Allah Gwani: Yin Sallah Na Rage Ciwon Baya — Bincike

Allah Gwani: Yin Sallah Na Rage Ciwon Baya — Bincike

Wani bincike da masana suka gudanar a Jami'ar Binghamton da ke New York na Amurka, ya yi nuni da cewa ayyukan da musulmi ke yi a cikin sallah ba iya ruhinsu zai amfana kaɗai ba, harda ma gangan jikinsu. Binciken ya tabbatar da cewa matuƙar musulmi suka yi sallah yadda aka ayyanata a aikace, hakan zai taimaka wajen rage ciwon baya.

Farfesa Muhammad Khasawneh, shi ne wanda ya jagoranci binciken, ya ce muddun masallata suka bi ayyukan da aka zayyana a sallah, kuma aka cika ƙa'idodinta, za ta iya rage matsalar ciwon baya.

Ya kuma ƙara da cewa, daga cikin ayyukan sallah, sujjada na ƙara ingancin ayyukan gaɓɓai, baya ga taimakawa wajen magance riƙewar gaɓoɓin jiki.

Haka nan, ƙari kan dalilin wannan bincike shi ne, yadda ayyukan da ke cikin sallah ke yin kamanceceniya da irin atisayen da likitocin fisiyo ke bayarwa ga masu ciwon baya da sauran masu fama da matsalolin gaɓoɓi da ke shafar ƙashi, jijiya da tsoka.

Bugu da ƙari, an lura cewa maimaituwar sujjada na daidaita da kuma haɓaka ayyukan sassan numfashi, zuciya, hanyoyin jini, da ƙwaƙwalwa ta hanyar ƙaruwar zagayawar jini da iskar oksijin a jiki.

An wallafa sakamakon wannan bincike ne a mujallar International Journal of Industrial and Systems Engineering.