An shiga barazanar yunwa saboda hare-haren 'yan bindiga a Zamfara
Al'ummar garin Kairu da sauran wasu garuruwa fiye da goma na yankin ƙaramar hukumar Bukkyum a jihar Zamfara na can cikin ƙaƙa-nika-yi sakamakon hare-haren 'yan bindiga da suka addabe su.
Al'amarin da ya hana manoma girbe kayan amfanin gona, bayan sace mutum fiye da hamsin don neman kuɗin fansa daga garuruwan, kuma ala tilas mafi yawan jama'ar yankin sun yi gudun hijira zuwa wasu wurare.
Wannan na aukuwa ne duk da alƙawarin da gwamnatin jihar ta Zamfara ta yi na samar da matakan tsaro a yankin.
An kwashe kimanin shekara goma ana fama da wannan matsala.
Wani mutumin yankin, da ba ya so a faɗi sunansa, ya bayyanawa BBC ce akwai garuruwa kamar 10 da har yanzu ba su isa su je gona ba.
Ya shaida cewa ko a ranar Asabar sai da aka kwashe mutane kuma an hana su zuwa gonaki kwata-kwata.
"Ba mu da halin zuwa gona ko girbe amfanin gonarmu, kullum hari suke kawo wa ko a jiya sai da suka kwashe mutane da neman kudin fansa."
"An kwashe mana yara kusan mutum 36 mun kai kudi sun ce sai an kawo Honda an kai musu sunce sai an kawo na Oga."
Manomin ya ce wannan yanayi na sanya su asarar milyoyin kuɗaɗe saboda rashin iya zuwa girbi, ga kuma barazanat fadawa cikin yunwa.
Ya roƙi jami'an tsaro su taimake su saboda mutanensu sun warwatse, saukin da ake ganin kamar za a samu har yanzu ya gaggara, a cewarsa.
"Ko kwanaki sai da aka kashe mutum 10, sannan duk bayanan gwamnati na samun sauki har yanzu ya gaggara".
Wannan lamarin dai ya haddasa wa jama'ar garuruwan asara mai dimbin yawa da tilasta wa mutanen garuruwan da abin ya shafa tserewa zuwa wasu garuruwa.
Wannan yanayi da ake ciki a Zamfara na cigaba da zamewa manoma wani karfen kafa.
Sai dai Mustafa Jafaru Ƙaura, babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar ta Zamfara kan harkokin watsa labarai, ya ce gwamnatin jihar na sane da wannan matsalar kuma tana iya kokarinta wajen shawo kanta.
Ya ce an tada tawaga mai karfi zuwa garin Kairu da sauran sassa domin jadadda mu su cewa ba wai an manta da su ba ne.
Ya ce ba wai kawai a karamar hukumar Bukkuyum ba, duk inda ake fama da wannan matsala suna kokarin ganin yadda za a kawo karshenta.
Ko a makonni biyu da suka gabata sai dai aka samu rahotanni da ke cewa wasu da ake zargin ƴanbindiga ne sun cinna wa gonakin manoma da dama wuta tare da yin garkuwa da mutane da dama a wasu ƙauyukan na jihar Zamfara.
Mazauna yankunan da ke iyaka da jihar Kebbi, sun ce ƴanbindigar sun sa sun tafka gagarumar hasarar amfanin gonar da suka noma da ya hada da masara da auduga, da wake da sauran su.
Ko a kwanan nan wasu mahara masu dauke da muggan makamai sun yi irin haka a Birnin Gwarin jihar Kaduna, inda suka kona amfanin gonar da ba a kai ga girbewa ba, da aka ƙiyasta cewa kudinsa ya kai na miliyoyin naira.
Duk da dai ikirarin hukumomi na yaƙar ƴanbindiga a yankin arewa maso yammaci, kusan a kullum sai an kai hari musamman a jihohin Zamfara da Katsina da Sokoto da Kaduna.
Jihar Zamfara na ɗaya daga cikin johohin da matsalar tsaro ta fi kamari a faɗin Najeriya, inda barayin daji ke afkawa garuruwa da kauyuka da kashe mutane da satar wasu domin neman kuɗin fansa, ga kuma sacewa ko kwace amfanin gonar da manoma suka shuka.
managarciya