za mu kai karshen matsalar tsaro a wata shekara---Gwamnatin Tarayya

za mu kai karshen matsalar tsaro a wata shekara---Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin tarayya ta ce ta fahimci yanda matsalar tsaro ke addabar Nijeriya don haka ta yi alkawalin Kawo karshensa kafin karshen shekarar 2024.
Karamin ministan tsaro Dakta Bello Matawalle ya fadi haka a hirarsa da BBC Hausa.
Matawalle ya ce gwamnati za ta kawar da 'yan bindiga gaba daya musamman a Arewa da suke addabar mutane.
"Da yardar Allah daga yanzu zuwa watan Nuwamban 2024 za a yi maganin matsalar tsaro" a cewarsa.
Ya ce matakin da aka dauka zai kawo karshen lamarin don shirin da aka yi za a rika Kai hari a maboyar 'yan bindigar ba tare da jiran sai sun Kawo farmaki ga mutane na.