Kasafin kudin jihar Zamfara na Naira Biliyan 545 ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya

Kasafin kudin jihar Zamfara na Naira Biliyan 545 ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya

Kasafin kudin jihar Zamfara na Naira Biliyan 545 ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya

Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara ta soki kasafin kudin shekarar 2025 da Gwamna Dauda Lawal ya gabatar inda ta ce ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar nan.

A wata sanarwa da aka rabawa Arewa PUNCH, kakakin jam’iyyar, Yusuf Idris, ya ce gabatar da kasafin kudin da Lawal ya yi ya sabawa duk wani tanadin tsarin mulki.

A cewar Idris, taron gabatar da kasafin kudi a kowace jiha ya kasance wani buda-baki ne ga duniya baki daya, sai dai ya koka da cewa, gwamnan ya hana jama’a da ma ‘yan jarida damar shaida bikin.

Idris ya ce, “A yayin da suke shirin kashe sama da Naira biliyan 545 a kasafin kudi na shekarar 2025, Gwamna Dauda Lawal da jama’arsa sun boye a zauren majalisar dokokin jihar domin yin girki a asirce yadda suka yi niyyar aiwatar da boyayyen manufarsu.

Don haka Idris ya yi kira ga gwamna da majalisar dokokin jihar da su sauya kasafin kudin tare da bin tsarin da ya dace.

Ya ce, “Don haka jam’iyyar APC a Zamfara tana kira ga gwamnan da ya gaggauta sauya kasafin kudin tare da neman gafarar jama’a domin amfanin kansu.

Jam'iyyar adawa ta yi barazanar daukar matakin shari'a idan har ba a sauya batun gabatar da kasafin kudin ba.

Abbakar Aleeyu Anache