Kungiyar ta'addancin Lakurawa na amfani da jirage marasa matuka wajen bin diddigin sojoji da fararen hula
Daga Abbakar Aleeyu Anache.
Bulama Bukarti, ya bayyana cewa, kungiyar ta’addanci ta Lakurawa tana sa ido kan al’ummomi da sansanonin sojoji a yankin Arewa maso Yamma.
Bukarti, lauya mai kare hakkin dan Adam ne ya bayyana hakan a lokacin da ya bayyana a gidan talabijin na Channels Television’s Politics Today.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne daraktan yada labarai na hedikwatar tsaro Manjo Janar Edward Buba ya bayyana ‘yan ta’addan a matsayin wata kungiya da ta fito daga jamhuriyar Nijar, bayan wani juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar.
Jaridar PUNCH Online ta ruwaito cewa sa’o’i 48 bayan sanarwar da sojoji suka bayar, ‘yan ta’addan sun kai hari garin Mera da ke karamar hukumar Augie a jihar Kebbi, inda suka kashe akalla mutane 15.
managarciya