Za mu kawar da ƙungiyar Lukarawa – Shugaban Yaki da ta’addanci na Najeriya
Cibiyar Yaki da Ta'addanci ta kasa a ranar Alhamis ta bayyana sabuwar kungiyar ta'addancin, Lukarawa, a matsayin maras kima, wanda kiyasin 'yan kungiyar ya ce mayakan sun gaza 150.
Cibiyar ta danganta yunkurin daukar ma'aikata na kungiyar a halin yanzu da kokarin da ake na kara yawan su.
Hedkwatar tsaro a kwanan baya ta tabbatar da bullar Lukarawa da ke aiki a yankin arewacin Najeriya, musamman a jihohin Sokoto da Kebbi.
A cewar daraktan ayyukan yada labarai, Manjo Janar Edward Buba, ‘yan ta’addan sun fara kutsawa yankunan arewacin Sokoto da Kebbi daga jamhuriyar Nijar da Mali, musamman bayan juyin mulkin da aka yi a Nijar.
Da yake zantawa da manema labarai a Abuja, kodinetan cibiyar na kasa, Manjo Janar Adamu Laka, ya yi watsi da fargabar da ke tattare da kasancewar kungiyar, yana mai bayyana cewa barazanar ba ta kai yadda ake tunani ba.
Ya kuma tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa, a ci gaba da kokarin yaki da ta’addanci, nan ba da jimawa ba za a kawar da kungiyar Lukarawa a matsayin matsalar tsaro.
Ya kuma gargadi ‘yan Najeriya da su guji yada fargaba a zukatan jama’a game da kungiyar.
managarciya