Gwamnatin Taliban ta hana mata yin sana'ar gyaran gashi a Afghanistan

Gwamnatin Taliban ta hana mata yin sana'ar gyaran gashi a Afghanistan

Gwamnatin Taliban ta Afganistan ta ba da umarnin rufe duk wasu shagunan gyaran gashi na mata, kamar yadda kafafen yada labarai na cikin gida suka ruwaito a yau Talata.

“Ba a bayar da hujjar yanke hukuncin ba. Lasisin da kayan kwalliyar ke buƙatar aiki za su ƙare a wata mai zuwa, '' a cewar sanarwar da kafofin watsa labarai na Afghanistan su ka wallafa.

Sana'ar gyaran gashi na ɗaya daga cikin 'yan tsirarun hanyoyin samun kuɗin shiga ga matan Afganistan, waɗanda da yawansu ne ke ciyar da iyalansu.

Da karbar mulki a watan Agustan 2021, Taliban ta yi alkawarin mutunta ƴancin mata.

Tun daga sannan ake ta hana mata yin wasu sana'o'i Na ƙwararru.

Haka zalika Taliban sun hana mata zuwa makarantun jami'o'i da na sakandare a Afghanistan.