Dokar haraji: Gwamnonin Arewa ba adawa su ke da Tinubu ba, in ji Gwamna Zulum

Dokar haraji: Gwamnonin Arewa ba adawa su ke da Tinubu ba, in ji Gwamna Zulum

Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya musanta rade-radin cewa gwamnonin Arewa suna adawa da Shugaba Bola Tinubu saboda manufofin sauya tsarin haraji da ya gabatar gaban Majalisar Dokoki ta Ƙasa.

Yayin wata hira da aka yi da shi a tashar Channels TV a ranar Lahadi, gwamnan ya tunatar da cewa kafin zaɓen 2023, shi ne ɗaya daga cikin  gwamnonin da suka dage cewa dole ne mulki ya koma Kudu.

Gwamnan ya bayyana cewa, a matsayinsa na mamba a jam’iyyar All APC, ya mara wa burin takarar Tinubu.

A cewarsa, Arewa ba za ta iya zama masu adawa da Tinubu ba bayan ya samu sama da kashi 60 na ƙuri’unsa daga yankin.

Ya nuna damuwarsa kan yadda wasu ke yaɗa labaran ƙarya cewa Arewa na adawa da gwamnatin Tinubu.

“Ni mamba ne mai ƙarfi a jam’iyyar APC. Idan za a lissafa gwamnonin da suka goyi bayan Tinubu kafin 2019 da 2023, za ka iya ambaton Gwamna Zulum. Ni ne gwamna na farko da ya fito fili ya ce dole ne mulki ya koma Kudu.

“Abin takaici, Shugaban Ƙasa ya samu labari daga da dama cewa Arewa na adawa da shi. Kashi 60.2 na ƙuri’unsa sun fito daga Arewa,” in ji shi.

Zulum ya bayyana cewa abinda gwamnonin suke buƙata shi ne a samu ƙarin tattaunawa kafin a amince da ƙudirin.