duk da cewa a lokacin sanyi ne sai da ta ji wani gumi-gumi ya fara tsattsafowa a duk wata kafar gashin jikinta.

Cikin rawar hannu ta fara rubuta masa martani, da rubutunta wanda karantawa ɗaya za ka masa kasan ba ƙwararre ba ne ya rubuta. Ga abin da take cewa

   "Don girman Allah Ja'afar kada ka azabtar da zuciyata da rashin ganinka ko jin muryarka ba zan jura ba. Yanzu dai ka faɗa mun ya kake so a yi, ina son ganinka."

Ba tare da ta tsaya sake bibiya ba ta tura da rawar jiki tare da komawa ta lafe luf kan katifarta cikin tsananin damuwa. Abin ya haɗe mata biyu ga zafin ciwon jiki ga na zuciya.

A can ɓangaren Ja'afar yana ganin saƙon martanin da ta mayar masa ya bushe da dariya tare da kallon abokinsa Hanif ya ce

 "Ka gani ba mutumina, dama na faɗa maka ni ba kanwar lasa ba ne, Kum ni nasan irin bishiyar ƙaunar dana dasa a zuciyar yarinyar nan, ina sane kuma na mata dashe mai ƙwari da zai yi wuyar tumɓukewa."

Hanif ya yı yar dariya irin tasu ta tsagerun matasa tare da buga kafaɗar Abokin nasa ya ce "Gaskiya Abokina ba ka da dama, kasan kan tsiya, yanzu dama duk wannan abin ba tsakani da Allah kake son Mahee ba?"

Dariya Ja'afar ya bushe da ita sai da ya yi mai isarsa, sannan ya zuƙi sigarin dake hannunsa ya fesar da hayaƙin ta salansar hancinsa  kafin ya ce "Ina sane na tsara duk wannan, dama duk wannan shirin na yi ne saboda zuwan irin wannan ranar, ba ita yar malamai ba? Yanzu za ka ga me zai faru don dole ta kawo mun kanta har nan, daga nan ne wasan zai soma." Ya sake zuƙar sigarin a karo na biyu.

"Ka bi a hankali dai, Allah sarki Mahee, wallahi tausayi take ba ni, baiwar Allah duk ta ɗauki son duniya ta ɗaura a kanka, ashe kai shirin yaudararta kake." Hanif ya faɗa cikin tausayawa.

Shi kuwa Ja'afar ban da dariya ba abin da yake, sai can kamar bayan mintuna talatin ya tura mata amsar saƙonta, a lokacin ne kuma suka yi sallama da Hanif ya wuce unguwarsu.

Har zuwa wannan lokacin ba ta yi bacci ba tana ta jiran amsarsa, taya ma za ta iya kwanciya a cikin wannan yanayin? Fita ta yi waje ta yo arwala ta zo ta tada sallar isha.

Tana idarwa ne kuma ta jiyo ƙarar shigowar saƙo a wayar don haka ba ta ko bi takan addu'a ba, ta ɗauko wayar tana karanta saƙon a fili da ragaggen sauti.

'Tabbas ba za ki ƙara ganina ba Mahee, in har kina son ki ganni sai dai ki zo da kanki har inda nake, in ba haka ba kuma ki ƙaddara a ranki ruhinmu sun yi bankwana da juna, idanuwanmu sun ƙauracewa ganin juna. Address DAGARMA gida mai lamba 60.'

   "Innalillahi wa innailaihir raji'un!" Ta furta a hankali muryarta na rawa. Lokaci ɗaya kuma hawaye suka fara tsere a tudun Kumatunta. Ta maimaita karanta saƙon ya kai sau uku kafin kowanne ɗaya daga cikin kalmomin dake rubuce a saƙon ya zauna a kwanyarta daram.

Tashi tsaye ta yi ta shiga zirga-zirga a tsakiyar ɗakin nata ita kaɗai "Tabbas Babana ya ɓallo mun ruwan da ba zan iya tarbe su ba." Ta furta a hankali.

Sai kai-komo take yi a tsakar ɗakin tana surutui ita kaɗai kamar zararriya.

   "Ba zan iya aikata wannan aikin ba Jafsee, sai dai ka yi haƙuri. Ni ce wai zan bar gidanmu ba da sanin mahaifana ba har na je ga saurayi? Abin da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa."

Numfashi ta ja ta sauke kafin ta ce "Tabbas ina sonka yanda ba zan iya misaltawa ba, zan iya komai a kanka amma wannan kuma ina fargabar aikatawa."

Can dai ta ji ƙafafunta sun kasa jure azabar zirga-zirga da take yi da su, ga shi dama duk Baba ya doddoke mata su.

Haka ta nufi shimfiɗarta jiki a saluɓe ko karkaɗe shimfiɗar ba ta yi ba ta kwanta, tana saƙa da warwarar abubuwa a zuciyarta.

Washegari Maheerah ta kasa tashi saboda nauyin da take jin jikinta ya yi mata kamar dutse, har wajajen tara da rabi tana nan kwance jikinta ya yi tsami sosai, wasu sassan jikinta ma duk sun kumbura da alama ta ji ciwo a gun.

Umma ce ta leƙo ɗakin tana faɗar "A'ah! Mahee yau kin yi nauyin bacci ne? Na zata ma tuni kin wuce makaranta da kika leƙa kika ga ina bacci."

Sai a lokacin ta buɗe idonta da suka fara kumbura ta zubawa umma su. Da ƙyar kamar mai ciwon baki ta buɗi baki ta ce "Umma na kasa tashi yau, jikina duk ya yi tsami, har yanzu bacci ne a idona."

Cikin tausayawa irin ta uwa ga yarta umman ta ƙarasa wurin shimfiɗar tana ƙoƙarin kamata don ta tashi, ta ce "Ayyah! Sannu ai dole ki kasa tashi irin wannan dukan da kika sha, don ma Allah ya taƙaita. Barin ɗebo ruwan zafi na gargasa miki jikin ko za ki ji daɗi."

Ba ta ce komai ba ta lumsashe kumburarrun idanunta.

Can bayan wasu mintuna umma ta shigo da 'yar roba da ruwan zafi a ciki hannunta riƙe da ƙaramin ƙyalle. Nan ta shiga aikin gasawa Mahee jikin.

Bayan ta gama ta kawo mata abincin kari har ɗakin ta ci.

Ai kuwa Mahee ta ji daɗin gashin ba kaɗan ba. Domin jikinta ya rage tsamin da yake bayan wani ɗan lokaci kuma ta lura da sacewar wasu wuraren da suka kumbura a jikin nata.

Can zuwa yamma abin duniya ya taru ya yi wa Maheerah yawa, ta kasa jure rashin Ja'afar a kusa da ita wannan dalilin ya sa ta ɗauki huɗubar da sheɗan ke yi mata ta zuwa gidansu Ja'afar ɗin kamar yadda ya buƙata.

Saboda haka ta faɗawa ummanta cewa za ta je duba jikin ƙawarta Zainab a unguwar Bashal. Umman ta yi yunƙurin dakatar da ita ta hanyar tuna mata yanayin da take ciki. Amma sai ta ce ba komai ai ta samu sauƙi za ta iya.

Da wannan ta samu ciyo kan ummar har ta amince mata. Don haka a gaggauce ta yi shirinta cikin atamfa doguwar riga da ɗankwali ta zura Hijab dogo wanda ya sauka har duga-duganta, da sauri ta fice daga gidan gudun Abbanta ya riske ta.

A ƙofar gidan ta ja ta yi turus saboda ganin mayenta da ta yi a tsaye, da alama ya jima tsaye a gun yana jiran ɗan aike.

Nan take yanayin fuskarta ya canza daga na damuwa zuwa na tsananin fushi. Ta ƙara tantame fuska sosai kamar wacce ba ta san an halicci wata aba mai suna dariya ba.

Yi ta yi kamar ba ta gan shi ba, ta raɓa za ta wuce kenan ya tare gabanta

 "Habah! Mahee ban cancanci irin wannan wulaƙanci daga gare ki ba, meye aibuna don na so ki?"

"Malam ka matsa mun daga hanya ina da wurin zuwa, in kai ba ka da abin yi." Ta faɗa tana jan kakkauran tsaki.

  "Ina cikin damuwa Mahee please ki taimaki wannan rayuwar da ta mace a kanki." Ya faɗa a marairaice kamar zai yi kuka.

Wani tsakin ta kuma ja tare da matsawa daga gefe tana yunƙurin wucewa ta ce "A halin yanzu damuwar da nake ciki ta ninninka wacce kai kake ciki, kuma silar wannan damuwar tawa kai ne, don haka ni zan tafi daidaita nawa al'amarin. In ka so ka kwana a nan."

Daga haka ta wuce abin ta, tana fita titi ta tari Napep sai unguwar Dagarma.