@Ramadan:Gwamnatin Sakkwato Za Ta Kashe Miliyan 396 Ga Mabukata 17000

@Ramadan:Gwamnatin Sakkwato Za Ta Kashe Miliyan 396 Ga Mabukata 17000

 

Daga Mukhtar Haliru Tambuwal Sokoto. 

Gwamnan jihar Sakkwato wanda mataimakinsa Honarabul  Manir Dan'iya, ya wakilta a wurin kaddamar da rabon kayan Azumi da sallah ga mabukata da marayu  ya ce gwamnati ta baiwa hukumar zakka tallafi  mai yawa domin ta samu damar gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.

 Munir  Dan’iya ya bayyana cewa gwamnatinsu tare da hadin gwiwar kungiyoyi na gida da waje kamar Qatar Charity, Indonesia, Malaysia  da kuma Dangote sun hada hannu wajen samar da kayan masarufi a bangarori daban-daban na rayuwar dan adam. 
 Ya kara da cewa an sanya sama da naira miliyan dari uku da casa'in da shida domin taimakawa a cikin watan Ramadan ta hannun hukumar zakka ta jiha.
 Kowace gunduma a fadin jiha  za'a kai kayan Suturar Sallah guda 100 ga marayu 100i da kudin dinki Naira dubu 100, tare da buhunan  shinkafa guda 100 da kudi Rabin miliyan ga mabukata a daukacin gundumomin 87 da ke a fadin jihar cikin kananan hukumomi 23. 
A nasa jawabin mai alfarma sarkin musulmi Alhaji  Muhammad Sa'ad Abubakar, ya yabawa kokarin gwamnati mai ci a jihar a Kan shirye shiryen ta ciki har da shirin ciyarwa a watan Ramadan da sauran abubuwan jindadin rayuwa.
Sarkin musulmi ya bukaci masu ruwa da Tsaki da su kara kaimi ga kokarin gwamnatin jihar akan hakan. 
Ya kuma ba da tabbacin majalisar Sarkin Musulmi a shirye take ta tallafa wa ayyukan hukumar domin gudanar da aikinta yadda ya kamata. 
Yayi kira ga masu hali da 'yan kasuwa da su rage  farashin kaya dan tausayawa talakka, kana yayi kira ga mahukunta da a kara  kaimi domin shawo matsalar da ake ciki. 
Ya shawarci al'ummar musulmi  da a dukufa da addu'a cikin wannan watan don a samu saukin halin da ake ciki. Kwamishinan ma'aikatar lamurran addini ta jiha  
Honarabul  Abdullahi Maigwandu,  yayi kira ga masu hali da su rage farashin abinci albarkacin wannan watan. 
 
Shugaban Hukumar Malam Muhammad Lawal Maidoki Sadaukin Sakkwato, ya bayyana cewa za su yi   rabon zakka da tallafin Gwamnatin Jiha ga marayu da mabukata a fadin gundumomi 87 a kananan hukumomi 23 na jihar nan wannan shekarar.
Malam Muhammad Lawal Maidoki ya cigaba da cewa tun a shekarar 2014 hukumarsa take karbar zakka da wakafi tana raba wa wadanda suka cancanta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada wanda hakan ke tasiri ga rayuwar wadanda suka amfana da iyalansu.
A cewarsa a shekarar 2021 sama da biliyan biyu da dari tara da tara da shida (2,996.286) ne aka fitar a matsayin zakka kuma za a raba tare da tallafin na watan Ramadan da gwamnatin jiha ke bayarwa.
Malam Muhammad Lawal Maidoki ya tabbatar da goyon bayan da hukumarsa ke samu daga kananan hukumomin jiha da majalisar dokokin jiha da ma’aikatu da  masarautar Sarkin Musulmi da uwayen kasa.
Ya ce, Hukumar Zakka ta fitar da wani tsari na tsawon shekaru goma domin dakile matsalar talauci a jihar nan da zuwa shekarar 2030. 
Hukumar tare da hadin gwiwar Asusun Qatar Charity da sauran masu hadin gwiwa na waje za su taimaka wa mabukata sama da dubu ga  nau’o’in tallafi daban-daban a  bayan Ramadan. 
Shugaban ya bayyana ce Hukumar ta karbi kayan Tallafin  abinci daga Kamfanin  KK Rice da Alhaji Murtala Abdulkadir Dan’iya domin rabawa mabukata.