Gwamnan Zamfara Ya Baiwa Iyalan 'Yan Sandan Da 'Yan Bindiga Suka Kashe Tallafin Miliyan 7

Gwamnan Zamfara Ya Baiwa Iyalan 'Yan Sandan Da 'Yan Bindiga Suka Kashe Tallafin Miliyan 7
Daga Hussaini Ibrahim, Gusau.
 
A kokarin da gwamna Bello Mohammed Matawale ke yi na ganin ya karawa jami'an tsaro kwarin gyuiwa wajan yaki da 'yan bindaga, yanzu haka ya ba iyalan 'yan sanda da 'yan bindaga suka kashe naira Miliyan bakwai kowa Miliyan daya domin su bakwai ne.
 
Kwamishinan 'yan Sanda na Jihar Zamfara, Ayuba Elkana ne ya bayyana haka alokacin da ya ke ba da tallafin kudin da iyalan 'yan Sanda a Hedikwatar 'Yan Sanda da ke Gusau.
 
CP , Elkana ya bayyana cewa, 'yan Sandan sun rasa ransu ne awajan fafatawa da 'yan bindiga  .wadanda suka hada da manyan Ofisoshin kamar haka,Donal Marcus, Salomon Apere, Steven Higher Nura Ibrahim.sai Kuma masu mukamin sajant da suka hada da Abdu Garba,Zubairu Saidu,da Musa Lawal.inji CP Elkana.
 
 Ya kuma kara da cewa, wannan Tallafin zai karawa Jami'an 'yan sanda kwarin gyuiwa wajan jajircewa a yaki da 'yan bindaga da miyagu masu manyan laifuka da ke cikin Jihar.
 
Kuma yanzu haka hukumar 'yan sandan Karkashin Jagorancin Sufeto Janar Alkali tana  kokarinta na ganin hakkokin su ya fito dan baiwa iyalan.