Shirin Zanga Zangar 1 ga Oktoba Ta Kankama, An Aika Sako ga 'Yan Sanda 

Shirin Zanga Zangar 1 ga Oktoba Ta Kankama, An Aika Sako ga 'Yan Sanda 

 

Wadanda suka shirya zanga-zangar #FearlessOctober1 sun bayyana cewa 'yan sanda, DSS da sojoji ba za su hana su gudanar da zanga-zangar ba kamar yadda suka tsara. 

Masu shirya gangamin sun kuma rubutawa Sufeto Janar na ‘yan sanda Kayode Egbetokun takardar neman tsaro a lokacin zanga-zangar da za su fara 1 ga watan Oktobar 2024. 
Wadanda suka shirya zanga-zangar sun lura cewa zanga-zangar wani hakki ne na 'yan kasa kuma ba za su mika wuya ga barazanar kowa ba, inji rahoton The Punch. 
A ranar Talata 1 ga Oktoba ne Najeriya za ta yi bikin cika shekaru 64 da samun 'yancin kai, ranar da wasu matasa suka shirya gudanar da zanga-zangar nuna adawa da tsadar rayuwa. Kodinetan zanga zangar 'Take It Back' na kasa, Juwon Sanyaolu, da daraktan hado kan jama'a na kungiyar, Damilare Adenola, sun ce tuni aka kammala shiryawa wannan gangamin. 
Sun kara da cewa ‘yan Najeriya za su fito kwansu da kwarkwatarsu daga sassa daban-daban na kasar domin gudanar da zanga-zangar. 
“Mun aikawa Sufeto Janar na ‘yan sanda takarda, mun sanar da shi wuraren da za mu gudanar da zanga-zangar tare da tunatar da shi hakkin masu zanga zangar na samun tsaro." 
Kungiyar ta bayyana cewa za a gudanar da zanga-zangar a dandalin Eagle Square da ke Abuja, inda aka gudanar da faretin ranar samun ‘yancin kai. 
A jihar Legas kuwa, masu shiryawar sun ce za a yi zanga-zangar a babbar gadar Ikeja suna masu cewa dawo da tallafin mai, kudin lantarki ne kawai zai dakatar da su.