'Yan bindiga sun kai hari fadar Sarkin Minna tare da harbin masu gadi da kuma sace kuɗaɗe

'Yan bindiga sun kai hari fadar Sarkin Minna tare da harbin masu gadi da kuma sace kuɗaɗe

 

Wasu da ake zargin ƴann fashi da makami ne a jiya Talata sun kai hari fadar Sarkin Minna, Umar Faruk Bahago, inda su ka yi awon gaba da wasu kudade da ba a tantance adadinsu ba.

DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa yan fas sun bi biyo wani jami’in fadar, wanda ke dawowa daga banki bayan ya ciro kudi.

Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, sakataren masarautar ta Minna, Garba Musa, ya ce jami’an tsaron fadar biyu da suka samu raunukan harbin bindiga a yanzu haka suna karbar kulawa a babban asibitin garin Minna.

“Muna cikin gida tare da Mai Martaba Sarki, sai muka fara jin kara mai nauyi. Da farko, muna tsammanin yara ne kawai suke wasa. Amma nan take muka ji mutane suna kururuwa ‘barayi ne; barayi ne’. Don haka na yi gaggawar fitowa na tarar a zahiri harin fashi da makami ne,” in ji Mista Musa.

“Sun harbi biyu daga cikin masu gadin fadar da ke kokarin dakile harin. Sai dai kash an harbi daya a cinyarsa yayin da daya kuma aka harbe shi a kirji. Nan take aka garzaya da su babban asibiti.”

Ya ce ‘yan bindigar sun bi ta kofar gida ta biyu inda suka samu shiga inda sarkin yake zaune.

Musa ya kuma tabbatar da cewa kudaden da aka sace na masarautar ne.

Ya kara da cewa an sanar da ‘yan sanda lamarin kuma sun yi alkawarin za su dauki matakin kamo masu laifin.