Ministan tsaro ya ba da umarni ga sojoji a binciko makasan Sarkin Gobir

Ministan tsaro ya ba da umarni ga sojoji a binciko makasan Sarkin Gobir
 
Ministan tsaron Nijeriya Bello Matawalle ya bayarda umarni ga shugaban sojojin Nijeriya Janaral Christopher Musa a matsa kaimi a kamo wadan da suka kashe Sarkin Gobir Muhammad Isah Bawa a jihar Sakkwato.
Sarkin Gobir ya samu tausaya wa a dukkan fadin Najeriya ganin yadda aka zalunce shi aka kashe shi ba da hakki ba.
A bayanin da jaridar Sahara Reporters ta rahoto ya bayyana wannan umarnin ne ga ƙaramin ministan ya bayar abu ne da ke cike da yar tambaya domin shima dai akwai zargi kansa.
Mutanen Arewa dai na fatar samun nasarar tonon asiran makasan sarki a duk in da suke.