Kungiyar Malaman Jami'o'i, ASUU ta tsunduma yajin aiki 

Kungiyar Malaman Jami'o'i, ASUU ta tsunduma yajin aiki 

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Neja Delta (NDU), mallakin gwamnatin Jihar Bayelsa ta tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani, sakamakon rashin cika yarjejeniyoyin da aka cimma da kungiyar a baya.

ASUU ta sanar da matakin ne a yau Talata bayan wani taro da ta gudanar a sakatariyar ta da ke Amassoma. 

Sai dai kuma ana sa ran yajin aikin zai kawo cikas ga harkokin ilimi a jami'ar, lamarin da ya jefa dalibai da masu ruwa da tsaki cikin rashin tabbas.